Uncategorized

MATAR UBA 9

????????????????????????????????          *MATAR UBA* 

????????????????????????????????

       _(A True Life Story_ )

            *Short story* 

 “`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“` 

Follow me on Wattpad @milhaat

Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️

 _(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________

*MATAR UBA*  Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.

Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK*  much Love.

???????? *MATAR UBA* ????????

     _(A True Life Story)_

           *Short story*

 “`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“`

Follow me on Wattpad @Milhaat

Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION*????????️

 _’kungiya d’aya tamkar da dubu_

https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa

_____________________________

 *MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayiwa Yan Uwa Mata nasiha,Allah ya bani ikon gama shi lafiya kamar yanda na Fara lafiya ameen.

Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* Much Love.

 *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

Not Edited

CHAPTER 9

????????????????????????????????????????????

………..Asiyah da Sallama ta shiga amma babu Wanda ya amsa tab’e Baki tayi alamun ko a jikinta, ganin safiyya a zaune ne a Kan sofa abin ya Bata mamaki cike da mamaki take kallon ta Tace “Safiyya Ashe dama kina Nan kina ji Ina Sallama ba ki amsa ba?”

Shiru ko kallon ta ba tayi ba bare ta amsa mata kad’a kai tayi Tace “please Safiyya idan wani abun na Miki tell me bana Jin d’adin sabon halin da Kika Fara min daga jiya zuwa yau”

Wani irin muguwar kallo ta Mata Kan ta Tace “Idan kin gama tambayoyin naki mummy na neman ki.”

Sai ta cigaba da kallon da take.

Asiyah kanta ne ya d’aure a zuciyar ta Tace “ko dai maganar shamsiyya gaskiya ce Anya ba mummy ba ce ta Shiga tsakanin su? In ko hakane ta cuceta ta cutar da Safiyya” cikin Wannan tunanin ne ta karasa kofan d’akin mummy tasa hannu zata kwankwasa kofar sai ji tayi Baraka na dariya har da buga kafa hakan tasa ta d’an tsaya don Jin abinda take fad’a “ke dai qawata bari, Shiyasa nake son ki kw d’in ta dabance na yi yanda kikace nasan Dole ita da kanta zatace ta hakura da makarantar.”

Dariya ta sake yi kana Tace “Haba ai Asiyah kamar kwallo take a hannu na ko ince kamar waina duk inda nasi zab juya ta gamar yanda na juya Ubanta, Qawata na so ace na kashe ta kamar yanda na kashe Anisah da Uwar su, Amma she is my next target.”

Asiyah dafe kirjin ta tayi ki tayi duniyar na juya Mata kanta Kuma ya Shiga tsarawa kamar zai tsage gida biyu, ganin tana kokarin fad’i wa ne tayi saurin jingina jikinta a jikin bango, ta d’auki tsawon lokaci a haka, a hankali ta nufi d’akin ta babu abinda ke Mata yawo a Kai da Kuma zuciyar ta sai kalmar da taji “Na so ace na  kashe. Ta kamar yanda na kashe Anisah da Uwar su” cikin Wannan tunanin ne ta zauna a bakin gado tare da have Kai da gwiwa “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un ashe itace sanadiyar mutuwar Mummy na,farin cikina Kuma sanyin idanuwata? Me suka Miki da har suka chanchanci mutuwa” kuka ta saki Mai cin Rai kuka take sosai Wanda tunda take Bata tab’a irin sa ba Jin ana kwankwasa kofar tane yasa tayi saurin mikewa had’e da share hawayen ta bud’e kofar ganin mummy ce tayi saurin gaishe ta Bata amsa ba, kallon ta take nason fahimtar abinda ke damin ta Amma ta kasa ta ce “Ke kukan uban me kike?”

Cikin shakewar murya Tace “Ba kuka nake ba”

Taking ta Yi sannan Tace “Safiyya Bata fad’a Miki Ina neman ki ba?”

“Ta fad’a min so nake na cire uniform sai nazo”

Tab’e baki tayi ta Mika wata leda had’i da fad’in “ki kaiwa Maman Yesmin” tana mika Mata ta juya zata tafi Asiyah Tace “Mummy kud’in machine fa?”

Wata muguwar harara ta Mata sannan Tace “me amfanin wad’an Nan?” Tana maganar tana nuna kafar Asiyah.

Asiyah ita ma kallon kafan nata tayi sannan Tace “Tafiya” “good to dasu Zaki tafi bani da kud’i”

Cikin sanyin murya Asiyah Tace “Mummy gidan fa da nisa gashi yanzu Maghriba ta kusa zan yi dare a hanya”

“Wannan Kuma ke ta shafa”

Kai a kasa Asiyah ta shige d’akin ta.

Canza Kaya tayi tasa abaya sannan ta d’auki hijab Wanda ya d’an rufe mazauninta kad’an sannan ta fice daga gidan, tafiya take ta na zuba saurin don Kar dare ya Mata a zuciyar Tace “In ba mugun ta da rashin imani ba ga motoci a gida sannan ga driver ai za’a ce ya kaini” maganar da d’azun ce ta sake dawo Mata tafiya take tana kuka ganin bazai amfane ta ba ta Shiga yin addu’o’in da duk suka Zo bakin ta  a Haka har ta isa estate nasu Nana (Maman Yesmin) tana Isa Taki ana kiraye kirayen  sallah da sallama ta Shiga Yesmin ce ta amsa ganin Asiyah ce da gudu ta nufo kofar ta rungume ta tana fad’in “Oyoyo aunty Asiyah yau kece a gidan namu?”

Nana Jin an ambaci sunan Asiyah yasa tayi saurin fita daga kitchen a tsawace Tace “Ke Yesmin ba ki da hankali ne? Sau nawa nake Miki warning a Kan ki daina Shiga har kar mayyar yarinyar Nan?”

Yesmin kai a kasa sai ta Shiga Wasa da yatsunta hanun ta.

Asiyah cikin girmawa ta gaishe ta kamar bata ji haushin maganar ba, cike da gadara ta amsa gaisuwar Kan Tace “Yesmin karb’i ledan hannun ta” cikin sauri ta Mika Mata sannan ta nuna Asiyah da Yar yatsa Tace “Get out from here Jaka kawaii”

Murmushi tayi sannan ta ce “Sai da safe mummy” sai ta fice daga gidan, Nana a zuciyar ta Tace “Wannan Wace irin yarinya ce da Bata da zuciya ko kad’an duk abinda ka Mata baya b’ata Mata Rai” 

Murya Yesmin ne ya dawo da ita daga tunanin da ta Lula “Na’am me kikace?”

Nana ke yiwa Yesmin tambayar nan, a Karo ja biyi ta kuma cewa “Mummy cewa nayi meyasa kukeyi Mata hakane ko tausayin maraicin ta ba ku ji?”

“To sannu uwata, kina jina Yesmin daga yau idan Kika Kuma Shiga harkar da ba naki ba sai na karya Miki hakori,wuce ki bar Nan” Yesmin turo Baki tayi had’e da bubbuga kafa Tace “Ku dai Rika Sara Kuna duba bakin gatari don wallahi Allah bazai Bar Ku ba”

“Lala lala Yasmin Ni kike fad’a wa hakan?” Ganin tayo kanta hakan yasa ta shige d’akin ta da gudu had’e da rofo kofan ta Ciki, cikin b’acin Rai Tace “Yau Ni da ke a gidan Nan Yesmin” har wani huci take.

******

“Son Dan Allah ka tashi kaje kayi dropping d’in Addar ka a gida”

Turo Baki yayi cikin shagwab’a yace “Mami Wai Dan Allah meyasa ake so a Maida Ni driver d’inta ne? Ta Kira mijinta Mana yazo ya d’auke ta, kuma ai tana da motar ta ko?”

Murmushi irin nasu na manta Mami Tace “Hashim Kasan halin Fadeelah Sarai ba ta fiye son tuki ba Dan Allah tashi ka kaita kaga karfe takwas harta wuce”

Ba don yaso ba ya tashi ya fita ta d’auko key ya nufi parlor, Da gudu yazo ya rungume shi shafo kansa yayi had’e da d’aukan sa yace “Adnan bakayi bacci ba?”

“Eh uncle Hashim Kai muke jira ka Maida mu gida da Momy”

“To gani nazo Ina Islam take?”

“Gata chan a bayan Momy tana bacci” Yana nuna inda Fadeelah ke tsaye kallon su take tana Murmushi, Kai yasa ya fice ba tare da ya Mata magana, Sallama tayi wa Mami sannan ta bi bayan su.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button