Uncategorized

MATAR UBA 8

“Eh Haka nace Amma yau na gani tunda gashi ka gani na Mata magana Kuma na fad’a Mata Ina sonta”

Dariya Faisal ya Shiga yi Yana tafi yace “kaji mahauci waya ce maka Haka ake tinkarar mace daga had’uwa sai kace kana sonta, meyasa baza ka bari na saka a hanya ba?”

Tsaki Mai Kara yayi sannan yace “Amma ai kaga sanda na fita ko?”

“Ina na gani ji nayi kawai na buge goshina”

“Ina zakaji ka tsaya kana sana’ar chatting da Emmata”

Murmushi Faisal  yayi Yana shafa kasumabar sa sannan yace “Alhaji baka San d’adin chat da Mata bane wallahi shiysa”

“Kai ware dalllah, Ni yanzu Taya za a yi na sake ganin yarinyar Nan?”

“Oh Allah Kai Kuma abin ta Kan kwaila ka Fara”

“Eh d’in kasan yarinyar Nan tafi Wannan mahaukaciyar budurwar ka”

Kama Baki yayi yace “Babyn tawa kake Kira mahaukaciya?”

“To mene ne in ba mahaukaciya ba, yarinya tayi kwalli kamar Mai aljanu?”

“Lallai Hashim one zero kaci tuwo a kaina Amma ba komai zan Rama”

Dafe Faisal Hashim yayi sannan ya Shiga girgiza shi had’e da fad’in “am sorry am sorry yanzu dai please help me out, ya kake ganin za’a yi?”

Kau da fuskar sa yayi ya d’an yi shiru kana yace “Let’s follow her muga gidan su, don alamu sun nuna a unguwar Nan take”

Cikin murna yace “Good advice” Nan ya murd’a key suka bi bayanta.

Asiyah tunda ta bar gun bata daina gudu ba har sai da ta Isa bakin gate na gidan su, Kan ta dai daita nitsuwata sannan ta bud’e karamin gate ta shige Ciki.

Hashim da Faisal sai dube suke Amma Shiru kake ji basu ganta ba Yar karamar tsaki Hashim ya ja had’e da buga steering motar sa kan kana yace “Kamar aljana ta b’ata baat?”

Yana maganar Yana leka waje.

“To wa ya sani ko aljannar ce , don nayi mamakin yanda ka damu da ita a lokacin guda haka in……”

Hararar da yayi Masa ne yasa Faisal ta kasa karasa maganar da yake.

Sauka yayi a Kan titin yayi parking a gefen, Faisal yace “Kar ka damu tunda dai tana zuwa islamiya ta kwana gidan sauki gobe ba sai mu dawo ba?”

Murmushin samun nasara yayi yace “Thanks Abokina” Nan ya tada motar suka bar unguwar dropping d’in Faisal yayi Kan ya wuce gida bai tsawon lokaci ba ya Isa gida dake gidan nasu ba nisa.

????????????????????????????????????????????

Kuyi hakuri da wannan, sabida na Koma maranta.

Wattpad bana ganin vote an Comments d’inku alamu sun nuna Baku Jin d’adin book d’in sabida zan daina d’aurawa kawaii.

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button