Uncategorized

MATAR UBA 30

Ad

_____

💦💦💦💦💦💦💦💦     *MATAR UBA*

💦💦💦💦💦💦💦💦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

Ad

CHAPTER 30

NOT EDITED

Hashim na ganin ta ya yi saurin sakin ta, wayar sa ya zaro cikin dabara ya tura text wa Nana 

*ki shigo yanzu*

Baki a Bud’e take kallon ta tace “Asiya kece dama kina raye?” 

💦💦💦💦💦💦💦💦

……… Murmushi tayi Tace “Eh nice Mummy”

Baraka ji tayi wani Abu ya tsaya mata a makoshi Rai a ‘bace Tace “Sau nawa nake fada cewar ki dai na Kira na da mummy?” Gyara tsayuwar ta tayi tace Wai tukunna ma uban me ya kawo ki gidana?”

“Na dawo gidan mune”

“gidan ku ke dawa?”

“Ina nufin gidan Mahaifina”

Murmushin keta tayi Tace “Kan na rufe idona na Bud’e ki fice min daga gidana”

“Me ke faruwa a Nan na ganku haka?”

Nana ke musu Wannan tambayar, Baraka kallon ta kawaii tayi ta Maida kallon ta ga Asiyah Tace “Baza ki fice ba?”

Asiyah kawar da kanta tayi kamar ba da ita take ba, hannu takai zata mare ta Hashim yayi saurin rike Mata hannu.

Nuna ta yayi da ‘yar yatsata yace “Don’t you dare try it,idan Kika kuskura Kika sa hannu ki ajikin ta wallahi wallahi sai na sa an Kama ki and I’ll make sure that babu Wanda ya isa ya fiddo ki”

Cike da mamaki take kallon sa Tace “And who the hell do you think you are da zaka Zo har cikin gidana ka nemi Gaya min magana,Kar ka manta kana matsayin d’ane a wuri na tunda auren ‘yata zakayi,Yar da na tsuguna na Haifa for that matter”

Yar karamar dariya yayi yace “eh hakane matsayin d’a nake a wurin ki,tunda Yar ki nake son aure, Amma ba Yar da Kika tsuguna Kika Haifa ba”

Cikin rashin fahimta murya na rawa Tace “Ban gane ba me ka… Kkk…nufi?”

“Ina nufin tunda Masoyiya yata ta dawo Safiyya bata da sauran gurbi a Rayuwata”

Safiyya fashewa tayi da kuka Tace “Dan Allah Hashim Kar ka min haka Dan Allah”

Har cikin ransa baya son ganin kukanta sabida a matsayin kanwa take a wurin sa Amma yayi burus yace “Kiyi hakuri Safiyya ke Kan ki kin San ba ke nake so ba Asiyah nake so”

“Amma kamin alkwari zaka aure ni yanzu kuma kace ka fasa please don’t do this to me”

Baraka tace “Munafuka algunguma Kinga daga zuwan ki kin ‘bata min komai,wallahi Baza ki zauna min a gida ba ki koma chan inda Kika fito ki cigaba da karuwanci ki”

“Babu inda…..”

Nana Ce tayi saurin katse ta Tace “A a Baraka kar kiyi haka duk lalacinta Nan gidan sune”

Baraka Tace “Amma kin San….”

“Kar ki damu zan fad’a miki dalili na,Zo mu shiga daga ciki” hannun ta ta riko ta maida kallon ta ga Asiyah Tace “D’auki kayanki ki shiga kinji?”

Kai kawaii ta d’aga Mata alamun toh.

Suna shiga Nana Tace “Wai dama Asiya bata gidan Nan?”

“Eh bata Nan”

“Toh Amma ina taje haka kin San min kwana biyu ban san me ke faruwa ba”

Nan ta kwashe mata yanda akayi ta zuba mata ruwan barkono a ido,har izuwa yanda baba mai gadi ya kaita asibiti “tun daga Wannan ranar ban sake sata a idona ba sai yau”

“Toh Allah ya kyauta”

” Ameen.”

” Yauwa kina jina? dalilin da yasa nace Kar ki koreta shine tunda har tayi gangancin dawo wa sai kiyi Mata abinda tun a baya bakiyi ba”

“kinyi gaskiya lokaci yayi da zan kashe ta kowa ma ya huta”

“A’a ba kashe ta ya Kamata kiyi ba, wahalar da ita zakiyi ba dare ba Rana da kanta zata tafi ta bar miki gida Kinga yaron Nan d’an gidan Alhaji shettima Yana da karfin da zai tsaya mata so nake ki kwantar da hankalin ki, a tsulale zamuyi maganin shegiya”

“Hakane kawata shiyasa nake sonki,Amma daga Ina kike ne?”

“Nazo wucewa ne nace bari na tsaya mu gaisa”

“Ina zakije Haka?”

“umm…umm hajiya tace ba lafiya”

“Ayya zazzabi ko?”

“Eh kin San Kuma jikin tsufa” mikewa tayi Tace “To ni zan wuce idan na samu sarari zan Zo mu Sha hira”

“To Shikenan sai na ganki.”

Tare suka fita Baraka wani irin mugun kallo tayi wa Hashim da Asiyah ta buga uban tsaki ta Maida kallon ta ga Nana “Muje nayi dropping ‘dinki”

“A’a Kar ki damu da mota ta na taho?”

“Tana Ina,ban ganta ba?”

“A waje na barta”

“Alright take care.” Ta shige motar ta, ta fice.

Wurin su Hashim Nana ta nufa tace “Kai Kuma ka yi maza ka bar gidan Nan Kuma Kar ka Kuma zuwa gidan Nan”

Cikin muryar kuka Safiyya Tace “Sabida me zakice Kar ya Kuma zuwa ni Kuma ya zanyi?”

“Banda ke Safiyya me zakiyi da na mijin da baya son ki?”

Zama tayi a kasa ta fashe da kuka, cikin sauri Asiyah ta nufe ta rike ta tayi, Safiyya da dukkanin karfinta ta ture ta.

Da gudu Hashim yayi kanta d’agota yayi ya rungume ta a tsawace yace “Baki da hankali ne?”

“Eh bani da shi” 

“Hmm ba laifin ki bane,Queen tunda kema kin San yarinyar Nan Bata da hankali ki daina shiiga harkarta”

“To Shikenan King”

Peck ya mata a goshi yace “please ki shige ciki kinji?”

Murmushi tayi Tace “Toh Shikenan take care”

“You too” ya shafa fuskar ta ya tafi.

Yana tafiya Asiya ta d’auki jakar ta ta shige, Nana Ce ta riko Safiyya ta kaita har d’akinta sai da ta rarrashe ta takwantar da hankalin ta kana ta yi tafiyar ta.

A gidan ta ta tarar da Hashim, “yauwa Hashim kamar kasan ina son magana da kai,banji dad’in abunda kayi wa Safiyya ba, yarinyar Nan fa Bata da matsala ko kad’an kawaii ta had’u da sharrin uwane”

Ad

_____

1 2 3Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button