HAUSA NOVELMAYE GURBI Complete Hausa Novel

MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Duk wannan abun da ta ke babu abinda zai sa, babu abinda zai hana, mu kuma mun san ba don abin duniya zamu bashi aurenki ba, kamar yadda ta ke fad’a.”

Fashewa ta yi da kuka, zuciyarta na raya mata, wannan wane irin aure ne mahaifinta ya ke shirin yi mata? Ta yaya za’a ce ta auri mijin Sumayya ‘kanwarta?

Amana ba ta ce haka, idan ta yi haka ba ta yiwa Sumayya halarci ba, duk ‘kaunar da ke tsakaninsu amma yanzu ace ita ce za ta auri mijinta?

Haka ta tashi ta koma d’akinta zuciyarta a cunkushe da tunanin neman mafita.

Dole ne ta sami Hafiz don shine kad’ai mutumin da zai iya da’kile wannan maganar.

Ranar ba ta kwana cikin dad’in rai ba, tunaninta d’aya, ya za’ai su had’u da Hafiz, don ita a ganinta wannan al’amarin ba mai yiyuwa ba ne, ai ana barin halak ko don kunya.

Ganin ba za ta sami had’uwa da shi ba, sai ta ha’kura ta bari, ranar addu’ar arba’in d’in Sumayyan za ta yi duk yadda za ta yi don su had’u da shi, wannan tunanin shine ya sa ta sami kwanciyar hankali, har Mama ta yi tunanin nasihar da ta ke mata kowane lokaci ne ta yi tasiri a zuciyarta.

Abinda ya basu mamaki a gidan shine ganin yadda ake ta shirye-shiryen addu’ar arba’in d’in Sumayya a gidan, alhali ga gidan mijinta.

Kasa ha’kuri Aunty Saratu ta yi sai da ta nemi sanin dalili, sai Baffa ya ba ta amsa da cewa “ni na bu’kaci a yi adda’ar a nan, kuma suka amince min.” Dole ta ja bakinta ta yi shiru.

Ana gobe arba’in su Aunty Saude a gidan suka yini, suna ta aiki, wanda hakan ya sa Aunty Saratu ta fara tsarguwa, don taga yanayin girkin kamar na ba na sadaka ba ne kawai.

 

 

*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Share_*
*_Vote_*
[10/23, 9:03 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*

*_UMMU AISHA_*

*Wattpad ummushatu*
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Shafi na goma sha biyar*

Ranar asabar ne ya kama kwana arba’in cif da rasuwar Sumayya. Tun safe ‘kofar gidan ya cika da mutane, zuwa d’an wani lokaci aka gudanar da addu’ar, bayan an kammala kuma aka gudanar da d’aurin auren *Hafiz Mansur da Amaryarsa Halima Hamisu*, bisa sadakin naira dubu d’ari la’kadan ba ajalan ba.

Zuwa ‘karfe goma na safe kowa ya kama gabansa, sai iya mata kawai a cikin gida.

Aunty Saratu kuwa zuciyarta kamar ta fashe don ba’kin cikin abinda ya faru, don tuni labari ya shigo musu.

‘Yan uwanta ne su ka dinga ‘ko’karin kwantar ma ta da hankali, akan kar ta yi abinda bai dace ba, ko ba komai ‘ya guda ta rasa ta yi ha’kuri bare wannan maganar, shi aure ai nufin Allah ne, kuma matar mutum kabarinsa.

Duk bayaninsu jinsu kawai ta ke, amma ta ‘kudura a zuciyarta, ba za ta zuba ido ayi mata abinda aka ga dama ba, dole ta d’auki mataki akai.

Zuwa bayan azahar kowacce ta koma gidanta sai iya mutanen gidan. Halima na kwance a d’aki kukan da ta yini yi da damuwar da ta saka a zuciyarta sun saukar mata da zazza6i.

Dole sai da Mama ta saka Yaya Usman ya kaita asibiti da magriba, don jikin ya yi zafi sosai.

Bayan magunguna da aka ba ta likitan ya bata shawarar ta daina saka damuwa a zuciyarta, don hakan zai iya zama illa ga lafiyarta.

Haka su ka dawo gida, zuciyarta cunkushe da tunanin ta yaya za ta iya zaman aure da mijin ‘kanwarta?

Tabbas idan ta ce har lokacin zuciyarta ba ta son Hafiz ta yi ‘karya, amma tun da d’ad’ewa ta cire shi daga lissafinta, sai kuma yanzu rana tsaka a d’aura mata aure da shi.

Sai da Mama ta yi fama da ita sosai kafin ta ci abinci ta sha magani. Nan ta zauna tare da Mama ta na ta kwantar ma ta da hankali da nasiha har Usman da Nura suka shigo, Suma nasihar su kai ta yi mata.

Shi kuwa angon na can cikin farin cikin samun cikar burinsa, duk da har lokacin bai fita daga alhinin mutuwar Sumayya ba, amma wannan bai hana shi kasancewa cikin farin ciki ba, da samun abinda zuciya da gangar jiki suka dad’e su na bu’kata.

Cikin satin sosai Halima ta yi ta fama da rashin lafiya, amma zuwa yanzu Alhamdulillah, jiki ya yi sau’ki sosai, sai dai ba ta koma makaranta ba har lokacin, don Baffa ya ce sai ta saurari zuwan mijinta, duk hukuncin da ya yanke ba shi da ja.

Ranar Juma’a da yamma misalin hud’u da rabi na yamma Halima na zaune, da hand out a hannunta, tana dubawa saboda jarabawa da ta ke gabatowa.

Nura ne ya shigo gidan da sallama, bayan ya yiwa Mama barka da gida ya juya ga Fatima da ke zaune ya ce “to amarya sai ki ajje wannan takardun ki tashi ga angonki nan ya zo ya na jiranki a d’aki na.”

Wani irin fad’uwar gaba ta tsinci kan ta a ciki sakamakon maganarsa, sai ta basar kamar ba ta san da ita ya ke ba, ta ci gaba da karatunta.

Ganin ba ta da niyyar tashi ya sa shi d’aure fuska ya ce “wai ba da ke na ke magana ba?”

Dole ba don ta so ba ta mi’ke, ta shiga d’akinta, hijabi kawai ta d’auka ta saka ta fito.

Har ta yi hanyar fita daga gidan Mama ta kira ta, tana zuwa ta ce “a haka ki ke nufin zaki fita? Wai dama Halima duk nasihar da na ke miki ashe ba ta shiga kunnenki?

Kafin rai na ya 6aci maza ki koma d’aki ki sauya shiga, kuma kar ki 6ata masa lokaci.”

Dole ba don ta so ba ta koma ta sauya kaya, doguwar rigar atampa ta sa, purple mai ratsin yellow, d’inkin ya kar6i jikinta sosai, sai ta lullu6e jikinta da yellown mayafi.

Sai da ta feshe jikinta da turare sannan ta fito gwanin sha’awa da ita, kamar ka sace ta ka gudu, duk da ko powder ba ta shafa ba a fuskarta bare a je ga batun kwalliya.

Sai da ta yi sallama ya amsa mata ta shiga d’akin. A zaune ta same shi kan kujera ‘kwaya d’aya da ke d’akin, ko ina tsaf a gyare, sai ‘kamshin air freshener ke tashi.

Sanye yake da shadda brown colour, d’inkin tazarce, anyi kwalliya da zare kalar coffee, sai ya sanya hula ma coffee colour, ba ‘karamin kyau ya yi ba.

‘Kamshin jikinsa ya had’e da ‘kamshin air freshener sai d’akin ya bada wani ‘kamshi na musamman.

 

 

*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Share_*
*_Vote_*
[10/27, 4:43 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*

*_UMMU AISHA_*

*Wattpad ummushatu*
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Shafi na goma sha shida*

Duk rashin walwalar da fuskarta ta nuna, hakan bai hana ta gaida shi ba, daga nan ta ja bakinta ta yi shiru.

Sun d’auki lokaci mai tsayi d’akin shiru kamar babu mutane a ciki, sai can ya nisa ya ce “nasan dole zaki kalli wannan al’amarin da wata fuska, amma idan ki kai tunani shi al’amari na Ubangiji babu yadda ba ya kasancewa.

Allah shi ya d’auke Sumayya ya musanya min da ke, ya kamata mu kar6i za6in Allah da hannu bibbiyu, mu kyautatawa junanmu……

Cakin zafin rai Halima ta katse shi da cewa “za6in Allah ko son zuciya? Daga rasuwarta ko kunya ba ka ji ba, ka zo ka nemi auren yayarta, duk irin soyayyar da Sumayya ta nuna maka irin sakamakon da za kayi mata kenan?

Tun wuri ya kamata ka san cewa ban shirya zama da kai ba, saboda tun farko ban tsara rayuwa da mutum irinka ba, don haka ka gaggauta d’aukar matakin da zai datse wannan ala’kar da aka ‘kulla a tsakaninmu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button