MAYE GURBI Complete Hausa Novel

A hanya ya ke yi Mata godiya, amma sai ta ce “ka daina yi min godiya ba don Kai na yi ba.”
Murmushi kawai ya yi, har suka je gida babu wanda ya sake magana da wani, shi ya San ko ya yi bai zama lallai ta amsa masa ba, don haka ya ja bakinsa ya yi shiru.
Tun da shige d’aki ba ta sake ko da le’kawa waje ba, bayan ta yi wanka da shafa’i fa wuturi sai ta yi kwanciyar ta, shi kuma ya na ta jiranta a parlour, ganin shirunvya yi yawa ya sa ya shiga d’akin.
Ga mamakinsa a kwance ya same ta, sai ya sami kan bed site drower ya zauna, cikin taushin murya ya ce “magana nake son mu yi da ke idan ba za ki damu ba.”
Tashi tayi zaune daga kwanciyar da ta ke, duk da ba yi magana ba amma ta tattara duk nutsuwarta a kansa, alamar dai ta na sauraronsa.
Sai da ya yi gyaran murya sannan ya ce “a matsayinki na mace mai ilmi bai kamata ki dinga yin abubuwan da ki ke min ba, haba Halima, ina tunaninki ya tafi? Wallahi ban zaci haka daga gareki ba.
Kina tunanin wannan zaman da muke zai sa jama’a su fasa fad’ar abinda su ka ga dama a game da mu? Idan wannan ne tunaninki gara ki sake tunani, shi mutum ba’a iya masa, kuma dama duk abinda za ka yi ba zaka birge wasu ba.
Allah ya sani ba muyi aure don cin amanar Sumayya ba, kuma na tabbatar da ana mutuwa a dawo Sumayya ba za ta yi ba’kin ciki da kasancewarta tare ba, sabida yadda ta ke sonki.
Ki yi tunani, ki duba abinda ya kamata, bai gudun zargi ln mutane ba, wani duk abinda za ki yi ba zaki birge shi ba.”
Tabbas maganganunsa sun yi tasiri a zaciyarta, amma har lokacin gani take kamar ba ta yiwa Sumayya adalci ba, ta rasa wanda za ta aura sai mijinta.
Kasa magana tayi Wanda hakan ya sa ya fahimci akwai alamun nasara, sai ya dage ya ci gaba da saw Mata misalai da maganganun da ya San za su ‘kara kwantar ma ta da hankali, daga ‘karsha ya yi Mata sai da safe ya tafi d’akinsa.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/8, 8:14 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com.
*Shafi na ashirin*
Tun daga wannan lokacin aka samu sauyi daga gare ta, don yanzu in ya same ta a palour ta daina tashi ta bashi wuri kamar da, kuma ko yana parlour’n a zaune zata fito ta zauna, wani lokacin har hira su ke a tsakaninsu.
Da wannan damar ya ke amfani, ko wane lokaci yana ‘ko’karin ganin ya cusa mata soyayyarsa a zuciyarta, kuma Alhamdulillahi ha’karsa ta cimma ruwa, domin zuwa yanzu duk wani motsi da za ta yi yana ma’kale a cikin zuciyarta.
Sannan duk wani abu da ta san na kyautatawa ne tana ‘ko’karin ganin ta yi masa.
__________________________________________________
Tun bayan dawowarsa daga masallaci ya na zaune a parlour, har zuwa lokacin da Halima ta gama komai da tasan za ta yi ta fito ta zauna, jifa-jifa suna hira, suna kallon wani series film da Haliman ke matu’kar so, har zuwa lokacin da aka gama.
Lokacin network news na yi ya kamo yana kallo, zuwa lokacin Halima ta gaji da zaman parlour ta tashi, ta yi masa sai da safe sannan ta shige d’aki.
Kai tsaye toilet ta shige ta yi alwala, ta fito ta yi shafa’i da wuturi, sannan ta yi shirin kwanciya barci, ta kwanta bayan ta yi addu’o’in da Manzon Allah (S.A.W) ya koya lokacin kwanciyar barci.
Shi kuwa Hafiz bayan ya gama kallon labaran d’akinsa ya koma ya yi wanka da alwala, ya na fitowa ya shafe jikinsa da mai, sannan ya sa saka kayan barci ya feshe jikinsa da turaruka.
‘Dakin Halima ya nufa a lokacin, ya same ta a kwance har lokacin ba ta yi barci ba, amma ta kashe wutar d’akin, alamar dai ta gama komai barcin ta ke jira ya d’auke ta.
A gefen gadon ya zauna, cikin lallausar murya ya ce “tashi ki yo alwala ki zo muyi sallah.”
Sai ta bashi amsa da cewa “ina da alwala.”
Umartar ta ya yi da ta tashi su yi sallah, babu musu ta mi’ke, sai ta d’aura zani akan kayan barcinta ta sanya dogon hijabi akai.
Sallah ya ja su raka’a biyu, bayan sun idar ya yi musu addu’o’i, sannan ya yi mata tambayoyi akan abinda ya shafi tsarki.
Yadda ya yi tunani haka ya samu, don yana kyautata mata zato game da ilmin addini, kuma cikin hukuncin ubangiji ba ta bashi kunya ba.
Tashi yayi ya fita daga d’akin, kafin ya dawo har ta koma kan gadon ta kwanta ta lullu6a da bargo.
Hannunsa d’auke cup ya shigo, ganin ta kwanta sai ya ce ta tashi, fresh milk ce a ciki, ya ba ta ya ce ta shanye, ba ta yin musu ba tar6a ta sha, sannan ta koma ta kwanta, sai ya ajje cup d’in a kan mudubi ya dawo, ya hau gadon ya kwanta ya janyo bargon da ta ke ciki shima ya shiga.
Tuni jikin Halima ya fara rawa, don maganar gaskiya ta na tsoron abinda zai faru, sannan ga kunya a tsakaninsu kasancewarsa mijin ‘kanwarta.
A hankali ya kai hannunsa jikinta, tuni rawar da jikinta ta ke ta ‘karu, sai ya mirgina kusa da ita sosai ya sanya ta cikin jikinsa.
Cikin dabara ya had’e bakinsu Yana mata wani salo mai mai rikitarwa
Babu inda hannunsa ba ya kaiwa a jikinta, abinda ya haifar mata da wani yanayi mai wuyar fassarawa.
Cikin hikima ya raba ta da duk kayan da ke jikinta ba tare da ta ankara ba, tuni Halima ta manta duniyar da ta ke ciki.
Shi kuwa da wannan damar ya yi amfani ya ci gaba da sake zautar da ita da salonsa mai rikita ta.
Hankalinta bai daeo jikinta ba sai da ta ji yana karanta addu’ar saduwa da iyali, a lokacin ne ta yi yin’kurin dakatar da amshi daga abinda ya ke ‘ko’kari aikatawa, amma ina ta makara.
Ni kaina ganin haka ya sa na kama gabana, don wannan rahoton ya fi ‘karfin d’aukata, na ga gara na basu guri, don ko ba komai sirrinsu ne.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/11, 5:32 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na ashirin da d’aya*
Tun a daren ya taimaka ma ta da ruwan zafi ta gasa jikinta, daga ‘karshe kuma ta yi wankan tsarki, bayan ta fito shima ya yi, sannan su ka koma su ka kwanta.
Da asuba har ya je masallaci ya dawo ba ta tashi ba, saboda wani irin zazza6i da ya rufe ta, tun cikin dare.
Tashinta ya yi daga barci, ta shiga toilet ta d’auro alwala ta fito, sai ta tarar baya d’akin, amma ya shimfid’a mata dadduma, ya ajje mata hijabinta a kai.
Bayan tayi sallah ba ta dad’e a zaune a gurin ba ta tashi, ta koma kan gado ta kwanta, don har lokacin jin kanta ta ke kamar zai tsage saboda ciwo.
Shi kuwa yana kitchen yana ‘ko’karin sama mata abinda za ta ci, ta sha magani.
Tea ya had’a mata sai ya dafa indomie ya soya ‘kwai ya d’ora akai, bayan ya juye indomie d’in a plate.
‘Dakin ya koma hannansa d’auke da d’an ‘karamin try wanda ya d’ora abincin akai.
Sai da ya ajje ya tashe ta, ta shiga toilet ta yi brush, sannan ya fara ba ta abincin.