HAUSA NOVELMAYE GURBI Complete Hausa Novel

MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Tsayawa ta yi daga baya, shi ya bud’e ‘kofar. Iya Talatu ce tsohuwar da ke taya Umma da aikace-aikacen gida, hannunta d’auke da kwandon kayan abinci.

Daga ba’kin ‘kofa ya kar6a bayan sun gaisa, sai ta juya, don dama driver ne ya kawo ta, sai dai ta bar masa sallahun ya gaida matar gidan.

 

 

*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/2, 4:48 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*

*_UMMU AISHA_*

*Wattpad ummushatu*

*Sadaukarwa*

*_Na sadaukar da wannan page ga d’an uwana Hafizu, Allah ya ba ka lafiya ya sa kaffara ne, Allah ya sa ka sake takawa da ‘kafafunka. Amin_*
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Shafi na goma sha takwas*

Yana juyowa suka had’a ido da shi, sai ta ji ta d’an daburce, cikin ‘karfin hali ta daure ta ce “ina kwana?”

Bayan ya amsa ya mi’ka mata kwandon dake hannunsa tare da cewa “ga break fast nan inji Umma.”

Ba tare da ta kalle shi ba ta kar6a ta ce “mun gode.” Sai ta nufi dining area ta ajje abincin akan table ta juya ta koma kitchen, ta d’auko cups da plates ta ajje ta juya ta koma d’aki.

Bayan ya koma d’aki wanka ya shiga, sai da ya shirya tsab cikin wani yadi milk colour, ya fito parlour yana ta baza ‘kamshin turare.

Ganin bai ganta ba ya sa ya nufi d’akinta, sai ya same ta zaune akan dressing mirror tana danne-danne a wayarta, tana sanye da riga da skirt na wani material kalar pink, d’inkin ya yi dai-dai da jikinta gwanin sha’awa.

Ganin yadda ta d’aure fuska tun shigowarsa ya sa shima cikin basarwa ya ce “ki tashi mu je mu yi break fast.”

Ta d’aga kai ta na kallonsa a kai-kaice ta ce “ka ci abincinka ni na ‘koshi.”

Murmushi ya yi marar sauti sannan ya ce “me kika ci da za ki ce kin ‘koshi? Duk abinda zaki yi zan barki ki gaji ki gama, amma ban da zama da yunwa, don in wani abu ya same ki ba zan iya yafewa kaina ba, don haka ki tashi, in kin ‘ki kuma wallahi d’ure zan miki.”

Ganin yanayin fuskarsa babu alamar wasa ya sa ta mi’ke, sai da ta d’auki hijabi ta saka, yana kallonta bai yi magana ba, sannan ta fice daga d’akin tana ‘kun’kuni.

Kunun gyad’a ne sai masa da miyar alaiyyahu wadda ta ji nama sosai. Plate ta janyo ta fara zaba ma sa, da gan-gan ta cika plate d’in don ganin gudun ruwansa.

Tana sa hannu don d’aukar wani plate d’in ya dakatar da ita da cewa “ni da wa za mu ci wannan abincin?”

Cikin ko in kula ta ce “naka ne kai kad’ai.”

Plate d’in da ta ke ‘ko’karin zuba na ta abincin ya kar6e ya ce “sai ki zo mu ci wannan tare tun da ni d’in ai ba jaki ba ne, da zan iya cinye wannan abincin ni kad’ai.”

Duk da zuciyarta ba ta so ba, tare ta zauna su ka ci abincin da shi, son tun da ya yi ma ta maganar d’ura ta ji tsoron yi masa gardama.

Bayan sun gama ta kwashe kayan ta mayar kitchen ta gyara gurin, sannan ta koma kitchen d’in ta wanke plate da cups d’in da su kai amfani da su.

Da ta fito daga kitchen d’in ba ta koma d’aki ba, sai ta zauna a parlour ta kunna TV tana kallo.

Ba ta dad’e da zama ba ya fito daga d’akinsa, hannunsa ri’ke da agogo ya na d’aurawa a d’aya hannun, ya ce “zan fita, amma bana tunanin zan dad’e, amma akwai sa’ko da za’a kawo, sai ki ajje komai a inda ya dace.”

“To” kawai ta ce, ta ci gaba da kallonta, sai da ta ga ya juya zai fita sannan ta ce “a dawo lafiya Allah ya tsare.”

Ya amsa da “amin” ya fice daga gidan.

Tun bayan tashin motarsa gidan ya yi tsit, sai ta ji babu dad’i, har zuwa wani kokaci, ta ji an nocking d’in ‘kofa.

Da ta bud’e wani sauraya ta gani, yana kama da Hafiz sosai, sai dai hasken fata da Hafiz d’in ya fi shi. Da fara’a a fuskarta ta tare shi ta ce ya shigo, amma sai ya ce ya na zuwa.

Komawa ya yi cikin motar ya dinga shigo da kaya, kama daga ruwa, lemuka da sauransu.

Sai bayan ya gama ya zauna su ka gaisa da shi, bai dad’e ba ya tafi, ita kuma sai ta je ta kwashe kayan ta ajje su a inda ya kamata.

Ba’a dad’e sosai ba ba’ki su ka dinga zuwa, musamman ‘yan uwan Hafiz d’in ma su zuwa ganin amarya.

Har akai sallar la’asar bai dawo gidan ba, har aka kawo musu abincin rana daga gidan Umma, gudun kar ya yi ma ta abinda ya yi da safe sai ta ci abincinta a lokacin ta ajje ma sa nasa.

Ba shi ya dawo gidan ba sai bayan la’asar, tun safen ya na kasuwa, saboda wasu kaya na sa da ya yi order su ka iso a ranar dole ta sa shi zuwa.

Kai tsaye d’akinsa ya shiga, duk da bai ga matar gidan ba, sai da ya yi wanka, ya shirya sannan ya fito don cin abinci.

A parlour su ka had’u, ita kuma ta fito d’aukar ruwa, sai ta yi masa sannu da zuwa. Tana ‘ko’karin wucewa d’aki ta ji maganarsa ya na ce ma ta ta zo ta bashi abinci.

Sai ta koma dining area d’in ta yi serving d’insa sannan ta tafi d’aki.

 

 

*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/4, 6:58 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*

*_UMMU AISHA_*

*Wattpad ummushatu*
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*_Not edited_*

*Shafi na goma sha tara*

Kimanin sati biyu kenan da bikin su, amma har lokacin ba ta da lokacin sauraronsa, don sau da yawa ma idan ta na zaune a parlour ya zo ya zauna, to ita kuma za ta tashi ta bashi guri.

Shi kuma ya zuba ma ta ido don ganin iyakar gudun ruwanta, bai ta6a nuna ma ta damuwarsa akan hakan ba.

A haka har ta koma makaranta, kullum shi zai Kai ta, idan ta gama lactures kuma driver zai je ya d’akko ta.

Ranar da ta cika wata d’aya a gidan ya ce ta shirya zai Kai ta gidansu ta gaida mahaifansa, bavta yi gardama ba, sai ma shiri na musamman da ta yi, don a cikin nasihar da Mama ta yi ma ta, ta ce ta kyautatawa iyayensa sosai domin wannan ma zai ‘kara saya ma ta daraja da kima a idonsa.

Dambun naman kaji ta yi mai yawa ta juye cikin poil paper, sai ta d’aukarwa Umma turning atampha a irin kayan lefenta, shi kuma Abba ta aika aka sayo masa turaruka da agogo.

Bai san da ahirinta ba, don haka lokacin da suka tafi sai da ya tsaya a wani store, su ka yi sayayya kafin su ‘karasa gidan.

Ta sami kyakkyawar kar6a daga Umma. Har ‘kasa ta dur’kusa ta gaida ita, cikin girmamawa, bayan sun gaisa sai ta zauna a nan ‘kasan inda ta ke, Umma ta ce ta koma kan kujera ta zauna amma fir ta ‘ki, wannan sai ya ‘kara ma ta ‘kima a idon Umman.

A nan gidan ya tafi ya barta ta yini, suk wani aiki da ta ga Umma za ta yi ba ta bari, za tayi sauri ta kar6a ta yi, har ita kanta Umman ta fara hana ta, ta ce ya kamata itama ta huta.

Har girkin dare ita ce ta yi, bayan ta gama ta wanke kwanuka da tukunyar da ta yi amfani da su, sannan ta yi alwalar sallar magriba.

Sosai Umma ta yaba da hankalinta, musamman da ta ga wata tsarabar da ban da ta kawo musu, bayan wadda aka shigo da ita lokacin zuwansu da Hafiz.

Sai bayan sallar isha’i, ya zo su ka tafi, kafin su bar gidan Umma ta ke sanar da shi abinda ta kawo musu, shi kansa ya yi mamaki, son bai yi tsammanin hakan daga gareta ba, ganin yadda Sam ba ta damu da duk wani al’amari nasa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button