MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Shi kansa ya tsorata da yadda ya ga jini na zuba a jikinta, ana saka ta a motar ya tada motar suka bar gidan, wani private hospital da ke unguwar su kai ta.
Cikin gaggawa aka shiga da ita labour room, dukkansu suna tsaye jigun-jigun, ita da Hidaya babbar ‘yarta da suka taho tare.
Wayarta ta kar6a a hannun Hidaya ta kira Mama ta sanar da ita halin da Haliman ta ke ciki, sannan ta sanar da ita Hafiz bai san me ke faruwa ba, a sanar da shi, ita ba ta da number d’in sa.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/20, 3:49 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na ashirin da bakwai*
Wasu takardu yaronsa ya kawo ma sa a lokacin, shiyasa ya dawo gida don ya adana su, bayan ya ajje su a cikin drower sai ya shiga toilet, yana fitowa ya ci karo da Hajar da ke zaune a gefen gadonsa, wai tana jiransa.
Har cikin zuciyarsa bai ji dad’in biyo shi da tayi ba, domin yin hakan cin fuska ne ga matarsa, sannan zuciyarta za ta iya raya ma ta abinda ba shine ba.
Duk yadda ya so ya nuna mata 6acin ransa amma ba zai iya ba, don wani irin kwarjini ta ke, masa, don ko biyo shi da tayi gidan ba’a son ransa ba, don dai ba zai iya hana ta ba ne.
Tare suka fita daga gidan suka koma gidan su Hajar d’in. Bai dad’e da komawa ba kiran Aunty Murja ya same shi, wannan ne dalilin da ya tafi asibitin hankali tashe.
Zuwansa ya yi dai-dai da fitowar wata nurse ta na tambayarsu, kayan haihuwa. Sai lokacin Aunty Murja ta tuna da batunsu, don tun lokacin da ta ga Halima kwance cikin jini, hankalinta ya tashi ta manta da komai.
A take Hafiz ya juya gida jin Aunty Murja ta ce sun manta ba su d’akko ba.
Cikin mintuna kad’an ya dawo, aka shiga da kayan.
Bayan wani lokaci, aka fito da baby kyakkyawa da shi, Masha Allah, ita kuma aka kai ta d’akin hutu.
Kafin wani lokaci labarin haihuwar ya gama karad’e dangi, kowa sai murna ya ke, ana ta farin ciki.
Sai washegari aka sallame su, gidan Umma aka wuce da ita, kamar yadda ta bada umarni, don gudun samun sa6ani, don tun a ranar da akai haihuwar Aunty Murja ta sami Hafiz da maganar su na son tafiya da ita gida, shi kuma ya shafawa idonsa toka ya hana.
Ganin maganar ta na neman kawo sa6ani a tsakaninsa da Haliman sai Umma ta sami Aunty Murja ta sanar da ita, cewa ita za ta tafi da ita gidanta. Wannan shi ya kawo masalaha a maganar.
__________________________________________________
Kulawa sosai Umma ta ke bata, kamar ‘yar cikinta. Babban abinda ya ke ba ta mamaki da Hafiz ko a waya bai damu da ya kira ta ba, ko ya ji lafiyar baby’n, don ba kullum ya ke zuwa gidan ba ma sai san da ya ga dama, bare kuma ta sa ran kira a waya.
Da haka har akai suna babu wani canji da ta gani daga gareshi.
Taron suna akai wanda aka sha shagali sosai, inda yaron ya ci suna Ahmad. Hafiz ya kashe kud’i sosai kamar bai san ciwon nemansu ba. Ita kuma Umma ta yi halin girma, don sai da ta sa Hafiz ya bawa Halima wadatattun kud’i saboda hidimar sunan, kar ta ga kamar ana son danne mata ha’k’kinta ne, shiyasa ta nemi ta dawo wurinta da zama.
Tun Umma ba ta fahimta ba, har ta fahimci irin zaman da suke. Ranar da misalin 10:00am bayan ta gama duk abinda ya kamata ta sami Halima har d’akin da ta ke.
Gefen godon d’akin ta samu ta zauna, sai ta mai da hankalinta kan Halima da ke ninke kayan Ahmad, wanda aka wanke da safe da akai masa wanka, ta ce “Halima dawo nan, magana na ke so mu yi da ke.
Nan take ta bar abinda ta ke, ta dawo gaban Umma ta zauna akan filo, kamar yadda Umman ta hana ta zaman ‘kasa.
“Ina so ki d’auke ni tamkar mahaifiya ba suruka ba, Allah ya sani ni a matsayin ‘ya na ke kallonki, bana son ki 6oye min wani abu da ki ka sani, domin idan matsala ta taso gaba d’ayanmu ta shafa, ba mutum d’aya ba.
Mene ne matsalarki da mijinki? Tun farkon zuwanki gidan nan na lura akwai matsala, musamman yadda sai ya yi kwana biyu bai zo gidan nan ba, bayan a baya ba haka ya ke ba,maganar da na ji ku na yi jiya, shi ya ‘kara tabbatar min da zargi na.
Wace yarinya ce na ji kuna magana a kanta? Ba na son ki 6oye min komai.”
Tun daga farkon lokacin da Hafiz ya fara sauya mata ta zayyanawa Umma har zuwa ranar da ya zo da ita gidan sannan ta ‘kara da cewa “ya ce min aurarta zai yi, amma ni abinda na ke ganin kamar cin fuska ne yadda zai shigo da ita har cikin gidan kuma ta bishi cikin d’aki….”
“Wanna ba kama ba ne Halima, cin fuska ne, ta yaya zai shigo miki da mace har cikin gida su shiga d’akinsa tare da ita? Yanzu abinda na ke son sani shine yarinyar ‘yar ina ce?”
“A nan ma’kwaftanmu ne gidan Alhaji Miko, ‘kanwar matarsa ce.”
Cikin mamaki Umma ta ce “gidan Alhaji Miko? Kina nufin ‘kanwar matarsa wannan shuwar ce?”
“Eh Umma ‘kanwarta ce, don ya ce ma wannan satin za su je Maiduguri da ita ya gaida iyayenta.”
Girgiza kai Umma ta yi cike da jimami ta ce, lallai akwai matsala, dole ki kasa gane kan mijinki, yanzu abinda na ke so da ke don Allah kar ki bari mahaifiyarki ko wani na jikinki ya ji wannan maganar, na yi miki al’kawari insha Allah nan da d’an lokaci, sai komai ya wuce kamar bai faru ba.”
Haka Umma ta zauna ta dinga kwantar ma ta da hankali, har zuwa wani lokaci sannan ta tafi kitchen don d’ora abincin rana.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/25, 6:57 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na ashirin da takwas*
Har ta gama girkin da ta ke tunanin al’amarin da ta ke kenan, tasan Alhaji Miko don matarsa uwargidan ‘yar ma’kwaftansu ce, bayan ita ya ‘kara wani auren, kuma suna zaman lafiya, tun lokacin da ya auro wannan shuwar zaman lafiya ya yi ‘karanci a gidansa, daga ‘karshe sai da ta kai ga ya kore su, daga su har ‘ya’yansu ya ce baya ba’katarsu a rayuwarsa.
Gaba d’aya ya susuce a kanta, ko danginsa babu wanda ya isa ya je gidan, ta dai mayar da shi kamar ra’kumi da akala sai yadda ta yi da shi.
A ranar da daddare bayan Abba ya dawo gida bayan ya gama cin abinci ta same shi da maganar. Ta sanar da shi duk yadda su kai da Halima.
Shi kansa maganar ba ta yi masa dad’i ba, ya kwantar mata da hankali sosai akan maganar, ya ce ta bari zai tattauna da wani malaminsa mai suna Malam Saminu.
Malamin makarantar allo ne, mutumin kirki ne sosai, sam baya yarda ya yi abinda ya san zai cuci wani, ko ya sa6awa Ubangiji, shiyasa tafiyarsu ta yi nisa sosai da shi, don shi Abba ba ya son yin abinda zai zama kamar mutum ya yi shirka.
Washegari Abba ya je har gida ya same shi da maganar, sai ya bawa Abba ‘kwarin gwiwa da ya kwantar da hankalinsa, insha Allah za’a d’auki matakin da ya dace akai, amma yanzu ya bashi kwana uku zai yi istihara akai duk abinda ake ciki zai sanar da shi.