Uncategorized

MATAR UBA 30

Sa mata kafa tayi ta Fad’i ta shiga Kai mata duka ta ko ina, Safiyya ihu take tana neman d’auki Amma bata daina zagin Asiyah ba ,Asiya kuwa yanda kasan ta samu jaka Saida ta ake ta son ranta ta sake ta,ta Kuma hankad’ata waje, ta nuna ta da yar yatsa “idan Kika Kuma shigo min d’aki ba tare da izini na ba sai na karya ki”

Cikin muryar kuka Tace “Allah ya Isa muguwa azzaluma ban yafe ba”

Ganin Asiya tayi kanta da gudu ta tashi ta wuce d’akinta.

Dariya ma abin ya bawa Asiyah, ta ja kofarta ta rufe a bayyane Tace “Yau Kam nasan za a min welcome yanda na daka mata ‘ya Nima hakan za a min,ko da yake duka ya zame min man shafawa duk da na kwana biyu” tana kallon fatar jikinta.

Karar wayarta ne ya sanya ta d’auko purse d’inta ta d’auko wayar gamin Hashim ne tayi Murmushi Tace  “King”

“Umm queen ni gaskiya a canza min sunan Nan bana so”

“Laa to me yasa?”

” Haka kawaii bana so”

“But da sunan Aunty take Kiran ka dashi”

“Eh na sani ke daban ita ma daban Wannan sunan da take kirana dashi ne,saboda haka a canza min”

“To yanzu fad’a min wani suna kake so na Rika Kiran ka dashi?”

“koma wanne Wanda ta dace dani”

“Toh idan na Kira ka Excellency yayi?”

” Idan ya Miki Nima yamin”

“To Nima a canza min queen din nan tunda sunan da kake kiranta dashine.”

Cikin murya Mai sanyi kamar rad’a yace “First Lady”

Murmushi tayi Tace “I like it”

“Like ma ba love ba?”

“Sorry to I love it”

” Ban yarda ba cire to d’in”

Yar karamar dariya tayi Tace “I love it”

“Yauwa yar Budurwata I love you”

” I love you too Dan Saurayina.”

Hirar su suka Sha sosai har aka Fara kiraye kirayen sallar azahar,yace mata zashi masallaci sannan zai bawa Nana CC camera ta kawo mata,Sabida gudun matsala.

Asiyah na idar da sallah ta kwanta, baccin ta take hankalin ta kwance ba ta tashi ba har Saida aka Kira sallar la’asar ban d’aki ta fad’a ta watsa ruwa had’e da d’auro alwala tayi sallah,cikin ta ne ke kugi wani irin yunwa take ji,da sauri ta tashi tayi hanyar kitchen, indomie ta d’aura don shine abinda zaifi Mata saukin girkawa agurguje ta daka Kayan Miya ta had’a indomie, tana saukewa ta juye a plate ta Fara ci Kennan Yar aiki ta shigo kallon ta tayi Tace “Wane Ne ke?”

“Yar masu gida” kawaii Tace Mata tab’e baki tayi,tayi ficewar ta,Saida ta cika cikinta ta d’auko lemu mai sanyi ta kora kana ta fita, a parlor ta tarar da Safiyya da Baraka,cikin girmawa ta gaishe ta tsaki tayi had’e da kawar da kanta.

Tab’e Baki Asiya tayi a zuciyar tace “ke Kika sani”

Daki ta koma ta d’auko wayarta fita tayi ta zauna a garden na gidan.

Chatting d’inta take hankalin ta kwance da farin cikin ranta,tana cikin chat din ne Diyya ta Kira ta, ta Kara mata karfin gwiwa akan ta dage da azkar tayi mata godiya sosai.

Bata koma cikin gidan ba har Saida taji ana Kiran sallar Maghriba, Asiya mamaki ne ya Kamata tana ta jiran a dake ta ko Kuma a balbale ta da masifa Amma shiru kake ji,har garin Allah ya waye Basu kulata ba ita ma Bata kula su ba.

Asiyah na kwance a d’aki taji tana bukatar Shan Abu Mai sanyi, a hankali take saukowa daga Kan stairs maganar da taji sukeyi ni Yasa tayi saurin komawa baya don tabbatar da abinda taji “Mummy na fad’a Miki ni fa bazan sa mishi komai yasha ba,nafi so ya Soni  tsakani da Allah bada asiri ba”

“Banda ke Safiyya kina ganin idan Wannan yarinyar tana raye ina zai kulaki? Ita ma asirin ta Masa Amma ke zan had’a Miki Mai karfi Wanda bazai guje ki ba”

“But Mummy asiri fa na karyewa”

“Haba Safiyya, kina da ni ai baki da wata matsala bazan Bari hakan ya Faru ba”

“To mummy na amince”

” Yauwa Daughter ga Wannan shi Zaki sa Masa a abinsha”

Karb’a tayi Tace “To Amma taya za’a yi Sha bayan kin san ba zuwa gidan Nan zaiyi wurina ba”

“Kiranshi zakiyi yazo idan ta Kama har kuka ki Masa”

Fridge d’in dake parlor ta nufa ta d’auko baban gorar Exotic ta karb’i maganinn ta juye duka a ciki Tace “Kan yazo ya jika sosai maza jeki ki kirashi ni yanzu zan fita zan ajiye Miki shi a marfin fridge d’in”

” To mummy sai kin dawo” saukowa Asiyah ta nufi hanyar kitchen kamar bata ga kowa Baraka a zuciyar ta tace “yarinyar Nan ta koyo rashin kunya” a bayyane kuma Tace “Asiyah Zo Nan”

Ba musu tazo,durkusawa tayi Tace “Ke Baki San yanda ake gaisuwa bane?”

“Yi hakuri mummy ban lura da ku bane”

” Mtsww matsalar kice Wannan tunda Allah yayi kin dawo sai ki d’aura daga inda Kika tsaya” ” ban fahimta ba Mummy”

“Ina nufin aikin gidan Mana,sai ki shige d’aki ki kulle Kanki kamar wata uwar mace”

” Insha Allah zan Fara”

“Da kin taimakawa kanki, tashi ki bani wuri”

 Tashi tayi ta koma d’akinta ,tana shiga ta Kira layin sa Yana picking ta fad’a Masa plan d’in da ake shiryawa, Yar karamar dariya yayi yace “Kar ki damu ba zuwa zanyi ba”

“A a kazo please”

“Meyasa Asiyah so kike ta mallake ni?”

“A’a kasan bazan so hakan ba kawaii dai kazo I’ll handle it bazan bari kasha ba nasan zata Kira ka.”

” Eh ga kiranta ma Nan ya shigo”

“Good sai kazo” ta katse wayar.

Tana jin karar motar Baraka na barin gidan ta leko ta Duba ba kowa a parlor cikin sauri ta nufi fridge ta d’auke exotic d’in ta d’auko wani ta ajiye a madadinsa tayi saurin komawa d’akinta ta juye a toilet.

Safiyya tayi mamakin yanda akayi ya amince zaizo cikin sauki, ba tayi Tunanin komai ba itae duk a wautanta tausayin ta yaji.

Bai d’au lokaci ba ya karaso gidan Asiyah ya Fara kira jiran ta yayi a waje Saida suka d’auki tsawon Mintuna talatin Kan ta fito ta koma cikin gida, tana shiga ta Kira Safiyya ya Sanar da ita ya shigo, fitowa sukayi suka zauna a parlor yace Yana “Yau anan zamu zauna?”

Murmushi tayi tace “Eh ai yanzu ka Zama na gida”

Tab’e baki yayi yace “Okay,gani kince kina son ganina?”

“eh dama…..dama….”

“Dama me? Kiyi magana please Ina da abubuwan yi a gabana na baro Nazo Nan,idan baki da abin fad’a zan tafi”

“Sorry dama so nake na baka hakuri akan abunda nayi maka nayi wasa da emotions d’inka bayan Kuma nasan bani kake so ba”

“Bakomai ya wuce a gaskiya naji dad’i da Kika gane gaskiya”

Murmushi tayi Tace “thanks for understanding, barina kawo maka abinsha ko?”

“Okay dama ishi nake ji”

” Me zaka Sha to?”

“As usual kin San favorite d’ina ai”

” Hakane”

Tashi tayi ta d’auko ta tsiiyaya Masa a cup ta mika Masa da bismillah ya fara sha, Asiyah dake sama tana kallon su abun dariya ya Bata.

Sai da ya shanye ya ajiye cup d’in.

????????????????????????????????

PLEASE SHARE AND COMMENTS

MILHAT CE

YAR TERAWA ????️

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button