MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Cikin nuna rashin damuwa da maganarta ya ce “kina ganin datse ala’kar da ke tsakaninmu abu ne mai sau’ki?”
“Kwarai kuwa, ni banga wani abin wahala a ciki ba.”
Sai da ya yi murmushi sannan ya ce “gara da kika ce ba ki gani ba, don ni na gani, ki d’auka a ranki cewa wannan auren namu mutu ka raba ne.
Abinda na ke so ki fahimta ban aure ki don na rabu da ke ba. Maganar Sumayya kuma Allah ne shaida ban yi haka don cin amanarta ba. Allah ya riga ya ‘kaddara sai na aure ta kafin ke shiyasa a waccan ranar tsautsayi ya sa na rasa wayata, da ita kad’ai ce hanyar da zata zame min tsani wurin had’uwa da ke.
Lokaci mai tsaho na d’auka ina nemanki a can wata unguwa da ban, ashe ke ga a inda ki ke.
Wannan kad’ai ya ishi mai hankali ya fahimci ikon Allah. Na had’u da ke a inda tunanina bai ta6a kaiwa nan ba.
Yanzu da na same ki kema kin san ba zan yi miki ri’kon sakainar kashi ba. Insha Allah na yi al’kawari zan zama mutum mai kyautatawa a gare ki, zan yi iyakar ‘ko’karina wurin ganin kin sami farin ciki a zamantakewarmu.”
Ba ta da abin cewa, don ta san duk abinda za ta fad’a ba zai ta6a tasiri ba, don haka yin maganar ma bashi da amfani a gare ta.
Sai da ta ga yana shirin tafiya ta kawo ma sa maganar makarantarta da cewa “ina son zan koma zuwa makaranta don gab mu ke da fara exams, ana ta wuce ni abubuwa.”
“A wacce makarantar ki ke karatun ne?” Ya tambaye ta.
“A BUK ne.” Ta bashi amsa a gajarce.
“Ok babu damuwa, amma ki bari zan turo wanda zai dinga kai ki, don ba zai yiwu ki dinga hawa motar haya ba.”
“Akan wane dalili?” Ta tambaye shi, da alamun maganar ba ta yi ma ta dad’i ba.
Ya bata amsa da cewa “saboda haka na ga dama.”
Daga ‘karshe haka su kai sallama ya fito da niyyar tafiya, ita kuma ta koma cikin gida. Bayan komwarta ne yaro ya shigo gidan d’auke da ledoji guda biyu sha’ke da kaya.
A kan idon Aunty Saratu yaron ya shigo, ai kuwa take zuciyarta ta cika da ba’kin ciki, har ta kasa 6oyewa.
Nan ta fara cewa “ai dama abinda ake so kenan, Allah dai ya raba mu da mmtum mai cin amana, yanzu duniya babu gaskiya, duk yadda ka kai da mutum, baya iya ri’ke maka Amana, in ba haka, Yaya ta auri mijin ‘kanwarta, kamar dama kad’an ake jira.”
Haka ta yi ta maganganunta babu wanda ya tanka mata, bare ta sami abokin yi.
Kamar yadda ya ce kuwa haka ya turo driver kullum ya kai ta makaranta, kafin ya tafi zata sanar da shi lokacin da za ta gama lactures ya zo ya mai da ita gida.
Akan wannan ma Aunty Saratu ta yi surutu sosai, daga ‘karshe dole ta gaji ta ha’kura, tun da babu mai kulata.
Sai da akai kimanin wata d’aya da d’aura auren Baffa ya saka ranar bikin Halima sati shida masu zuwa.
Tun daga lokacin Aunty Murja ta soma ‘ko’karin ganin ta gyara amarya kamar yadda ya kamata, kusan ko da yaushe ta na tafe a kan hanya.
Itama Mama ba ta zauna ba, bayan shirye² da take na sayayyar kayan kitchen, sai kuma koya mata dabarun zaman aure, da hanyoyin da za ta bi ta kafu a zuciyar mijinta babu boka babu Malam.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/1, 8:40 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na goma sha bakwai*
Shiri sosai ake akan bikin daga kowane 6angare, amma ban da amarya da ta takura kanta, kullum gani ta ke kamar ta ci amanar ‘yar uwarta ne, wannan dalilin ya hana ta sakewa.
Saura sati d’aya biki aka kawo lefe, lefen da ya amsa sunansa, masha Allah kowa ya ke fad’a, don ba ‘kananan kud’i aka kashe gurin had’a lefen ba.
Aunty Saratu don ba’kin ciki sai da ta yi kuka a d’aki, don wannan ko kusa ba za’a had’a shi da lefen Sumayya ba wanda ta yi ta yiwa mutane kuri da fele’ke a kai, sai ga na Halima ya fi wancan komai.
Ana ya gobe za’a fara biki Karimah da ‘ya’yanta su ka dira a gidan, aikuwa Aunty Saratu ta dinga fad’a kamar za ta ari baki, don yadda ta ke ba’kin ciki da auren so ta ke duk wanda ya ra6e ta ma kar ya yi farin ciki da batun.
Ta na fara yiwa Karimah fad’an zuwanta ta ce “haba Aunty, idan ban zo bikin Halima ba bikin wa ki ke so na je? Har yanzu kin kasa fahimtar matsayin Halima a gurinmu.
Ko kin san cewa tun asali Hafiz saurayin Halima ne ba Sumayya ba? ‘Kaddara ce ta raba su, shi kuma bai san gidan nan ba, lokacin da suka had’u da Sumayya Halima gujewa had’uwarsu da shi ta dinga yi, saboda kar had’uwarsu ya rusa maganar auren shi da Sumayya.
Bai tashi had’uwa da Halima ba sai bayan ya auri Sumayya, wanda daga ‘karshe damuwa da tunanin babu yadda za’a yi ya sami Halima ya na tare da Sumayya ya sa shi kamuwa da hawan jini.
Amma duk da haka bai ta6a wula’kanta Sumayya ba. Ita kuma Halima da Sumayyan ta tare ta da maganar ‘kin sauraronta ma tayi.
A yanzu Sumayya ta bar duniya, don sun yi aure sai ya zama laifi? Don Allah ki daina irin wannan abubuwa wallahi bai dace ba, ba na jin dad’in haka.”
Duk bayanin da Karimah ta ke jin ta kawai ta ke, amma zuciyarta cike ta ke da takaicin yadda ta zauna ta na wanke laifin Halima a idonta, har zuciyarta ji ta ke da tana da yadda za ta yi da ko magana ta fatar baki ba za ta bari Karimah ta yi da Halima ba.
Sai da Karimah ta dage sosai akan Halima kafin ta yarda ayi mata flower, da gyaran gashi, don da farko kafewa ta yi akan ba za ta yi komai ba.
Ranar Juma’a da yamma akai walima, wadda ta ‘kayatar sosai, an wa’azantar da al’umma, daga ‘karshe aka ci aka sha, sannan kowa ya koma gida da kyaututtukan da aka tanada don ba’kin da suka sami damar halartar taron.
Washegari akai yini, da yamma kuma aka kai amarya gidan mijinta. Sai dai fatan Allah ya ba su zaman lafiya mai d’orewa.
Tun da mutane su ka watse ta tashi ta kulle ‘kofar d’akinta da mukulli ta bar key d’in a jiki, don ba ta san da idon da za ta dube shi ba a matsayin mijinta.
Wajen ‘karfe tara na dare ya shigo gidan hannayensa d’auke da manyan ledoji guda biyu.
Sai da ya shiga d’akinsa ya yi wanka ya shirya sannan ya fito ya nufi d’akinta, sai dai duk yadda ya kai ga ‘kwan’kwasa ‘kofar biris ta yi da shi ta ‘ki bud’e masa ‘kofar, daga ‘karshe haka ya ha’kura ya koma d’akinsa.
Washegari tun da ta tashi da asuba ta yi sallah ba ta koma ba, sai ta kunna karatun Qur’ani a wayarta ta na bi, har zuwa lokacin da gari ya yi haske, sannan ta kashe.
Toilet ta shiga ta wanke, sannan ta dawo ta gyara d’akin, sai da ta tabbatar ya yi yadda ta ke bu’kata sannan ta fita ta fara tsaftace parlour.
Har ta gama aikinta ba ta ji motsin kowa ba, alamar maigidan ya na kwance kenan.
Har kitchen sai da ta goge duk da babu datti ko kad’an, sannan ta koma d’aki ta yi shirin shiga wanka.
Bayan ta fito, ta shafa mai sannan ta saka kaya, bata yiwa fuskarta wata kwalliya ba, daga powder sai lip gloss kawai ta yi amfani da su, sai turare da ta yi amfani da shi.
Wajen tara da rabi ta ji ana ‘kwan’kwasa ‘kofa daga parlour, sai ta mi’ke ta fita dai-dai lokacin da shima Hafiz ya fito daga nasa d’akinsa sanye da jallabiya, yanayinsa ya nuna daga barci ya tashi a lokacin.