MATAR UBA 28

“A’a gami a bakin gate,Kuma Kamar a kulle”
“Okay Ina zuwa”
Yana fito wa ya Bud’e musu gate din inda aka tanadar don ajiye motoci yayi ya yi parking, Faisal ne ya fara fita.
Rungumar juna sukayi farees yace “Am sorry dake kasan sabon gidane ban samu mai gadi ba tukunna”
“Kai dama Banda gulma meyasa zaka sauka anan bayan ga gida,Kai bada Mata ba”
” Kai Dan Allah bar maganar matan Nan”
“Ai wallahi baka Isa ba,Ni ba karamin dad’i naji ba da ka rabu da arniyar Nan jennet ba”
Tab’e Baki yayi “Kai dai ka sani,Kai da wane……”
Bai karasa maganar da yake ba ya hango Hashim ya fito daga cikin motar.
‘dan kauda Kai yayi Hashim Murmushi yayi a zuciyar sa yace “har yanzu Yana fushi Dani Kenan? matsalar gajeren mutum Kenan fad’in Rai” Mika Masa hannu yayi kallon hannun sa ya tsaya yayi gyaran murya Hashim yayi “Assalamualaikum”
Mika Masa yayi shim murya chan ciki yace “Wa Alaikassalam” ya Mika Masa hannu had’e da zarewa.
Murmushin gefen Baki yayi yace “Farees it seems like haryanzu fushi kake Dani ko?”
“Fushi Kuma a Kan me?”
“Action speaks louder than voice farees”
“Wai Dan Allah me ke faruwane? Kun Sani a duhu”
Nan Hashim ya fad’a Masa tsaki yayi yace “Wai duk wannan akan Diyya ne? To farees ai wahalar da kanka kake tunda yanzu haka maganar aure ne a tsakanin Diyya da hash”
Zaro Ido yayi yace “Don’t tell me,are you serious?”
“Yeah am serious sun dai daita ai, infact mata biyu zai aura”
Yar karamar dariya yayi yace “Amma dai wasa kake ko?”
Hashim yace “A a da gaske ne, and it’s a long story”
“To mu shiga daga ciki mana”
Suna shiga ya kawo musu lemon gora da cups, Nan Hashim ya labarta Masa komai da komai.
“Tirkashi,yanzu duk su biyun zaka aura?”
“Eh ya Zama Dole, bazan ‘boye muku ba naso Diyya a baya Amma a yanzu duk bana jinta a Raina Kamar Asiyah, Ina ji bazan iya rubuwa da ita ba,auren Diyya da zanyi don farin cikin Asiyah ne ba don yin kaina ba”
Farees yace “To Kai kana ganin auren su duk su biyun shine mafita karfa ka d’auki abunda baza ka iya ba”
“Hmm insha Allah Zan iya Asiyah Bata da matsala don Sam bata kishi da ita Amma kaga Diyya hmm”
Faisal yace “That’s the difference between babba da yaro Kenan Asiyah na Kara girma tana sanin ciwon kanta zata yi”
Farees yace “Ko Kuma su had’a maka Kai su Rika gara ka”
Dariya duk sukayi Hashim yace “Wato
Sun samu garegare ko?”
Farees yace “Kai dai ka sani” ya Maida kallon sa ga faysal “Kai ya labarin Yar budurwar taka?”
“Hmm Kai dai Bari,magana tayi karfi a tsakanin mu Amma yarinyar Nan ta samu wani gara Mai tsuke wando, babu irin rashin mutuncin da bata shuka min ba”
Dariya Hashim ya shiga yi yace “Yaushe akayi haka Dan Allah bani da Labari”
“Ai Kaji matsalata da Kai Kenan shiysa fa ban fad’a maka ba don na San Hali”
Cikin dariya yace “Am sorry Abokina abun ne sai a hankali duk yanda take mutuwar son Kan Nan har zata iya ganin wani?”
“Gashi kuwa tayi”
“to me zai Hana ka leka gidan su Yesmin, yarinyar na da nitsuwa sosai”
“Ehhhh ka kawo shawara Mai kyau Amma kasan ban Santa ba”
” Ka Santa ka dai manta da ita ne,sai ka ganta kawaii”
“To yanzu yaushe zamuje?”
‘dan jingina Hashim yayi a jikin kujerar da yake zaune ya zaro wayar sa chan ciki yace “Sai na shirya”
“Hash da ace za a baka mulkin Nigeria da mun shiga uku”
Farees yace “abun harda warayyane Nima a nema min Mana ko Asiya zaka bani” cike da zolaya yake maganar.
“Tab Ashe zanyi kisa,but idan kana so Zan had’a ka da kanwar Asiyar”
“Gani bola ko Kai ka kita bayan kasan yarinyar bata da ‘da’a”
” No wallahi bata da laifi idan vaka manta ba a cikin labarin da na baka asiri a ka mata Kuma yana karyewa Shikenan”
“Tun tashin ta take fama”
“Eh Amma idan aka kwana biyu bata Sha ba normal take sai an Kuma bata”
” Toh Allah ya bata lafiya”
Hashim yace ” Ameen”
Faisal yace “Kaga Sai a had’a bikin Rana d’aya”
Farees yace “Kai da ma ba a San da zaman ka ba”
“Kai din an San da naka ne?”
“Za a sani ai soon”
” Nima soon”
Dariya ya Hashim ya shiga yi yace ” Zaku Fara ko anjima idan kunyi nesa a Fara cewa I miss my favourite cousin this and that”
Nan suka fara Hirar yaushe gamo,sun cikin hirar ne wayar Hashim ta Fara ringing wakan M Shareef ne Mai taken Yar budurwa ta ya Budurwata Asiya sonki yay nisa a zuciya.
Farees da Faisal kallon juna sukayi suka kwashe da dariya Hashim yasan dalilin dariyar taso hakan yasa Bai kula su ba.
Ganin Sunan Safiyya a fuskar wayarsa yace “Farees mutuniyar kace fa”
“Kai haba,Kayi picking Mana”
Picking yayi cikin muryar Shagwab’a Tace “Prince ashe ka dawo? Tunda ka tafi baka nemi ba”
“am sorry princess manta wayata nayi a Nija shiyasa jiyan Nan na dawo”
“Amma shine baka nemi ni ba?”
“Sorry princess yanzu Haka na shiryaa ne Zan Zo ganin my princess”
Yar karamar tsalle tayi tace ” Dan Allah dagaske”
“Allah kuwa da gaske nake,gani Nan zuwa yanzu”
“To sai kazo”
Ganin farees sukayi ya tashi ya shiga d’aki Bai dad’e ba ya fito jikinsa sanye yake da shadda fari kal, yayi mutukar kyau, Hashim yace “Malam ina zuwa?”
“inda zaka je Mana,ai tare zamu je”
“Lallai aiki ya same ka”
Faysal yace “Daga Nan mu wuce gidan su Yesmin?”
Hashim yace “Allah shi kyauta”
Suka fice,motar da suka Zo dashi suka shiga Kai tsaye sai gidan su Safiyya.
????????????????????????????????
Please vote and Comment
MILHAT CE
YAR TERAWA
[ad_2]