MAYE GURBI Complete Hausa Novel

“Aunty Halima ga wayarki ana kira” cewar Sumayya lokacin da ta ke mi’kawa Halima wayarta da ta bari ajje a d’ikinsu.
Tana gurin har ta gama amsa wayar da sannan ta dube ta tare da cewa “wai don Allah yanzu Aunty Halima ba za ki rabu da mutumin nan ba? Ni fa a ganina wallahi sam ba ku dace da juna ba.
Cikin murmushi ta ce Sumayya kenan, har yanzu da sauranki, ban san me ki ke hange ba, banga laifin Ibrahim ba, yana da asali, yana da sana’a, yana da ilimin addini da na zamani, ga kuma nutsuwa, me ake nema a gurin mijin aure bayan wannan?”
Ba wai na raina masa ba ne, kawai ni hankalina ya fi kwanciya da wannan mutumin da ki ka ta6a ba ni labarin had’uwarku, duk da ban san shi ba nasan zaku da ce da shi, musamman ganin yadda da kanki kika zauna kina bani labari a kansa, nasan ya kwanta miki a zuciya.”
Fuskarta d’auke da murmushin ‘karfin hali ta ce ” kin ta6a tunanin shi d’in idan ba mijina ba ne babu yadda za’a yi muyi aure da shi? Karki manta shifa mutum babu yadda za’ayi ya auri matar da ba tasa ba, kamar yadda mace ba ta isa auren mijin da ba nata ba.
Ki cire maganarsa daga zuciyarki, dama can Allah bai tsara akwai aure a tsakanina da shiba, shiyasa ma daga sau d’aya Allah bai sake had’amu ba.
Ki taya ni da addu’ar Allah ya bani miji nagari, shine ‘kaunar da zaki nuna min ‘yar uwata.”
“Insha Allahu” cewar Sumayya da ta ke ficewa daga d’akin.
Kamar yadda aka tsara ranar Alhamis akai walima a islamiyyar da su Sumayya su ke zuwa. Taron ya ‘kayatar sosai, anyi wa’azi mai ratsa zuciya, har zuwa lokacin da taron ya watse lafiya.
Washegari akai kamu, wanda aka kashewa kud’i sosai, kamar yadda uwar amarya ta ke buri, don ta nunawa duniya matsayin mijin da ‘yarta za ta aura.
*_Follow me on wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[9/29, 5:50 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na had’u*
Ranar asabar da misalin shad’aya na safe aka d’aura aure a masallacin juma’a na Unguwar, bisa sadaki mafi daraja. Yayin da mata su ke ta nasu shagalin bikin a cikin gida.
Su Halima yayyan amarya an zama busy, don ko wanka ba ta sami damar yi da wuri ba sai bayan da wasu mazan suka fara shigowa gidan, shaidar an gama d’aura aure.
Kusan rabin awa ta d’auka a band’akin kafin ta fito, jikinta sanye cikin hijabi akan zanin da ta d’aura.
Fitowarta ta yi dai-dai da shigowar ango da abokansa don gaida surukai.
Bata ankaraba ta ji idonta cikin na angon, wanda ya kasance miji ga ‘kanwarta, da sauri ta d’auke kai ta daina kallonsa.
Amma shi ya kasa d’auke fuskarsa daga saitin da take, wani irin kallo ya ke bin ta da shi mai cike da shau’ki, har ta shiga d’akin Mama don d’akinsu cike ya ke da ba’kin ‘yan biki.
Babu wanda ya kula da abinda ke faruwa sai abokinsa Mahmud da ke kusa da shi, shi ya dungure shi ta gefe, ganin ya na neman 6allo musu ruwa, kar ya yi abin kunya a gidan surukai, duk da yasan cewa mata ba su wani dame shi ba, amma kallon da ya ke bincta da shi akwai alamar tambaya.
Tun da su ka bar gidan Hafiz ya rasa walwalarsa, Mahmud na kula da shi, amma bai yi ma sa magana ba, ya bari sai da su ka koma gida.
Gefe guda ya kira shi, inda babu jama’a ya ke tambayarsa da ce wa “me ya sauya ka daga farin ciki zuwa damuwa? Kar ka manta yau rana ce ta farin ciki, kuma mai d’umbin tarihi a gare ka.”
“Na ganta, wallahi ita ce” kai tsaye ya bashi amsa a dun’kule ba tare da tunanin zai fahimci ko wacece ya ke magana akai ba.
“Ita ce wa?” Mahmud ya mayar masa da wata tambayar cikin mamakin furucinsa.
“Ka tuna yarinyar da na d’auki tsawon sama da shekara ina nema? Ya rinyar da tun daga had’uwar farko ta yiwa rayuwa ta 6atan dabo, na kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali a dalilinta, ita na gani yau a gidan su Sumayya, kuma tabbas ba zan iya ha’kura da ita ba, domin ita ce macen da zuciyata ta ke so da muradin rayuwa da ita.”
“Me ka ke son ka ce min ne Hafiz? Kar ka manta yau fa aka d’aura maka aure, kuma a gidansu amaryar ka had’u da ita, baka san wane irin matsayi ta ke da shi a gurin Sumayya ba, sannan ba ka da masaniya akan ko ita d’in matar wani ce. Ka yi ha’kuri ka rungumi ‘kaddara, wata’kila ita d’in ba alkhairi ba ce a gare ka shiyasa ta ku6uce ma ka, duk da tsantsar ‘kaunar da ka ke mata.
Don Allah kar ka sanya damuwa a zuciyar ka, bare har wasu su fahimci halin da ka ke ciki, shi rabon bawa ba ya ta6a su6uce ma sa, sai dai in dama can ba rabonsa ba ne.”
Haka dai Mahmud ya yi ta ‘ko’karin ganin ya kwantar na sa da hankali.
Ita kanta Halima ta ji wani abu na yawo a zucuyarta, da ganin da ta yiwa mijin ‘kanwarta ta, to amma ya za ta yi? Duk inda ta kai ga son sa ba ta isa ta canzawa kanta ‘kaddara ba, Allah ya riga ya ‘kaddara ba mijinta ba ne, dole ta yi ha’kuri.
Tayi ‘ko’kari sosai gurin ganin ta danne damuwar da ke ranta, don ba ‘karamin sonsa Allah ya jarrabe ta da shi ba. Tun bayan mutuwar Auwal ba ta sake had’uwa da mutumin da zuciyarta ke so kamar Hafiz ba, amma Allah ya yi ba mijinta ba ne.
Da haka ta daure aka ci gaba da shagalin biki da ita ba tare da kowa ya gane halin damuwar da ta ke ciki ba.
Tun misalin biyar na yamma motocin d’aukar amarya su ka zo, kasancewar ana son aje da wuri don shirin tafiya gurin dinner da za’a gudanar da misali karfe takwas na dare.
Sosai Halima ta so ta doje, ta ‘ki zuwa wurin dinner amma sai Sumayya ta dage, dole daga ‘karshe ta ha’kura ta je.
Ta yi kyau sosai cikin doguwar rigar less mai kalar sararin samaniya an yi masa kwalliya da zare kalar pink mai haske, d’inkin ya yi matu’kar kar6arta, sai ta yi amfani da pink d’in mayafi, jaka da takakminta ma duk kalar pink ne mai haske, don haka ba ‘karamin kyau ta yi ba.
Sau wajen biyar su na had’a ido da shi daga high table d’in da ya ke zaune, wannan ne ya sa, ta mi’ke kamar mai amsa waya ta fice daga gurin, kai tsaye waje ta nufa, cikin sa’a ta samu Adaidaita ta shiga, tai komarta gida.
Tun yana tunanin dawowarta har ya fahimci ba dawowa za ta yi ba, dole ya maida hankalinsa kan abubuwan da ake gudanarwa a gurin, duk da zuciyarsa cike ta ke da tunaninta.
Zuwa ‘karfe goma an gama, kowa ya koma inda ya fito. Yayinda duk wad’anda suka dawo gidan labarin irin had’uwar da dinner ta yi su ke, har zuwa lokacin da kowa ya kwanta barci.
Washegari ba’ki suka soma tattara shirginsu don komawa gida, zuwa yamma sai gidan ya zama babu kowa sai iya ‘yan gidan.
Karima ce kawai ba ta tafi ba. Bayan sallar la’asar ta le’ka d’akin Mama ta ke cewa Halima ta shirya za su je gidan amarya yanzu.
Har cikin zuciyarta ba ta son zuwa, amma sanin ba ta hujjar da za ta kare kanta in an tambayeta dalilin ‘kin zuwan ya sa ta shiryawa su ka tafi.
Basu wani dad’e sosai ba su ka isa gidan, sosai Sumayya ta yi farin cikin ganinsu, yayin da Halima ta ke ta addu’ar Allah ya sa kar su had’u da maigidan a cikin zuciyarta.
Sai dai bisa ga rashin sa’a bayan ta kawo musu ruwa da lemo sai ta nufi d’aki, ta cewa “bari na kirawo shi ku gaisa.”