MAYE GURBI Complete Hausa Novel

*Bayan shekara biyar*
Wata mota ce ‘kirar Camry tayi parking a harabar gidan, da gudu wani kyakkyawar yaro d’an kimanin shekaru biyar ya fito Yana cewa Mummy oyoyo.
Hannu Halima ta bud’e bayan ta tsugunna, yaron na zuwa ya shige cikin jikinta Yana murnar dawowarta.
“Mummy Daddy ya dawo” ya fad’a cikin alamun yana murna da dawowar mahaifin nasa, hannunsa ta kama bayan ta mi’ke, suka nufi cikin gidan, Yana bata labarin tsarabar da ya kawo masa.
Suna shiga parlour’n ta tura shi d’akin iya Yalwa, tsohuwar da ke yi mata aiki. Da sallama ta shiga d’akin, baya ciki, sai dai motsin ruwa da ta jiyo daga toilet alamar wanka ya ke.
Bata zauna ba sai da ta fito masa da kayan Shan iska, wanda zai saka idan ya fito, don tasan ba zaibyi wahala ya sake fita in ba masallaci ba, don haka ya ke you idan yayi tafiya, don yau kwanansa biyar a Legos akan wasu kaya nasa da suka Sami matsala, sai yau d’in ya gama clearing komai.
Kitchen ta quce ta samar masa abinci mai sau’ki, a zuciyarta sai mita take na yadda yayi Mata zuwan bazata, bayan ko a yau sun yi waya da shi, amma bai ce Mata Yana hanya ba. Da ta san zai dawo da ba zata fita gun aiki ba.
Cikin lokaci kad’an ta gama had’a abincin, ta juye komai. ‘Dakinsa ta nufa da abincin jerw a kan tray.
Tana shiga d’akin ta samu ya fito har ya shirya, abinci ta gabatar masa, sai da ya ci ta ‘koshi, sannan ta tattare kwanukan zuwa kitchen, sannan ta dawo d’akin.
‘Korafi ta fara yi masa na yadda yayi mata bazata, sai yayi murmushi yace “nasan halinki, da na gaya miki yau zan dawo, ba Zaki huta ba, kinyi ta hidima kenan.”
Jararar Wasa tayi masa ta ce “aikuwa sai na rama.”
Tana ‘ko’karin zama ya ce “ina my Summy ne? Tun da na dawo gidan ban ganta ba, d’auko min ita in ganta.”
“Tana gidan Umma, tun safe da zan fita makaranta na niya ta can na ajje ta, sai dai zuwa anjima.”
Ido ya kashe yana murmushi ” ki ce yau ango nake kenan, babu ‘yar hana ruwa gudu a gidan.”
“Ai ‘yar uwata babu abinda za ta hana, dama Kai ko da yaushe ango nee kowane lokaci.”
Hannu ya bud’e Mata alamun ta zo, babu musu ta tshi faga inda take ta shige cikin jikinsa, suka rungume juna, cikin muryar rad’a ya ce “so nake a yau ‘yar uwanrki ta sami ‘kanwa ko ‘kani.”
“In dai ‘ya’ya naka ne ko nawa ne, bana shakkar haihuwarsu, karka manta hausawa sunce ribar soyayya aure, ni kuma na ce babbar ribar da ke cikin kowane aure shin haihuwar ‘ya’ya na gari.”
Murmushi yayi ya ce “Allah ya azurtamu da ‘ya’ya nagari.”
*Alhamdulillah*
[ad_2]