MAYE GURBI Complete Hausa Novel

*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/15, 9:26 AM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na ashirin da hud’u*
Da asuba da kyar ya iya tashinta ta yi sallah, don wani irin barci ta ke ji, har yaji idonta ya ke ma ta, ta na idarwa a gurin ta kwanta wani barcin ya yi gaba da ita.
Da ya dawa daga masallaci ya same ta a kwance a gurin da ta yi sallah, sai ya girgiza kai kawai, shima ya d’akko pillow ya kwanta a kusa da ita. Bai jima da kwanciya ba shima barci ya yi awon gaba da shi.
Ita ce ta fara tashi, lokacin takwas da rabi ta kusa, har lokacin ba ta jin dad’in jikinta, ga wani nauyin jiki da ta ke ji. Ido ta zuba masa daga inda ya ke kwance, ya na barcinsa cikin kwanciyar hankali, fuskarsa kamar ya na murmushi.
Toilet ta shiga ta had’a ruwa mai zafi sosai ta yi wanka da shi, ko za ta ji dad’in jikinta, motsinta ne ya tashe shi daga daddad’an barcin da ya ke, ya d’an harare ta ya ce shine ki ka tashi ki ka ‘ki tashi na?”
Na ga kamar kana jin dad’in barcin ne, sai na ga bai kamata na tashe ka ba.”
Mi’kewa ya yi daga gurin ya nufi toilet d’inta, don yin wanka ta na cewa “kin kyauta.” Kafin ya gama ya fito har ta gama shiryawa ta gyara d’akin cikin ‘karfin hali, tun da har lokacin ba ta jin dad’in jikinta sosai, kuma ita kanta ba za ta ce ga takamaimai abinda ya ke damunta ba.
Tana ‘ko’karin barin d’akin ya fito don har ta kama handle d’in ‘kofar za ta fita ya fito. Cikin mamaki ya ke dubanta ya ce “ina zawa kuma?
Juyowa ta yi ta na kallonsa ta ce “zan gyara parlour sai na d’ora mana break fast.”
‘Daure fuska ya yi, ya girgiza kai ya ce, babu wani aiki da za ki yi, ke da ba kafiya ce da ke ba, dawo ki kwanta, zan yiwa Umma waya ta aiko mana da abinci.”
Duk yadda ta so ta fahimtar da shi lafiyarta ‘kalau ya barta ta yi aikin ‘ki ya yi, daga ‘karshe dole ta ha’kura ta kwanta, shi kuma ta tafi d’akinsa don ya shirya, aikuwa kamar wadda akai wa ba’a nan da nan barci ya yi awon gaba da ita.
Lokacin da ya dawo d’akin bayan ya gama shiryawa ya samu ta koma barci, tsoro abin ya fara bashi, wannan wane irin barci ne? Duka-duka yaushe ta tashi daga barcin amma har ta koma, bai tashe ta ba, sai ya koma parlour ya zauna.
Yana nan zaune driver’n da ya tura ya dawo bayan ya kar6o musu abinci daga gurin Umma. Sai a lokacin ya tashe ta.
Brush ta fara yowa sannan suka fito, sai da ta shiga kitchen ta d’akko plates da cups, ta ‘karasa dining d’in.
Ta fara bud’e flask d’in, tana ganin ‘kosai da kunun gyad’a wani irin dad’i ya kama ta, nan ta jawo plate ta zubawa kanta ta fara ci, ko Hafiz d’in bata zubawa ba, sai ta kanta ta ke.
Wani irin kallo ya ke ma ta don yau sai ya ga yanayin cin abincinta ya sauya, ba kamar yadda ta saba ba, idan bai manta ba jiya ma haka ta yi a parlour’n Mama, har ya na tunanin ko kewar abincin gidansu ta yi.
Ita kuwa ko a jikinta, sai da ta ci iya son ranta sannan ta bar shi, ta zauna jiran sa, bayan ya gama ta tattare kwanukan zuwa kitchen, ba ta fito ba sai da ta tsaftace.
A parlour ta sami Hafiz a zaune ya saka computer a gabansa ya na ta aiki, wata kujerar ta samu da ban ta zauna, don kar ta takura ma sa.
Ba ta dad’e da zama ba ta ji wata kasala ta rufe ta, sai ta kwanta akan kujerar, nan da nan barci ya kwasheta.
Gaba d’aya ajje computer da ke gabansa ya yi, kawai ya tsaya ya na kallonta, daga jiya zuwa yau ya fuskanci wani irin barci ta ke mai ban mamaki, tun da su ka dawo gidan ba ta yin mintu ashirin ba tare da barci ya d’auke ta ba, zuwa yanzu abin ya fara ba shi tsoro, don gaskiya da alama wannan barcin ba na lafiya ba ne.
Ita kuwa gogar ba ta san wainar da ya ke toyawa ba, sai kwasar barcinta ta ke, cikin kwanciyar hankali.
Sai bayan awa biyu ta tashi, ta ji jikinta ya rage nauyin da ya yi ma ta sosai, tashi ta yi don zuwa ta rage mararta, don fitsari ta ke ji sosai. Shi kuwa Hafiz sai kallonta ya ke, kamar wanda zai gano abinda ya ke damunta a jikinta.
Bayan ta fito ta na shirin zama ya kira ta inda ya ke, a hannun kujerar da ya ke zaune ta zauna, hankalinta na kansa.
‘Dago da fuskarsa yayi yana kallonta, ya ce “Halima me ya ke damunki?”
Cakin mamaki ta ce “damu na kuma? Ni babu abinda ya ke damu na, wani abin ka gani?”
“Daga jiya zuwa yau ba ki kula da yawan barcin da ki ke ba? Sannan d’azu ba ki ga yadda ki ka dinga cin abinci ba, kamar wadda ta kwana da yunwa, kuma jiya ma haka ki kai a d’akin Mama, wannan na yi tunanin kewar abincin gida ki kai, amma na yau ya bani mamaki sosai.
Ki shirya mu je asibiti a duba ki, don mu san abinda ya ke damunki.”
Murmushi ta yi, sannan ta zamo kan kujerar ta kwantar da kanta a ‘kirjinsa, cikin sanyin murya kamar mai yin rad’a ta ce “ni fa lafiya ta ‘kalau, haka kawai na ke jin gajiya kamar wadda ta yi aikin wahala, amma yanzu na daina ji, abinci kuma wallahi kamar ka sani kewa ce ta sani cinsa haka, kasan na dad’a ban ci irinsa ba.
Amma in ban da wannan babu abinda ya ke damu na, lafiya ta ‘kalau, ba sai mun je asibiti ba.”
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/15, 8:55 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na Ashirin da biyar*
Dole ya biye ma ta ya ha’kura, ba don zu zuciyarsa ta so ba. Kuma cikin ikon Allah tun daga ranar bai ‘kara ganin wata alama ta rashin lafiya a tattare da ita ba, duk da kullum cikin jin kasala ta ke, amma sai ta ke daurewa don kar ta tayar ma sa da hankali.
Shima barcin ba wai ta dena ba ne, amma ta na iyakar ‘ko’karinta gurin ganin ba ta yi ba, idan yana gidan, don sau da yawa sai ta ‘kir’kiri wani aiki da za ta yi, don kar barcin ya yi tasiri a kanta.
Sai dai gaba d’aya cimarta ta sauya ga d’an banzan kwad’ayi da ta ke fama da shi, daga yau ta ce ta na son wannan sai gobe ta ce ta na son wancan.
Sannan idan dai ita ta yi girki to duk son ta da shi ba za ta ci ba, sai dai ta ci wani abu da ban, fahimtar halin da ta ke da ummay ta yi, saboda yawan zawu kar6a ma ta abinci da ake ya sa ta hana ta yin girkin gaba d’aya, kullum sai dai ta aiko musu da abinci.
Duk da canje-canjen da ta ke ji a jikinta hakan bai sa ta yi wasa da karatunta ba, don sosai ta d’auke shi da muhimmanci.
Kuma cikin ikon Ubangiji ta na ganin nasara sosai.
Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya har aka d’auki tsayin watanni, ba tare da ta je asibiti don a dube abind ke damunta ba, musamman yanzu da ta daina jin kasalar, shima yawan barcin zuwa yanzu ya ragu, sai dai matsalar yawan cin abincin ta na nan. Tun abin baya damunta yanzu har ya fara damunta, musamman ganin yadda ta yi ‘kiba sosai kamar ba ita ba, ga wani kumatu da ta ajje kamar an hura balloon, sai kuma jifa-jifa ta ji kamar wani abu na yi ma ta kicking a ciki.