HAUSA NOVELMAYE GURBI Complete Hausa Novel

MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Bayan ta ajje jakar hannunta, ta cire hijabin jikinta, ta sami guri ta kwanta, don ta d’an sami barci kafin lokacin sallar azahar ya ‘karasa.

Lokacin da aka fara kiran kiran sallah Sumayya ce ta tashe ta daga bacci, sai da ta shiga band’aki ta fito, sannan ta yi alwala, ta koma d’aki tayi sallarta, bayan ta gama addu’o’inta, ta fito ta shiga kitchen don d’auko abincinta, amma ga mamakinta, ba ta sami abinci ko kad’an a kitchen d’inba.

Ba ta yiwa kowa magana ba, ta juya zuwa d’akinsu, don idan da sabo ya ci a ce ta saba, da halin Aunty Saratu, jakarta ta bud’a ta d’auko kud’i, ta fita da su.

Ta sami ‘kaninta Aliyu, ta aike shi ya sayo mata abu, sai ta koma d’akin ta kwanta ta na jiran dawowarsa.

A kullum tunaninta wacce irin ‘kiyayya matar nan ta ke mata? Ita da gidan ubanta amma ace anyi girki babu rabonta, wannan abu ya na ba ta mamaki, tunda ba ta san me ta tsare mata a rayuwa ba.

Lokacin da Aliyu ya dawo daga aiken, ta kar6a ta shiga kitchen, cikin mintunan da ba su fi ashirin ba, ta gama dafa jallop d’in taliya, wadda ta ji kifi sai ‘kamshi ta ke.

A ‘kofar kitchen d’in su kai kici6is da ita, ita Halima ta fito, ita kuma ta na niyyar shiga, hannun ta kai da nufin kar6e food flask d’in hannunta, cikin zafin nama Haliman ta goce, ba tare da ta samu nasarar kar6ar abincin ba ,cikin masifa ta ce “uban waye ya baki damar shiga kitchen kiyi girki? Duk rashin kunyar da ki ke ji ni zanyi maganinki, kuma wallahi wannan abincin baki isa ki ci shi ba.”

A d’age Haliman ta kalleta ta ce “Allah ko?”

Ta juya ta yi tafiyar ta, cikin sauri ta tari gabanta tana kokwawar ‘kwatar kwanon, sai ta ji magana daga bakin ‘kofar shigowa gidan, “ke Saratu mene ne haka? Bana son zubda girma da sayawa kai raini fa, ina ke ina kokwawa da Halima?”

Nan take sai ta fashe da kukan munafurci, cikin kuka ta ke cewa “yanzu rainin da Halima ta yi min har ya kai na ajje maka abinci, ta d’auka ta ce shi za ta ci a gidan nan, ni wallahi na gaji da wannan abin, ko uwarta da muke auren miji d’aya da ita ba ta takuramin ba sai ita.”

Kallonsa ya mayar kan Halima cikin alamar tambaya. Cikin ladabi ta ce “Abba abinci na na zo d’auka, na tarar ba ta raba da ni ba, sai na aiki Aliyu ya yo min cefane na yi girki, shine ta zo wai wallahi ban isa na ci wannan abincin ba.”

Ai makirar sai ta kama sallallami ta na tafa hannuwa, kamar wadda akaiwa sharri.

Sumayya ya ‘kwallawa kira, ta fito da sauri, don amsa kiran mahaifinta, duk da ta na jin duk abinda ya ke faruwa a tsakar gidan, wannan hali na mahaifiyarta ya na 6ata ma ta rai, don dai ba ta da yadda za ta yi ne, amma itama ta sani ba yau ce rana ta farko da ta yi girki ta hana Halima a cikin gidan ba.

“Wane irin abinci aka dafa a gidan nan yau da rana?” Ya jefo ma ta tambaya, bayan ta sami guri ta tsugunna.

“Shinkafa da wake aka dafa.” Ta bashi amsa kai tsaye, ba tare da ta kula da hararar da mahaifiyarta ta ke wurga ma ta ba.

Dubansa ya mayar ga Halima ya ce ” bud’e min kwanon nan mu ga abinda ya ke ciki.”

Tana bud’ewa lafiyayyar jollop d’in taliya da ta ji kifi da kayan had’i ta bayyana, ya maida hankalinsa, inda Aunty Saratu ke tsaye, sai ya ga, ba ta gurin, kai kawai ya girgiza ya wuce ya na cewa su Halima su ma su tafi.

 

 

*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[9/28, 4:15 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*

*_UMMU AISHA_*

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Shafi na uku*

Itama Haliman daga nan d’akin Mama ta shiga, sai da ta sami guri ta zauna, Maman ta ce “wato Halima ba kya jin magana ko? Sau nawa na ke gaya miki cewa Saratu ba abokiyar yin ki bace? Amma don rashin kunya ki dinga biye ma ta kuna sa’insa a cikin gidan nan, wato duk abinda za ki jawowa mutum magana kin iya shi ko?”

“Ki yi ha’kuri Mama, wallahi nima ban yi niyyar tanka ma ta ba, shiyasa da na je kitchen ban sami abinci ba ma, ban yiwa kowa magana ba, sai na aika Aliyu ya yo min cefane na girka abinda zanci. Kin san da safe da tea da bread na karya, kuma kin san baya ri’ke min yunwa, yanzu kuma na dawo ba ta raba abinci da ni ba, saboda Allah kuma na girka sai ya zama laifi, don dai ba ta so a zauna lafiya?”

Mama na sauraronta har ta ‘kare maganarta sannan ta ce “koma mene ne, ba mutunci ba ne ki dinga fad’i in fad’a da matar mahaifinki, don ko babu komai matsayin uwa ta ke a gare ki, sannan yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, wannan kad’ai zai iya zame miki matsala idan Allah ya kawo miki miji, za’a iya cewa kina taya mahaifiyarki kishi, mutane ba za su duba laifin na waye ba.”

Muryarta a sanyaye ta ce “shikenan Mama, insha Allahu irin hakan ba za ta sake faruwa ba, yau d’inma ba kula ta na yi ba, tunda har na taho, ta zo ta kama ni da kokwawa sai ta kar6e.”

____________________________________________

Shi ma Baffa da ya shiga d’akinsa ga mamakinsa, sai ya sami abinci a ajje, wannan shi ya tabbatar ma sa da cewa neman magana ne kawai ya sa Saratu, shiga harkar Halima.

Zuwa wannan lokacin ha’kurinsa ya fara gazawa a kanta, dama saboda darajar ‘ya’yanta ya dawo da ita gidansa, amma gaskiya idan ba ta sauya hali ba zai d’auki mataki a kanta.

Ko abincin bai ci ba, yadda ta kawo ta ajje haka d’auki abinta, wanda hakan ba ‘karamin sake 6ata ma ta rai ya yi ba.

Bayan ya dawo daga sallar isha’i ya kira ta duk da ranar ba ita ke da girki ba, bayan ta je ne ya ke tambayarta dalilin da ya sa tayi abinci ta raba babu Halima.

Sai ta yi mirsisi, wai ita sharri ake ma ta, ta kama borin kunya. Ya na jinta har ta gama yin ta sannan ya ce ma ta cikin kakkausar murya ” ba zan lamunci irin wannan ba Saratu, ba zai yiwu in je in sha wahala in nemo abinci kuma ya gagari ‘ya ta ba.

Duk abinda ya ke faruwa a gidan nan ina sane, rashin tanka miki kuma da bana yi, ba yana nufin zan ci gaba da zuba miki ido ki yi duk abinda kika ga dama ba ne.

Wallahi daga yau ba ke ba, ko uwar da ta haifi Halima ce ta yi girki ta hana ta a gidan nan to sai na d’auki mataki a kanta, kuma abinda zan yi ba zai yiwa kowa dad’i ba.

Wannan ya zama karo na ‘karshe da irin wannan zai sake faruwa, in kuma ba haka ba duk hukuncin da ya biyo baya ba ruwana.”

Wannan shi ya ‘kara hura wutar ‘kiyayya tsakanin ta da Halima, don a kullum ji ta ke kamar ta zuba mata fetur ta hura mata wuta ta mutu kowa ma ya huta.

____________________________________________

Shirye-shirye ake sosai na bikin Sumayya, da ke ‘kara matsowa, don har an kawo lefe daga gidan miji.

Aunty Saratu kuwa kullum cikin yarda magana ta ke ga Halima da mahaifiyarta. Yayin da a gefe d’aya kuma babbar ‘yarta da ke da aure mai suna Karima kullum cikin zuwa kasuwa sayayya suke ita da ‘kanwar Aunty Saratun.

Duk wani ‘ko’kari da Sumayya za ta yi don ganin Halima sun gaisa da angon na ta mai suna Hafiz, amma abin ya ci tura, daga ‘karshe dole ta ha’kura, tunda ta fuskanci had’uwarsu ce ba ta so.

Tuni ba’kin nesa sun fara zuwa, don ranar Alhamis za’a yi walima, juma’a kuma kamu, don ma amaryar ba mai son bidi’a ba ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button