MAYE GURBI Complete Hausa Novel

*Shafi na goma sha uku*
Wannan shine farkon ala’ka a tsakaninsu, wadda har ta kai su ga aure. Abu d’aya ya ‘kudurce a ransa duk ranar da Allah ya sake had’a shi da waccan yarinyar muddin ba tai aure ba, to ko ata biyu zai aure ta.
Sai kuma Allah ya bayyana ma sa ita a matsayin yayar matarsa.
Ya sha wahala matu’ka lokacin da ya fuskanci irin ala’kar da ke tsakaninsu, wannan ne dalilin da ya sa yanzu bai yi ‘kasa a gwiwa ba ya sanar da mahaifansa bu’katarsa.
Umma ta so ta hana maganar, amma sai Abbansu ya dan’kwafe ta ya hana ta, ya nuna mata hakan da zai yi bai haramta ba a addinin musulunci, sannan bayaninsa ya nuna irin son da ya kewa yarinyar, idan aka hana shi aurenta ba’a yi masa adalci ba.
Daga ‘karshe Alhaji Mansur ya bashi umarni akan ya je ya sanar da Yayansa wato Alhaji Hamza maganar.
__________________________________________________
*Ci gaba*
Sam ita Halima ba ta san halin da ake ciki ba, hankalinta kwance, ta mai da hankalinta kan karatunta.
A ranar Baffa ya sanar da Mama halin da ake ciki. Har zuciyarta ba ta yi farin ciki da wannan al’amarin ba, don dai kawai babu yadda za ta yi ne, musamman da harkar ya had’a da Aunty Saratu, ta san sai dai kawai ta toshe kunne.
Tun a ranar ta kira Murja ‘kanwarta, ta sanar da ita halin da ake ciki. Sosai su ke shiri duk da ance ba tare za’a yi d’aurin aure da biki ba.
Duk budirin da ake Aunty Saratu ba ta da labari, gashi har lokacin Yayanta bai ce mata komai akan maganar da su ka yi da shi ba, shima Baffa ta yi tunanin zai yi ma ta maganar amma shiru, gashi lokaci kullum ‘kara ‘kurewa ya ke.
Ita tsoronta ma kar idanunsa su ‘kyallo wata ya ‘ki kar6ar maganar Sadiya, gashi daga ita har Sadiyan sun saka rai sosai da maganar.????
Yau saura sati guda arba’in d’in Sumayya wanda ya yi dai-dai da saura sati d’aya d’aurin auren Halima da Hafiz, amma har lokacin ita kanta amaryar ba ta sani ba bare kuma Aunty Saratu.
A ranar ta shirya zuwa gidan Yaya Yahaya don ta san me ake ciki game da maganar da suka yi kwanaki, akan Sadiya da Hafiz d’in, don ta san halin da ake ciki.
Bayan sun gaisa da shi ta ce “Yaya dama akan maganar da mu kai da kai ne, tun tuni ina ta zuba ido sai na ji shiru, kuma shima malam har yanzu ban ji daga gareshi ba, shiyasa naga ya kamata na zo, na ji me ake ciki, tun da ga lokaci yana ta tafiya.”
Sai da ya nisa ya ce “me ki ke so na ce miki bayan ga yadda al’amarin ya juye? Dama can Allah bai yi ita matarsa ba ce, don haka ki cire wannan batun daga zuciyarki.”
Cikin mamaki ta ke kallonsa ta ce “ban gane me ka ke magana a kai ba, wani abu ne ya faru?”
“Kina nufin baki san halin da ake ciki ba akan maganar aurensa da ‘yar mijinki?”
“Wace ‘yar mijin nawa? Wai Halima? Mene ne yake faruwa Yaya? Don Allah sanar da ni, in san halin da ake ciki.”
“Kamar yadda na yi miki al’kawari washegari na je har gida don na sami Malam Hamisu da maganar, sai na tarar da shi da ba’ki, ba wasu ba ne ba’kin face iyayen Hafiz.
Tare muka shiga yajensu da shi, bayan mun gama gaisawa suka gabatar da dalilin zuwansu, ba komai ne ya kawo su ba, sai nemawa shi Hafizun auren Halima ‘yar abokiyar zamanki.
Ganin haka ya sa ban sanar masa da abinda ya kawo ni ba, sai na bar maganar na dawo gida. To na yi tunanin ko kin sami labarin shiyasa ban sanar da ke ba.”
“Cabd’ijan, babbar magana, au irin cin amanar da za’a yi min kenan? Ai basa fad’a ba, tunda sun san ba su ‘kulla abin arzi’ki ba.
Ita yanzu ko kunya ba ta ji ba, ta rasa wanda zata aura sai mijin ‘kanwarta gotai-gotai da ita, duk yadda Sumayya ta d’auke ta irin sakayyar da za ta yi mata kenan?”
Dakata Saratu, duk me ya kawo wannan maganar? Shifa aure nufin Allah ne, kuma matar mutum kabarinsa, sannan ni banga abin 6acin rai a cikin wannan batu ba, idan Allah ya yi ita ce matarsa da wanda ya isa ya hana ne?”
Ban fad’a miki wannan maganar don ki je ki tayar da fitina ba, kar ki kuskura na ji wani abu marar dad’i ya faru akan wannan maganar.”
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Share_*
*_Vote_*
[10/22, 8:31 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na goma sha hud’u*
Yadda kasan kububuwa haka ta shiga gidan, sai cika ta ke, ta na batsewa kamar ta fashe, ko sallama ba ta yi ba, duk da Mama da ke aikace-aikacenta a tsakar gida.
Zuwa wajen uku da rabi Halima ta dawo gidan a gajiye, saboda yau sun yi test har biyu a makaranta.
Tun da Aunty Saratu ta d’aga ido ta ganta, ta ji ‘kululun ba’kin ciki ya tokare zuciyarta, ji ta ke kamar ta bud’i ido ta ga ba ta numfashi.
Sai da ta yi wanka ta yi sallah, sannan ta yi zaman cin abinci, ta na ci suna hira da Mama don ranar ba ita za ta yi girkin dare ba, sai ta yi zamanta a d’aki, gudun fitinar Saratu, bare yadda ta shigo gidan ta san kad’an ta ke jira.
Baffa ya na dawowa gidan ko abinci ba ta bari ya ci ba ta tare shi da maganar “Malam wani labari na ji wai kana kana shirin aurawa Halima mijin Sumayya?”
Ba tare da ya dube ta ba ya ce “kina da matsala da hakan ne?”
Wannan tambayar ta ‘kara tunzura ta, ta ce “kwarai kuwa, in banda cin amana yaushe har Sumayyan ta rasu, da za’a yi tunanin *maye gurbinta* da yayarta don abin kunya?
Tun da na ke ban ta6a ganin inda ya ta auri mijin ‘kanwa ba, sai kai da kake shirin farawa, to wallahi tun wuri wannan maganar a bar ta……”
“In ba haka ba fa?” Ya katseta da tambaya.
Za’ayi tashin hankalin da ba’a ta6a yi ba a gidan nan. In dole ne sai an *Maye Gurbin* ai ga Sadiya nan, ita ya kamata a bashi tun da ita ce ‘kanwarta, amma don kwad’ayi da son abin duniya sai a d’auki yayarta a bashi, to wallahi ka ma sake shawara, don ba yarda zanyi da wannan maganar ba.”
“Sai dai kiga tashin hankalinki ke kad’ai, kuma wallahi ba zan lamunci yi min fitina a gida ba. Auren Halima da Hafizu kuma abu d’aya ne zai sa a fasa shi, idan su suka zo da kansu, suka ce sun fasa, kamar yadda suka zo suka nemi auren da kansu.
Sai dai ina son ki sani na gaji da fitinarki a gidan nan, wallahi wannan karon ba zan d’auka ba, idan ki ka nemi tayar min da hankali zan d’auki mummunan mataki a kanki, idan kuma kina ganin wasa na ke ki gwada ki gani.”
Ya na gama fad’ar haka ya juya ya fice, ya bar gidan gabad’aya, aikuwa ta fito ta dinga yada magana a tsakar gida, har Halima da ba ta san komai akan maganar ba ta san me ake ciki.
Hankali tashe ta ke tambayar Mama gaskiyar abinda ta ji, nan Mama ta tabbatar ma ta da gaskiyar maganar, ta ‘kara da cewa “tun farko abinda ya sa ban sanar da ke maganar ba, saboda Baffanku ya ce da kansa zai sanar da ke.
Abu d’aya da zan fad’a miki shine ki zama mai biyayya ga umarnin mahaifinki, ba talla ya yi da ke kamar yadda ki ka ji ta ce ba, iyayen yaron ne da kansu, suka ro’ki alfarmar a bashi aurenki, shi kuma bai yi shawara da ke ko neman za6inki ba, saboda ya na da tabbacin ya isa da ke, to ina so ki nunawa duniya da gaske ya isa da ke d’in.