MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Iya ruwan tea kawai ta iya sha ta ce ya isheta, sai ya bata paracitamol tasha saboda zazza6in da ke jikinta, ya bari sai anjima ya sayo mata magani.
Tun da ta koma ta kwanta ba ita ta tashi ba sai 9:30. Band’aki ta soma shiga ta yi wanka, sai ta dawo d’akin ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa.
Har zuwa lokacin bata jin dad’in jikinta, amma dai yanzu babu zazza6in a jikinta.
‘Dakin ta fara gyarawa sannan ta fito parlour ta gyara, sannan ta zauna tana ‘ko’karin yin break fast, sai ga shi ya dawo, hannunsa ri’ke da ledar magunguna.
Sai da suka gama break fast ya bata magungunan tasha, ta tashi tana ‘ko’karin tattare kwanukan ya hana ta. Shi ya kwashe komai da kansa, ita kuma ta koma d’aki ta kwanta.
Tun daga wannan lokacin komai a tsakaninsu ya sauya. Wani irin zama suke mai burgewa, kowanne a cikinsu burinsa ya yi abinda ya san zai faranta ran d’an uwansa.
Cikin abinda bai fi sati biyu ba jikinta ya sake murjewa ta yi wani irin kyau, kamar mai yaron ciki.
Shi kansa Hafiz sau da yawa zama ya ke kawai ya na kallonta.
Ranar asabar tun safe ta tashi da zumud’i, don tun a daren jiya Hafiz ya yi mata al’kawarin zai kai ta gidansu ta yini a can, wannan al’amari ya yi mata dad’i, shiyasa ta ke ta zumud’i, don rabonta da gidansu tun ranar da aka kawo ta gidan Hafiz a matsayin matarsa.
Tun kafin takwas na safe ta gama komai da ya kamata ta yi, ta shiga wanka.
Bayan ta fito sai da ta shirya tsaf cikin wani arnen less, d’inkin riga da skirt, mayafi da jaka da takalmin da ta yi amfani da su duk sun dace da less d’in, ta sha gold wuya da hannu.
Shi kansa Hafiz da ya gan ta kasa daina kallonta ya yi, don ba ‘karamin kyau ta yi ba.
Suna gama karyawa ta kwashe kwanukan zuwa kitchen, sai da ta tsaya ta wanke komai sannan ta fito.
Ko zama ba ta yi ba, ta d’auki mayafi da jakarta da ke ajje kan kujera a parlour’n su ka fice.
Tun da suka tafi zuciyarta ke cike da farin ciki, amma sai ta danne, don da ta nuna Hafiz zai ce murna ta ke za ta barshi shi kad’ai.
Suna tafe ya juyo da fuskarsa ya kalle ta, sai ya ri’ko tafin hannunta ya na murzawa a hankali, cikin taushin murya ya ce “ji nake kamar ki fasa zuwa unguwar nan, kawai mu koma gida nai ta kallonki.
Kwalliyar nan taki ta birge ni matu’ka, ha’ki’ka ina cikin mutane masu sa’a da Allah ya bani ikon mallakarki a matsayin matata, fatana mu kasance cikin kyakkyawar rayuwa har zuwa ‘karshen rayuwarmu.
Duk wani abu da d’a namiji ya ke bu’kata a gurin matarsa Halima kin had’a shi, tun daga tsafta, iya girki, ladabi da biyayya, kyautatawa, ga kuma uwa uba iyayena da ki ka d’auka tamkar naki.
Babban burina ki kasance a yadda ki ke yanzu, ni kuma na yi al’kawarin zan zame miki tamkar bawa, sai yadda ki kai dani.”
Har su ka zo ‘kofar gidan maganar da su ke kenan. Yana yin parking ko gama dai-daita motar bai yi ba, ta fito da sauri ta shiga cikin gidan.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share-*
[11/13, 3:28 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na ashirin da biyu*
Ta na yin sallama a tsakar gidan Aunty Saratu da ke sunkuye ta na shara ta d’ago ta na shirin amsawa, ganin mai yin sallamar ya sa ta yin shiru, musamman yadda ta ga Haliman ta sake canzawa ya sa ta saki baki tana kallonta, ta kasa amsa sallamar.
Duk wani yanayi da ke nuna Haliman na jin dad’i ta gan shi a tare da ita, ban da sutturar da ke jikinta da duk wanda ya kalla ya san mai tsada ce sosai.
Ita kanta Haliman da gan-gan ta yi wannan shigar don ta tsokale idon ma’kiyanta, kuma Alhamdulillah, ha’karta ta cimma ruwa, domin Aunty Saratu ta ji babu dad’a har cikin zuciyarta.
Ganin bata da niyyar amsawa ya sa tayi gaba, za ta shiga d’akin mahaifiyarta. Kamar ance ta d’aga kai sai ta ga Sadiya na le’kenta ta window d’in d’akin Aunty Saratu.
Da murna ta shiga d’akin, bakinta d’auke da sallama. Mama da ke fitowa daga uwar d’aki ta amsa sallar fuskarta d’auke da fara’a saboda ganin ‘yarta ta.
Cikin farin ciki suka gaisa, sai Maman ta tambaye ta Hafiz, sai lokacin ta tuna cewa tare suke ta barshi a ‘kofar gida.
Ai kuwa tana fad’awa Mama ta hau ta da fad’a “wannan ai rashin hankali ne, taya ya zaku zo da mutum ki bar shi tsaye a ‘kofar gida? Maza wuce ki shigo da shi.”
Jingine ta same shi a jikin motarsa, ya nad’e hannayensa a ‘kirji, ya na ganinta ya sakar mata lallausan murmushi, itama martani ta mayar masa, sannan ta ce “Mama ta ce ka shigo ciki.”
Bayanta ya biyo har zuwa soron gidan, ta na ‘ko’karin wucewa ciki ta ji ya ri’ko hannunta ya janyo ta baya ya ce “ni nasan da Mama ba ta ce ki shigo da ni ba, da tuni kin manta da ni, saboda ni d’in ba d’an gatanki ba ne.” Ya ‘karashe maganar ya na kashe mata ido d’aya.
‘Dan turo baki ta yi gaba, kamar irin shagwa6a6un yaran nan ta ce “ya akai ka dan da haka? Ina d’okin Mama ne, ka san na dad’e ban ganta ba shiyasa.”
Tare su ka shiga, ta na gaba ya na bin ta a baya, har zuwa parlourn Mama.
Cikin mutuntawa da girmamawa su ka gaisa da Mama, ya d’auki kimanin mintuna biyar zaune a parlour’n suna magana jefi-jefi da Mama, don yana son matar a ransa, tamkar mahaifiyarsa ya ke jinta. Ya mi’ke ya fito, sai Mama ta sa Halima ta je ta yi masa jagora zuwa parlour’n Aunty Saratu don su gaisa.
Zaune ta same su ita da Sadiya sun yi jigun-jigun kamar ma su zaman makoki, ya na daga ‘kofar d’akin a tsaye ta sanar da ita cewa zai shigo su gaisa.
Dole ta d’akko hijabi ta saka. Ta na zama yana shigowa d’akin, har ‘kasa itama ya tsugunna ya gaida ita, sannan ya mi’ke ya fice.
Halima na biye da shi har zuwa soron gidan, janyo ta ya yi jikinsa ya rungume ta, cikin wata murya kamar mai yin rad’a ya ce “yau zan yi kewarki hubby, tun yanzu har na fara jin babu dad’i, kamar ki zo mu koma gida.”
Cikin taushin murya ta ce “idan kana ganin da matsala in d’akko jakata mu koma, ai ko yanzu mun gaisa.”
Wani farin ciki ne ya ‘kara kama shi, fuskarsa da murmushi ya ce “a’a ki zauna, ai nasan Mama ma tana bu’katar ganinki, insha Allah da daddare zan zo mu tafi.
Ita kanta ta san ta fad’a ne kawai, amma ba wai har cikin zuciyarta ba, haka su kai sallama ta koma cikin gida shi kuma ya fita gurin matarsa.
Yara ne suka yi sallama a gidan suka fara shigo da kaya, bayan Mama ta tambayesu ta tabbatar kayan daga Hafiz ne sai ta sa suka ajje a ‘kofar d’akinta, bayan sun gama ta basu kud’i su raba, yara suka fita suna ta murna.
Da gadara Aunty Saratu ta fito, ta fara kwashe kayan za ta kai d’akinta, Halima da ta fito daga d’aki, tana son shiga band’aki ta ce ‘A’a Aunty ina za’a kai wannan kayan kuma?”
Cike da gadara ta ce “d’akina, ko za ki hana ne?”
Cikin fusata Halima ta ce ‘kwarai kuwa, don ba ke aka kawowa ba, kuma wallahi ko tsinke ba za ki d’auka a cikin kayan nan ba.” Tana gama fad’a ta sa hannu ta kar6e kayan.
Dai dai lokacin Mama ta fito daga d’aki saboda hayaniya da ta ji daga tsakar gidan, sai ta tarar da abinda ya ke faruwa.