MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Umarni Mama ta bata da ta bar mata kayan ta yi duk abinda ta ga dama da su, Halima ta ce “wallahi Mama ko tsinke ba zan bar matar nan ta d’auka ba, don ta ga komai tayi ana rabuwa da ita ya sa take zaton tsoronta ake, ita in ta san kunya har ta kalli wani abu da aka kawo gidan nan da sunana?
Ta manta lokacin da za’a shigo mata da kaya, amma ko Baffa ba zata nunawa ba, haka za ta hana kowa kayan ta yi yadda ta so da su, to wannan ba ikonta bane bare ta yiwa mutane gadara akai .”
Cikin masifa Aunty Saratu ta ce “ai duk abinda aka kawo gidan nan ta dalilin Hafiz ikona ne, domin ba don Sumayya ba da ba’ki san shi ba bare har ayi aure cin amana.”
Halima na ‘ko’karin sake magana Mama ta yi mata wani kallo, dole ta had’iye abarta ta fasa.
Shigowar Yaya Nura cikin gidan ya sa Aunty Saratu saurin shigewa d’akinta, don ta san yanzu ranta zai 6aci, don ta san shi, duk abinda za ta yi ba zai tanka ba, amma in ta ta6a masa uwa sai ranta ya 6aci, don kwanaki ba don Mama ta shiga tsakaninsu ba so ya yi ya zane ta, saboda shigowa da ya yi, ya samu ta na yiwa Maman tijara, tun daga lokacin ta shiga hankalinta da shi.
Wannan shi ya bawa Halima damar kwashe kayan gaba d’aya ta shigar cikin d’aki.
*_Follow Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*”Share_*
[11/14, 6:32 AM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na ashirin da uku*
Tun da suka shiga d’aki Mama ta ke yiwa halima nasiha akan muhimmancin ha’kuri da kuma ribar da me yinsa ya ke samu a rayuwa.
Daga baya suka shiga hirar da ta shafe su. Sai da yamma ta yi sannan Baffa ya dawo gidan, ya yi murna sosai da ganin Halima, musamman yadda ya ga ta kwantar da hankalinta.
Sun dad’e da shi ya na ta yi ma ta nasiha, lokacin da ta mi’ke don barin d’akin sai ga Aunty Saratu ta shigo ko sallama babu.
Ko zama ba ta yi ba tace “na zo ne ina son kayi min iyaka da Halima da uwarta a gidan nan, tun kafin rayuka su 6aci.”
Ba zan d’auki rashin mutunci ba, don ta ga ta yi aure shine za ta nemi zagi na akan gaskiya ta.
Har Halima ta kai ba’kin ‘kofar d’akin Baffa ya kira ta ya ce ta dawo, babu musu ta dawo ta samu guri ta zauna.
Ya ce “me ya had’a ki da ita da har kika zage ta?”
Cikin ladabi ta ce Baffa ban zage ta ba, nan ta zayyana ma sa duk yadda su ka yi da ita, tun daga farko har ‘karshe ya na sauraronta.
Sai da ta gama bayaninta ya maida hankalinsa kan Aunty Saratu ya ce “abinda ta fad’a gaskiya ne? Ta amsa masa da cewa “eh, haka ne.”
Idan har haka ne kuwa ke ce ba ki da gaskiya, ba ki da hurumi akan kayan da mijinta ya kawo alhali mahaifiyarta ta na cikin gidan nan, in da ace kin kwantar da hankali kun zauna lafiya ba zai zama laifi ba don kin ta6a kayan, amma ai wannan isa da mallaka ki ke son nun……”
“Dakata Malam.” Ta katse shi daga maganar da ya ke, a zafafe, kenan ka goyawa matarka da ‘yarka baya, kar ka manta tun kafin Rabi ta zamar surukar Hafiz ni na fara zama surukarsa, kuma in banda mutuwa babu yadda za’a yi Hafiz ya auri Halima.
Don haka wallahi sai ta fito da komai an raba, yadda ta ke surukarsa nima surukarsa ce.”
Yana sauraronta bai ce komai ba, sai ya cewa Halima “tashi ki tafi.”
Mi’kewa ta yi ta fice daga d’akin, sannan ya maida hankalinsa kan Aunty Saratu da ke tsaye ta cika fam kamar kububuwa, tana ganin ba’a yi ma ta adalci ba.
“Wallahi Saratu gab ki ke da kai ni bango a gidan nan, kuma duk ranar da na tashi d’aukar mataki a kanki ba za ki ji dad’i ba, idan kin ce wasa ne ki ci gaba ki ga me zai faru.
Idan banda yanzu na ta6a sanin Hafiz ya na kawo wani abin arzi’ki gidan nan a matsayina na mahaifin Sumayya? Shine yanzu don ba ki da kunya za ki tayar da fitina akan abinda ki ka san ba ki da iko da shi? To indai na isa da Rabi a gidan nan ko tsinke na cikin kayan nan ba za ki mora ba, marar kunyar banza, marar kunyar wofi.
Tashi ya yi ya fice daga gidan gaba d’aya saboda 6acin rai.
Ita kuwa tana komawa d’aki ta zauna a bakin gadonta, zuciyarta cunkushe da tunani, ga Sadiya ta tafi, bare ta samu abokin tattaunawa.
Irin kayan masarufin da ta ga an shigo da shi ba ‘karamin d’aga Mata hankalivya yi ba, don ko lokacin Sumayya bai ta6a kawo kaya masu yawa haka ba, musamman da ta tuna ko da yaushe haka kyautar Hafiz ta ke, kamar wanda bai san zafin neman kud’i ba.
Takaicinta ta ga an saukewa Mama kayan ita kad’ai, duk tsiya da Sadiya ya aura da yanzu ita za’a ci gaba da kawowa wannan garar arzi’kin, amma abin takaici sai dai ta gani a gurin kishiyarta.
Ta tuna lokacin Sumayya, sau da yawa idan an kawo kayan sayar da su take, don ba za ta iya barinsu a gidan Mama da ‘ya’yanta su ci arzi’kin ‘yarta ba, kuma sai ta yi sa’a ba’a ta6a kawo kayan a gaban Baffa ba, don haka har Sumayya ta rasu bai ta6a sanin mijinta ya na kawo wani abin arzi’ki gidanba.
Yanzu kuma ba za ta iya jurar gani ana kawowa Mama wannan ka6akin arzi’kin ba. (Haba Auntu Saratu, ai sarki goma zamani goma, har kin manta lokacin da ki ka tsula tsiyarki?????). Haka ta yi ta karanta wasi’kar jaki ita kad’ai a d’aki.
Sai bayan anyi sallar isha’i ya zo tafiya da ita, har cikin gidan ya sake shigowa su ka gaisa da Baffa, tunda da safe da ya zo baya nan, nan Baffa ya yi masa godiyar abinda ya kawo sosai, sai abin ya bashi mamaki, don tunda ya auri Sumayya har ta koma ga mahaliccinta bai ta6a kawo wani abu gidan Baffa ya yi ma sa godiya ba.
Tare su ka fito daga gidan, yana gaba ta na binsa a baya, hannunta ‘ri’ke da ledar da Mama ta had’a ma ta kayan kad’i kamar busasshiyar bu6ewa, kuka daddawa, kayan ‘kamshi da sauransu.
Tun a mota ya ke tsokanarta da cewa ” yau me Mama ta baki haka ne? Yini d’aya har kin canza, daga gani ko kewa ta ba ki yi ba.”
Murmushi ta yi sai ta kwantar da kanta a kafad’arsa, ta ce “haka ma za ka ce? Bayan duk yinin yau ban ji dad’insa ba saboda kewarka, shine zaka ce min haka.”
“Kar ki manta dai tu’ki nake, kar ki sa mu fad’i.”
Matsawa ta yi kan kujerarta, ta gyara zamanta. Har suka isa gida babu wanda ya ‘kara magana a cikinsu.
Tare suka shiga ciki,. Bayan maigadi ya bud’e ma sa get ya shiga ya yi parking d’in motar.
A gajiye ta ke jin jikinta kamar wadda ta yini ta na aikin wahala, duk da tunda ta je gidan babu aikin da ta yi, tun da ranar ba Mama ce ke girki ba, ita kuwa Aunty Saratu ba’a yi mata gwaninta, sai ta yi ficewarta daga gidanma, gaba d’aya ta shisshiga ma’kwafta su ka gaggaisa.
Wanka ta fara yi, tana fitowa ta yi shafa’i da wuturi, da kyar ta iya saka kayan barci ta kwanta saboda wani irin wahalallen barci da ta ke ji.
Shi kansa Hafiz tun ya na tunanin zuwanta d’akinsa, har ya fatar da rai, ganin har sha d’aya ta wuce ba ta zo ba.
Mi’kewa ya yi, ya sanya slippers a ‘kafarsa, ya fita zuwa d’akinta. Ga mamakinsa a kwance ya same ta, tana ta barci ko wutar d’akin ba ta kashe ba, daga gani barcin ya na yi ma ta dad’i. Sai ya kashe wutar ya sami guri a gefenta ya kwanta.