MATAR UBA 8
???????????????????????????????? *MATAR UBA*
????????????????????????????????
_(A True Life Story_ )
*Short story*
“`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“`
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram
https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️
_(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.
???????? *MATAR UBA* ????????
_(A True Life Story)_
*Short story*
“`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“`
Follow me on Wattpad @Milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION*????????️
_’kungiya d’aya tamkar da dubu_
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayiwa Yan Uwa Mata nasiha,Allah ya bani ikon gama shi lafiya kamar yanda na Fara lafiya ameen.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* Much Love.
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Not Edited
CHAPTER 8
????????????????????????????????????????????
……….. Asiyah jiki ba Karfi ta tashi ta mike ta haura bedroom d’inta, a galabaice ta Shiga bathroom ta Watsa ruwa had’i da alwala, tana fitowa ta shafa Mai sannan ta d’auko doguwar Riga da doguwar Hijab d’in da take sallah ta zurma sannan ta tada sallah bayan ta idar ta jero addu’o’in neman tsari da ga sharrin Baraka da Kuma nema mata gafara da Kuma neman gafara wa Daddy, mummyn ta da Kuma Anisah.
Jiki a Sanyaye take saukowa daga step din ganin ba kowa a parlor hakan yasa ta kusa kanta a cikin kitchen, dube dube ta Shiga yi ko zata Samu sauran Abinci Amma babu duk an wanke kwanukan, girgiza Kai tayi Had’i da rike kwankwason ta a fili Tace “Ya Allah ka kawo min karshen wannan abun” Nan ta hangi wata bakar leda akan dakalin kitchen d’in tayi saurin bud’ewa ganin garin kwaki ne a Ciki hakan yasa ta San shine abincin ta gashi d’an kad’an ne tasan bazai koshar da ita ba murmushin gefen baki kawaii tayi ta nufi washing hand basin ta d’auki roba ta juye a ciki, ba b’ata lokaci ta jika ta Shiga Sha sai da ta Shanye,ji tayi kamar bata Sha komai ba amma ko ba komai ya tare Mata wani gun, d’akin ta ta Koma ta gabatar da sallar la’asar bayan ta idar ne ta d’auko uniform d’in islamiyar ta sannan ta d’auki jakarta ta fice daga gidan, dake ba nisa daga gidan su Bata d’au lokaci ba ta Isa, bayan sun tashi suna tsaye da shamsiyya sai ta ga wucewar motar gidan su ya shigo, wani irin muguwar harara safiyya tayi musu had’i da tskai Mai Kara sannan ta shige motar suka fice daga makarantar.
Shamsiyya mamaki ne ya rufe ta baki a bud’e take kallon bayan motar har suka fice ta daina ganin su sannan ne ta Maida kallon ga Asiyah Tace “kamar safiyya na gani ko? Ko ba ita bace?”
Murmushi tayi sannan tace “Eh itace” tana maganar ne tana kokarin b’oye abinda ke damin ta, Kai shamsiyya ta girgiza Tace “Kina so kice min har yanzu Mummy Baraka Bata daina abinda take ba?”
“Shamsiyya sai ma abinda ya karo kawai ki cigaba da sani a addu’a”
“Ina kai Qawata Amma Ni abinda ya bani mamaki shine naga har safiyya ta wuce ba tare da ta mana Magana ba sai ma wani irin kallo da ta mana”
“Ni kaina lamarin safiyya na d’aure mini Kai, daga jiya zuwa yau ta sauya min na rasa dalili”
Tab’e baki tayi Tace “Ai nasan Dole za a Rina, ta yaza a yi mummy ta zuba Muku Ido bayan irin son da safiyya take Miki Kuma ta barku, idan ba ta Mata muguwar hud’u ba, to tabbas ta Mata wani abun”
“Ke dai Allah ya shirye ki baza ki canza Hali ba ya kamata ki sani shi fa zato zunubine ko da ya kasance gaskiya ne”
“Zaki Fara wannan wa’azin naki” karar horn da ta ji ne yasa su juyo was a tare, shamsiyya Tace “Zo Muje ganan driver d’in mu sai mu ajiye a hanya”
“A a Kar ki damu zan taka da kafa na ai ba nisa” shamsiyya tayi tayi da ita Amma ta ki hakan yasa sukayi sallama ta shige motar, Asiyah Kuma ta nufi hanyar gida.
A nitse take tafiya damuwar duniya ta had’u ta Mata yawa hakan Shiyasa ta Fara tilawar haddar ta acikin zuciyar ta.
Wani handsome guy na hango zaune yake a cikin mota black kirar Ferrari 2020 sai sheki take,baki a bud’e ya ke kallonta taka birkin motar yayi Wanda shi kansa Bai sai yayi ba abokin tafiyar ji yayi ya buge goshin sa sabida irin taka birkin da yayi da saurin ya dafe kansa Yana ambatan “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un” d’ago kansa da yayi yaga har ya fita, da saurin gaske ya Sha gaban ta, yace “Emmata ji Mana” wani irin kallo tayi Masa daga sama har kasa, dogo ne,Fari ne tass fuskan sa d’auke yake da gemu irin Wanda samari ke yayi bai cika Masa fuska ba Wanda shi ya Kara kawata Masa fuskar say, hancin sa dogo ne sosai har b’aka, sai d’an madaidaicin pink lips din sa wanda ya Dace da fuskar, kunnen sa sanye yake da earpiece sannan yasa pea cap, sanye yake da farin T-SHIRT had’i da Wando Jean Mai Ruwan Navy blue, sai da ta Kare Masa kallo Tass Kan tayi kokarin tafiya.
Da sauri yasha gaban ta yace “Please am sorry, my mistake Sallama ya kamata na miki, Assalamu Alaiki” Yana maganar hannayen sa a hard’e guri gudu, fuska a d’an tamke ta amsa da “Wassalam”
Yace “Dan Allah Emmata idan baza ki damu ba zan iya sanin sunnanki?”
Kallon sa kawaii tayi sannan ta sake kau da kanta, a Karo na biyu ta sake fad’in “Tun da na ganki naji zuciya ta ta kamu da sonki, na ga bazan iya barin ki ki wuce ba tare da na Miki magana ba ji nake kamar bazan iya Rayuwa babu ke ba”
Ganin tayi Shiru ba ta da niyar bashi amsa sai yayi kokarin matsowa kusa da ita, Asiyah ganin hakan tayi saurin bin ta gefen ta sa arce da gudu, magana yake Amma ina bata saurare shi ba.
Hannu ya d’aura a kwankwason sa sannan ya girgiza Kai huci yayi Had’i da fad’in “Kiyi iya gudun ki insha Allah sai na Nemo ki” murmushin yayi Had’i da girgiza Kai a Karo na biyu, sai ya nufi motar ya Shiga ya zauna.
Abokin tafiyar tasa yace “Kai Amma anyi soko wallahi yanzu akan wanchan Yar Yarinyar chan kake kokarin hallaka Ni?”
A hankali ya juyo ya kalle shi ganin yanda bakin sa ya kumbura yasa shi fashe wa da dariya yana nuna fuskar abokin tafiyar nasa sai da yayi Mai isar sa yace “Faisal kaga goshin ka kuwa?”
Rai a b’ace yace “Ina zan gani tunda makahone Ni, Amma wallahi Hashim ka Raina min wayo tsabagen mugunta da rashin tausayi irin naka ka ji min rauni Kuma ka tsaya kana min dariya?”
Wanda aka Kira da Hashim na gani Yana kokarin rufe bakinsa da hannun sa ganin ran abokin nasa ya soma b’aci yace “Am sorry my man wallahi baka yanda yarinyar Nan ta tafi da imani na bane ba, kasan wani irin shock da naji kuwa?”
Tunda Hashim ya Fara magana Faisal yake kallon Adams Baki a bud’e hannun sa Kuma a Kan goshin sai sai da ya Bari ya ida maganar dake bakin sa kana yace “Hashim Kenan kana da abin mamaki, naga Kaine kullum kake fad’in baka da lokacin Mata Kuma baka ga yarinyar da zaka bud’i Baki kace kana sonta ba?”