MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Shi kansa Hafiz d’in ya kula da haka, don haka ranar ya dage sai ta shirya sun je asibiti, wannan karon ba ta musa ba don itama zuwa yanzu ta tabbatar akwai abinda ya ke damunta.
Asibitin prime alliance da ke kwanar maggi su ka je, bayan sun gama yiwa likita bayanin abinda ke tafe da su, tambaya ta farko da ya fara yi ma ta itace when last da ta ga period d’inta?
Tuni ta shiga rud’ani, don ta manta watannin ma ita, murmushi kawai likitan ya yi, sai ya d’auki waya ya kira wata nurse, tare ya ce su je da Halima ta bata fitsarinta ayi mata PT ( pregnancy test).
Cikin mintunan da ba su fi goma ba nurse d’in ta kawo result d’in, likitan ya kar6a, bayan ya duba ya kalli Hafiz fuskarsa d’auke da murmushi ya ce “congratulations, matar ka na d’auke da juna biyu.
Fuskarsu cike da mamaki suka d’ago kai suna kallon likitan, don tunaninsu bai ta6a kai wa nan ba.
Gaba d’ayansu farin ciki su ke da abinda likitan ya sanar musu, sai dai Hafiz farin cikinsa ya gauraya da fargaba, musamman da ya tuna cewa a dalilin haihuwa ya rasa sumayya.
‘Dakin scanning likitan ya umarce su da zuwa, don ya na son ya tabbatar da watannin cikin, bayan ya yi ma ta scanning d’in ya ke sanar da su cikin ya na cikin sati na goma sha bakwai. Sai a lokacin ta fahimci motsin da ta ke ji a cikinta ashe na Baby ne.
Ita kanta Halima sai a lokacin ta ke ganin tarin wautar ta, duk tsahon lokacin nan ba ta ganin period d’inta amma tunaninta bai ta6a ba ta akwai dalilin faruwar hakan ba.
Shawarwari sosai ya ba su na yadda za su kula da cikin, daga ‘karshe ya rubuta mata magungunan da za su ‘kara mata kuzari, ya sallame su.
Tun a mota Hafiz ya kira Umma ya sanar da ita, sai kawai ta ce ‘Allah ya inganta, don a tunaninta daga Hafiz d’in har Haliman sun san da samuwar cikin.
Amma ga mamakinta sai ta ji sa6anin haka, lallai dukkansu da sauransu in dai har ba za su gane samuwar ciki ba har ya d’auki irin wannan dogon lokacin, musamman Halima da ta ke mace, ita da cikin ya ke jikinta.
Cikin lokacin wata irin kulawa ya ke bata, don da ya na da hali ko numfashi ba zai barta ta yi da kanta ba, sai dai ya yi mata.
Babban taimakon da Allah ya yi mata cikin tun farko ba mai yawan laulayi ba ne, shiyasa ma har ya d’auki lokaci ba tare da ta san da samuwarsa ba.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/16, 3:01 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na ashirin da shida*
Zuwa yanzu cikin Halima ya tsufa sosai, kullum zuba ido ake da haihuwa. Shi kuwa oga Hafiz duk wani abu da maijego da jaririnta za su bu’kata ya saye shi, sai jiran zuwan haihuwa da ake.
A wannan tsakanin kuma sai ta fara ganin wasu sauye-sauye daga gare shi, da baya fita hirar dare, amma yanzu sai ya tsiri fita, idan ya dawo daga sallar isha’i zai fesa wanka, ya baza ‘kamshi ya fice, sai goma na dare zai dawo gidan, wani lokacinma sai ya zarta hakan.
Kuma ko a gidan ya ke a zaune bashi da lokacin hira da ita, idan ba aiki ya ke da computer sa ba, to sai ya d’auki waya ya kama chatting, abinda a baya sam bai dame shi ba.
Tun abin ba ya damun Halima har ya fara damunta, don a tunaninta wani laifin ta yi masa ya ke hukunta ta, dan haka ranar ta same shi har d’akinsa da nufin bashi ha’kuri.
Tsaye ta same shi a gaban wardrobe d’aure da towel, yana duba kayan da zai saka, alamun daga wanka ya fito.
Gefen gadonsa ta samu ta zauna da ‘kyar, ga mamakinta ya na kallonta amma ko a jikinsa, sa6anin baya da zai ta yi ma ta sannu.
Katse shirun da d’akin ya yi ta yi da cewa ” dama na zo ne don in baka ha’kuri, ko wani laifin na yi maka ba tare da na sani ba, a tunani na bai kamata ka hukuntani ta wannan hanyar ba ko don duba da yanayin da na ke ciki.
Idan wani abu na yi maka gara ka zaunar da ni ka sanar da ni, ni kuma sai in gyara kuskurena sannan in baka ha’kuri, ba wai ka dinga fushi da ni ba.”
Sai da ya gama saka kayan a jikinsa sannan ya juyo ya dube ta ya ce “ni na ce kin yi min laifi?”
Cikin sanyi jiki ta ce “a’a, sai dai yadda ka sauya min ne ya sa ni yin tunanin ko akwai abinda na yi maka wanda zuciyarka ba ta so.”
“Ke ki ka ga chanjawar tawa amma ni ban gani ba, a cikin duk ha’k’kinki da ya rataya a wuya na wanne na kasa saukewa? Ciyarwa, shayarwa ko suttura? Ba na son ‘korafi akan abinda bai kai ya kawo ba Halima, bai zai yiwu ki ce yadda ki ke so haka za ki samu……”
Maganarsa ta katse sakamakon kiransa da aka yi a waya, da sauri ya d’aga ya ce “gani nan fitowa ranki ya dad’e, afwan.”
Daga nan ko ta kan ta bai sake bi ba, ya yi ficewarsa daga d’akin ya barta zaune ita kad’ai.
A gurin da ya barta nan ta zauna hawaye na zuba daga idanunta, tsoronta d’aya kar Hafiz ya ce zai juya mata baya a yanzu, bayan ta gama sallamar ma sa da dukkan soyayyarta.
Haka ta gaji da karanta wasi’kar jaki ta tashi ta bar d’akin. Kullum adda’arta d’aya Allah ya kawo ma ta d’auki akan abubuwan da su ke faruwa, amma sai ta ga kamar zuga shi ma ta ke.
A haka suke zaune, sam zaman ba ya yi mata dad’i daurewa kawai ta ke, musamman ganin halin da ta ke ciki, kar damuwa ta haifar mata da illa ga lafiyarta.
Bayan wasu kwanaki, Halima na zaune a parlour da daddare ta tashi ta shiga kitchen da niyyar had’a tea, saboda yunwar da ta ke ji, don tuni ta daina girki, tun da idan ta yi ma Hafiz ba ci ya ke ba, yadda ta ajje haka za ta d’auki kayanta, sai ta sallama yin girkin gaba d’aya, idan ta ji yunwa sai ta samarwa kanta abu mai sai’ki ta ci.
A kitchen d’in ta zauna ta shanye tea d’in tare da cake bayan ta had’a, ta na cikin kitchen d’in ta ji tsaiwar motar Hafiz harabar gidan. Fitowarta parlour’n ya yi dai-dai da shigowarsu shi da wata budurwa.
Kallo d’aya za ka yi mata ka tabbatar da cewa ita d’in kyakkyawa ce, irin ta gaban motar nan. Sanye ta ke da wani arnen material, d’inkin riga da skirt, komai na jikinta ya bayyana, saboda yanayin d’inkin, sai wani yatsina ta ke, kamar wadda ta ga kashi.
‘Kamewa Halima ta yi tana kallon ikon Allah, a kujerun da ke parlour’n su ka sami guri su ka zauna, sai Hafiz d’in ya mi’ke ya ce “sweet ina zuwa” ya shiga d’akinsa.
Itama yarinyar tashi ta yi ta bi bayansa, Halima na tsaye ta na kallonsu ko ‘kwa’k’kwaran motsi ta kasa.
Da kyar ta iya Jan ‘kafarta daga gurin zuwa d’akinta, akan gadonta ta kwanta, sai dai kamar ta kwanta akan ‘kaya haka ta ji, nan ta ke ta ji wani irin azabebben ciwo da ba ta ta6a jin irinsa ba sai a lokacin, zagaye d’akin ta fara yi ta na yarfe hannu bakinta na d’auke da salati, zuwa wani lokaci ta ji abu mai d’umi na bin ‘kafarta, ta na dubawa ta ga jini ne, wannan ya ‘kara tayar da hankalinta.
Wayarta da ke ajje saman dressing mirror ta d’auka ta kira Aunty Murja ta sanar da ita halin da ta ke ciki.
Kafin Aunty Murja su zo har ta fita daga hayyacinta, lokacin da su ka zo da kyar su ka iya fita da ita daga cikin gidan zuwa harabar gidan, inda mijinta ya yi parking d’in motarsa.