MAYE GURBI Complete Hausa Novel

____________________________________________________
Kamar yadda su kai al’kawari kuwa a bayan kwana uku Abba ya koma, bayan Malam d’in ya sallami ba’kon da Abban ya tarar da su tare, sannan ya shiga cikin zauren da Malamin ke zaune.
Bayan sun gaisa Malam d’in ya ce “Alhaji nayi istihara kamar yadda na ce ma, kuma gaskiyar magana sihiri aka yiwa yaron nan, sai dai da izinin ubangiji zan yi iyakar ‘ko’karina wurin ganin na karya abin.
Yanzu ina so ka samu lokaci ka turo min shi, ina son ganinsa.”
“To shikenen Malam Insha Allah zan turo maka shi, ni dai babban burina a karya abunda ke jikinsa. Ba zan so ya auri yarinyar nan ba, domin alamomi sun nuna ba mutuniyar kirki ba ce. In dai tun a waje mace zata yiwa mutum asiri to Allah ne kad’ai ya san abinda zai faru idan ta shiga gidansa a matsayin matarsa.”
“Ka kwantar da hankalinka, insha Allah ba za ta ta6a samun nasara akansa ba, wannan ma Allah ne ya ‘kaddara hakan zai faru. Babbar matsalar matasanmu na yanzu shine, ba sa son gyara jikinsu, sai su ce su babu abinda zai same su.
Sun manta sihiri ya kama fiyayyen halitta ma, bare mu, sai ka ga mutum na zaune da kowa da kyakkyawar zuciya, amma wani yana ‘kudure da mugun nufi akan sa, ba tare da ya sani ba.
Shiyasa ya ke da kyau mutum ya shirya jikinsa ba sai an sami matsala a zo ana neman magani ba, wani in ya tashi rayuwar mutum ya ke nema ko lafiyarsa.
Idan har mutum zai kula da karanta azkhar d’in safiya da maraice, da kuma na kwanciya barci zai yi wuya sihiri ya kama mutum kuma ko da ace zai kama d’in abin ba zai ta’azzara ba.”
“Tabbas haka ne, Allah ya tsare mu daga sharrin masu sharri.”
“Amin ya Allah”
Da haka su kai sallama Abba ya tafi gida, zuciyarsa cike da farin ciki, don yasan Malam Saminu mutum me mai jajircewa akan abinda yasa a gaba.
_____________________________________________________
“Oh! Ikon Allah, gaskiyar hausawa da suka ce in da ranka ka sha kallo, ai yanzu tun a duniya Allah ya ke nunawa mutum iyakarsa.
Yau Allah ya sakawa Sumayya cin amanarta da akai, yo dama duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba, ai tasa ko d’umi ba za ta yi ba.
‘Karyar fankama ta ‘kare, kishi da shuwa sai an shirya, kai amma Hafiz ya birge ni, da wannan aure da ya ke shirin yi, dole yarinya ta dawo gidan ubanta, don matar da zai aura ta fi ‘karfin zama da kishiya.
Yo tun yanzu ma gidan mijin ya fi ‘karfin zamanta bare kuma amarya ta shigo.”
Duk maganganun da Aunty Saratu ta ke, Mama da ke aiki a kitchen na jinta, amma ta bawa banza ajiyarta, kamar ba ta san me take ba. Amma can cikin zuciyarta Allah kad’ai ya san damuwar da ta ke ciki. Allah-Allah ta ke, ta gama abinda ta ke, ta kira Halima ta ji gaskiyar al’amarin.
Sai bayan sallar magriba ta samu kiran Haliman, bayan sun gaisa take tambayarta lafiyar Ahmad, da Umma.
“Dama tambayarki na ke son yi Halima, menene gaskiyar magana game da auren da mijinki ya ke nema?”
Cikin mamaki ta ce “Mama a ina ki ka san wannan maganar?”
“A bakin Saratu na ji, maganar ta bani mamaki, tun da ni dai ban ji daga bakinki ba, ban san dalilinki na ‘kin gaya min ba.
A take Halima ta kwashe komai da ya ke faruwa ta gayawa Mama har yadda su ka yi da Umma.
Jikin Mama ya yi sanyi da jin maganar, duk da ta ji dad’in matakin da Umma ta ce za ta d’auka akan al’amarin.
Tayi Mata nasiha sosai, kuma ta ‘kara da cewa “ko nan gaba kar ki ‘kara 6oye min magana irin wannan, ko da ba zan iya yi miki komai ba, zan taimaka miki da addu’a, suk duniya babu wanda zauna fini shiga damuwa idan wani abu ya same ki.”
Daga ‘karshe sukai sallama kowacce ta kashe wayarta.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[11/27, 5:30 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na ashirin da tara*
A ranar Abba ya nemi Hafiz a waya ya sanar masa ya zo yana son ganinsa. Bai sami damar zuwa ba sai dare, don a nan ya ci abinci tare da Abban.
“Dama dalilin kiranka in son in sanar da kai ranar asabar idan Allah ya kai mu akwai d’aurin auren da na ke so ka wakilce ni a Katsina, saboda ba zan sami damar zuwa ba.”
Har cikin zuciyarsa bai ji dad’in maganarba, saboda tafiyar da suka shirya za su yi Maiduguri shi da Hajar, amma ba zai iya musawa mahaifinsa ba, dole sai dai su d’aga tafiyar zuwa wani satin.
Bai bari Abba ya fahimci damuwar da ya shiga ba, sai yace “Allah ya kaimu ranar, insha Allah zan shirya na je.”
Cikin jin dad’i Abba ya ce “Masha Allah sai magana ta gaba, ina son gobe da safe idan Allah ya kaimu ka je ka gaida Malam Saminu, don sai cigiyarka ya ke tun kwananki, to d’azu da mu ka had’u na yi masa al’kawarin insha Allah yau za ka je ku gaisa.”
Sai ya amsa da cewa “babu matsala Abba in Allah ya yarda zan je goben.”
Daga nan suka fad’a wata hirar da ta shafe su har zuwa wani lokaci, sannan ya tashi ya shiga wurin Halima.
Sam babu wata magana mai dad’i a tsakaninsu duk da yadda abin ya ke damunsa, ko da yaushe ta na ma’kale a zuciyarsa, amma da ya zo inda ta ke, sai ya ji sam baya son kasancewa kusa da ita.
Bai wani dad’e a d’akin ba, saboda wani haushinta da ya ke ji marar dalili, ya dai d’auki d’ansa kafin ya fita daga d’akin.
____________________________________________________
A 6angaren Aunty Saratu kuwa duniya sabuwa, ta na cikin farin ciki, kan labarin da ta samu na halin da Halima ta ke ciki ita da Hafiz daga bakin Sadiya, da ta jiyo a gurin wata ‘kawarta ‘yar unguwar su Haliman.
Kusan duk ma’kwaftan sun san yadda zuwan wannan shuwar ya tarwatsa gidan Alhaji Miko shiyasa yanzu da Hafiz ke soyayya da ‘kanwarta labarin ya bazu a unguwa, don wasu ma cewa suke auren Haliman mutuwa ya yi, kowa dai da abinda yake fad’a.
Duk abinda ta ke Mama bata ta6a nuna ta san tana yi ba, bare ta kula ta. Wannan abu yana ci mata tuwo a ‘kwarya, don so ta ke Maman ta kulata ta gaya mata maganganu, sai kuma bata samu dama ba.
Ita kuwa Mama tun daga ranar da su kai magana da Halima ta san halin da ta ke ciki ta dage da addu’a da yawan sadaka da niyyar duk wanda ke da niyyar kawo na’kasu a cikin zaman auren Halima da hafiz Allah ya yi musu maganinsa.
Kamar yadda Abba ya umarci Hafiz washegari kafin ya tafi kasuwa sai da ya je gidan Malam Saminu, bayan sun gaisa ya yi masa nasiha sosai akan rayuwar duniya. Cikin hikima ya nuna masa muhimmancin ri’ke addu’o’in kariya, sannan ya bashi wani rubutu, ya yi masa bayanin yadda zai yi amfani da shi, da wani ruwan addu’a da zai yi amfani da shi da ganyen magarya.
Ya yi masa bayanin yadda zai yi amfani da su, sannan ya umarce shi da yawaita yin sadaka don tana maganin musiba.
Godiya ya yi masa sosai, sannan ya d’auko kud’i daga aljihunsa masu yawa ya bashi, da farko Malam d’in ‘kin kar6a ya yi, don cewa ya yi shi ba don ya biya shi ya yi masa ba, amma Hafiz ya dage dole sai da ya kar6a.
____________________________________________________
Kamar yadda Malam ya bashi umarni haka ya dinga amfani da magungunan da ya bashi. Cikin kwanaki ‘kalilan ya fara jin sauyi a tare da shi, don a baya yana jin kamar ana bashi umarni ne akan duk wani abu da zai aikata, ko da zuciyarsa ba ta so, sai ya yi.