MATAR UBA 4

Baraka Kuma ta koma kitchen, bayan ta cire uniform ta dawo dinning table ganin ba abincin ta nufi kitchen a dai dai Nan ta samu Baraka na fad’in “Shegiya mayya idan Kika ci abincin Nan Dole ki mutu kamar yadda yar Uwar ki ta mutu guba ai ba Wasa bane” tana b’arbad’a guban akan abincin, Asiyah ta tsorata sosai ta rasa yanda zatayi a hankali take tafiya har ta haura sama.
Tana kallon duk motsin Baraka, ganin Baraka ta fita daga kitchen d’in ta Shiga d’aki da sauri ta sauko ta Shiga kitchen d’in ta zuba abincin a bakar leda sannan ta wanke plate d’in tass Kan ta sake zuba wani ta aje sai tayi saurin fita ta koma d’akin ta.
Baraka na fitowa ta Shiga kiranta a nitse ta fito Tace “Mummy gani” ganin Daddy ya fito ta shafa Kanta Zo muje kici abinci ko?” Tana Mata Murmushi itama Asiyah Murmushin ta Mata.
Asiyah taci abincin Nan sosai don tun rasuwar Anisah ba a bata abinci sabida Daddy baya gida, bayan ta gama cinyewa Baraka Tace “Kin koshi ko na Kara Miki?”
Tace “Na koshi”
“Naman fa baza ki Kara ba?”
Murmushi Baraka tayi Tace “Nagode na koshi”
Murmushi tayi Tace “toh Allah ya Miki Albarka”
Ta amsa da “ameen” kwashe plate d’in tayi ta Kai kitchen, Baraka na jira taga ta fad’i Amma shiru Nan da Nan hankalin ta ya tashi Daddy yace “Yadai Baraka ya Naga fuskan ki haka? Kina Laifiya kuwa?”
Kirkiran Murmushi tayi Tace “Lafiya Lau”
Kallon ta yake yi shi Sam bai yarda ba ta sake cewa “Kin tabbata babu abinda yake damun ki?”
Mikewa tayi Tace “Ina zuwa bari na d’auko wayana”
Yace “Okay” tana Shiga d’aki ta kira Nana, Nana na picking Tace “Nasan zaki kirani Amma ban d’auka a yanzu Zaki Kira ba”
Cikin damuwa Tace “Qawata ba wannan ba please don’t mind me d’azun b’acin Raine, kin san mene ne kuwa?”
Daga d’ayan b’angaren ta amsa da “Sai kin fad’a”
“Umm yarinyar Nan nasa Mata gubar Nan a cikin abinci kamar yanda kikace Amma baiyi Mata komai ba”
“Haba haba kin San karfin maganin Nan kuwa kana cin Loma d’aya zai kashe ka”
Tace “Wallahi ta cinye abincin Nan duka ba ta rage komai ba Kuma nasa maganin fiye da yanda akace”
Nana ta ce “Ikon Allah,abin da mamaki Kam”
Baraka Tace “Ina gani fa kamar yarinyan Nan mayyace, Amma duk maitan ta na fita, Bari na Koma parlor anjima zan Kira ki” sai ta katse wayar tana saukowa daga Kan step sai ta zame, ihu ta fara yi Wanda yasa Daddy ya taso da gudu, Asiyah ma ta fito daga d’akin a tare suka nufe ta yayi kokarin d’aga ta sai yaga jini na bin kafan ta Baraka na ganin jini ta fashe da kuka Tana fad’in “My baby my baby” sai rarrashin ta yake yasa ta a mota sai asibiti ,suna zuwa likita ya tabbatar da cikin ya lalace kuka ta Shiga yi har suka dawo gida.
A ranar ba tayi bacci ba kwana tayi tana kuka Daddy yayi rarrashin duniya Taki sai ya hakura ya Kyale ta.
*WASHE GARI*
Ta Kira Nana ta Sanar mata, Nana na Jin hakan ba b’ata lokaci tazo ta tarar dasu a parlor tana kwance a jikinsa Yana ta aikin rarrashin ta Yana fad’in “Baraka ki daina kuka insha Allah Zaki samu wani cikin Allah da ya bamu wannan shi zai sake bamu kinji?”
Bayan Nana sun gaisa yace “Dan Allah Nana ki rarrashe ta tun jiya take abu d’aya”
Murmushi tayi Tace “Kar ka damu insha Allah zan Mata magana”
Shafa kanta yayi yace “Ni na Shiga ciki zan d’an kwanta”
Sai ya haura sama.
Nana na ganin ya Shiga Tace “Baraka Taya Za’ayi mijin ki zai ce miki kar kiyi kuka,kiyi kuka sosai har sai hawayen ki sun kafe”
Cikin rashin fahimta tace “kamar Yaya? Nayi kuka ban fahimce ki ba?”
“Eh Mana Taya zaice Kar kiyi kuka bayan shekara d’aya d’aya har uku baki samu ciki ba, zuwa gidan bokaye da malamai cikin Nan ya samu ya lalace Kuma yace Kar kiyi kuka?”
A tsawace Tace “Me yasa Baki da hankali ne Nana ke Wace irin qawace? Ke yanzu ba Kya Jin tausayina?”
Yar karamar dariya tayi Tace “Ke ai ba abinda tausayi bace ba Sadeeq ne abin tausayi” tashi tayi Tace “Anyways Naga jikin naki da sauki tunda har kina iya masifa Kinga tafiya ta” tana Kai Nan tayi ficewar ta.
????????????????????????????????
PLEASE SHARE AND COMMENT
*MILHAAT CE YAR TERAWA*
[ad_2]