MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Sannan yawan jin haushin Halima da ya ke idan ya ganta yanzu ya ragu da kashi tamanin cikin d’ari.
A hankali ya ji Hajar tana fita daga zuciyarsa, sai a lokacin ya ke tunanin shi bai ma san yadda akai ya fara soyayya da ita ba, don ko ba komai ya na sane da yadda auren yayarta ya tarwatsa gidan ma’kwafcinsa Alhaji Miko, amma yayi gangancin fara soyayya da ita.
Ranar juma’a yana zaune a gida tun bayan dawowarsa daga masallaci, wani aiki yake a computer, so yake sai ya gama zai tafi can gida ya ci abinci, kamar yadda ya mayar al’adarsa a yanzu, tun bayan warwarewar kamai.
Takun takalmi ya dinga ji ‘kwas! ‘kwas! An shigo parlour’n ba tare da anyi sallama ba.
Barin abinda yake yayi, ya d’ago kai, ya ga mai shigowa kai tsaye, babu sallama bare neman izini. Ga mamakinsa Hajar ya gani, tana dumfaro kujerun parlour’n, sai wani shan ‘kanshi ta ke.
Har ta sami guri ta zauna bai tanka Mata ba, don yana son ya ga iya gudun ruwanta. Ita kuma a nata 6angaren jira take yayi mata magana, amma ga mamakinta sai taga ya ci gaba da aikinsa kamar bai san da samuwarta a wajenba.
Cikin ‘karfin hali ta nisa ta ce “ban gane abinda kake nufi da ni ba Hafiz, kana kallona amma kayi kamar baka san ina gurin ba, bayan ka san kayi min laifi.
Barin abinda yake yayi, ya d’ago yana kallonta, cikin mamaki ya ce “laifi? Wane laifi nayi miki kuma?”
“Au kana nufin baka san laifin da kayi min ba? Mun yi al’kawarin zuwa garinmu ka gaida mahaifana, ka watsar da maganar, yanzu kuma ka watsar da ni, ko a waya ka daina nema na bare na sa ran zaka zo gurina, amma ka ce baka san me kai min ba?”
Sai da yayi murmushi ya ce “banga dalilin da zai sa naje garinku ba, tunda nasan ba aurarki zanyi ba, da farko ma ban san abinda ya kaini wueinki ba, wannan ne dalilin da yasa na daina kiranki a waya, son tun farko ma ni ban san yadda akai na fara soyayya da ke ba, amma yanzu ina son ki manta da wata magana ta soyayya ta ta6a shiga tsakanina da ke.”
Yana gama fad’ar haka ya mi’ke ya nufi d’akinsa tare da cewa, idan kin fita ki ja min ‘kofar parlour’n.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[12/1, 8:30 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na talatin*
????????????
*Not edited*
Cikin mamaki ta dinga binsa da har ya shige, tuni tunaninta ya tafi wani wuri, sai ayyanawa take a ranta me kenan yake nufi? Yana nufin duk fad’i tashi da suka sha kafin su same shi ya tashi a banza?
Da kyar ta iya mi’kewa jikinta a matu’kar sanyaye, ta fita daga gidan, zuciyarta cike da tsanar matarsa, don ta san babu wanda zai lalata mata aiki sai ita.
Tun farkon ganinta da shi Allah ya jarrabi zuciyarta da son shi, musamman da taga yana da wadatar dukiya irin mijin dai da take fatan samu a rayuwarta.
Tayi iyakar ‘ko’karinta don ganin ta samu ya saurareta, amma sai ya nuna bashi da lokacinta, sole sai da ta sanar da mahaifiyarta maganarsa, aka yi mata aiki a kansa sannan ya kawo kansa gareta, kuma sai yanzu da take ganin burinta ya cika komai ya lalace? Gaskiya duk runtsi ba zata iya ha’kura da Hafiz ba.
Da kuka ta shiga gidan, Auntynta dake zaune a parlour da remote a hannunta, ta d’ago tana kallonta cikin mamakin dalilin kukanta, bayan lafiya ta fita daga gidan.
Tambayarta take abinda ya saka ta kuka. Cikin kuka ta bata amsa da cewa “komai ya lalace Aunty, yau Hafiz da bakinsa ya ke cewa shi bai san yadda akai ya fara soyayya da ni ba.”
Cikin mamaki ta ce “Hafiz d’inne ya fad’a miki haka?” Cikin shesshe’kar kuka ta ce wallahi haka ya ce, da nai masa maganar zuwa Maiduguri kuwa cewa yayi bai ga amfanin zuwa ba, tunda ya san ba aurena zai yi ba.”
“Lallai wannan Hafiz d’in sai munyi da gaske a kansa, yanzu Yana nufin duk abinda akai a kansa ya tashi a banza kenan?
Mari yanzu na kira Ummu na sanar da ita, son wannan ba maganar da za’ayi Sanya ba ce.”
Nan dai ta zauna tayi ta rarrashin ‘yar uwar ta da maganganu, tana nuna mata tunda ya riga ya shiga komarsu da farko yanzu ma al’amarinsa ba zai zo musu da wahala ba.
______________________________________________________
Shi kuwa Hafiz sai da ya tabbatar ta bar gidan sannan ya fito, Kai tsaye harabar gidan ya fita, ya nufi d’aya daga cikin motocinsa da ke fake ya shiga, ya tafi gidansu.
A d’akin da Halima take ciki ya zauna, ya ci abincin, duk da har lokacin babu wata jituwa a tsakaninsu, don Halima ta ‘ki bashi fuska tun bayan abinda ya faru a tsakaninsu, sai dai shi da kullum ya ke burin ganin ya shawo kanta sun dawo kamar da.
Ya dad’e a d’akin kafin ya bar gidan, zuwa sabgogin gabansa, har ya je ‘kofar d’akin ya dawo har zuwa inda Halima ke zaune, ya sunkuya ya ba ta hot kiss, suk yadda ta so ta goce ya ‘ki bada dama, sai da ya ga dama don kansa sannan ya bar ta ya fita fuskarsa d’auke da murmushi.
Ita kanta murmushi ta ke, don tasan zuwa yanzu ba zata iya rabuwa da Hafiz ba, duk abinda take, tana tauna tsakuwa ne, son aya ta ji tsoro.
A haka har su kai arba’in, zuwa lokacin Ahmad ya yi 6ul-6ul da shi, ga wayi Masha Allah, kamar yafi wata uku.
Washegari Umma ta ce su shirya ta je, ta yiwa su Mama kwana uku, daga nan sai su zagaya dangi, Hafiz kamar yayi me don takaici, son gaba d’aya ha’kurinsa ya ‘kare, ya gaji da zaman kad’aici.
Amma son ya san ko ya fad’i ra’ayinsa ba yarda Umma za tayi ba, dole ya ja bakinsa ya yi shiru.
Kamal ‘kaninsa ne ya kai Halima, gidan, bayan motar cike da tsaraba.
Tun da Aunty Saratu ta jiyo sallamar Halima ta fito da sauri d’ankwali a hannu, tana ‘ko’kari d’aurawa. Fuskarta d’auke da murmushi ta ce “A’a yau masu jego ne a gidan namu? In ce KK a gaji da 6oye mana mutuwar auren da zaman ro’kar surukai? Kai wallahi wasu dai mata suka rako, in ba haka ba yaya namiji zai saki mace ta koma gidan iyayenaa ta zauna, don dai tsabar rashin zuciya?”
Ko kallo ba ta ishi Halima ba ta shige d’akin Mama zuciyarta cike da d’okin ganin ta. Nan yara su kayi ta shigowa da tsara ar auna ajewa a ‘kofar d’akin Mama.
Kwananta uku a gidan kamar yadda aka bata umarni. Duk inda ya kamata ta je gidajen dangi ta zagaya sosai, ranar da ta cika kwana uku da yamma sai ga Kamal ya zo d’aukarta, haka ta shirya su kai sallama da Mama, ta fito ta tafi d’akin Abba shima su kai sallama da shi.
Ganin da gaske komawa za ta yi, ya sa Aunty Saratu kasa ha’kuri sai da ta nuna halinta, abinda ya sa Abba fitowa daga d’aki kenan ya tsawatar mata, amma da yake fitinanniya ce kamar zuga ta ya ke, har suka soma fad’i in fad’a a tsakaninsu, faga ‘karshe Abba ya yanka mata red card.
A washegari Halima ta koma gidanta, bayan Umma sunyi magana da Mama a waya, mutum biyu aka turo daga danginta d’aya 6angaren Mama, d’aya kuma 6angaren Abba.
Ranar Hafiz ya just dad’i sosai, sai rawar Kai ya ke, kamar tsohon da ya d’auki budurwa, ranar dai Halima ta d’and’ana kud’arta a hannusa, don sai da ya sauke mata gajiyarsa ta watanni.
_______________________________________________________