MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Kamar ta jawo ta ta hana ta kiransa haka Halima ta ji. Kamar minti biyu sai gasu sun fito tare, tana gaba ya na bin ta a baya, har suka sami guri suka zauna.
Tun da suka fito idonsa na kan Halima, yayin da ita kuwa ta had’e fuska, ta ‘ki ko da kallon inda ya ke, don ba ta ga dalilin kallon da ya ke ma ta ba.
Cikin mutunci da girmama juna su ka gaisa, sai Sumayyan take gabatar ma sa da su a matsayin yayyanta. Har zuciyarsa bai ji dad’in kasancewar Halima sha’ki’kiyarta ba.
Sai yanzu ya fahimci duk yadda akai da gan-gan ta ‘ki yarda su had’u a baya, lokacin da Sumayya ta so ta had’a su su gaisa.
*_Follow me on wattpad_*
*_Commen_*
*_Vote_*
*_Share_*
[9/30, 6:54 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*WANNAN SHAFIN NAKU NE MASOYAN _MAYE GURBI_*
*_Adama Aliyu_*
*_A A S_*
*_Maman Noor_*
*_Maman Abulkhairi_*
*_Maman Yaseer_*
_ina jin dad’in comment d’inku, ina godiya Allah ya bar ‘kauna_
*Shafi na biyar*
Tun da ya koma cikin d’aki yake kwance, damuwa fal zuciyarsa, shi kansa bai san wane irin so ya ke mata ba, mai hana mutum sukuni da kwanciyar hankali.
Ranar da ciwon kai ya kwana saboda damuwa da ya sakawa zuciyarsa.
Ita kuwa har suka koma gida ba ta yi sakacin da wani zai fuskanci halin damuwar da ta ke ciki ba. A ranar itama Karima ta tattara yaranta ta koma gidanta, sai gidan ya sake d’ad’ewa ya zama shiru kamar ba’a yi taron biki ba.
Matsala ta farko da Halima ta fara fuskanta bayan bikin ita ce matsalar Sadiya, ta fuskanci ba ‘karamin raini yarinyar ta yi mata ba, duk da ba shiga sabgarta ta ke ba.
Ko tsinke ba zata d’auke a d’akin da sunan gyara ba, ga Halima kuma Allah ya yi ta da tsafta, sai ta zage ta gyara d’akin sai Sadiyan ta 6ata da gan-gan, don tsabar neman magana, amma sai ta rabu da ita, shiyasa wasu ranakun na girkin Mama ta fi zama a d’akin Maman, sai ta barta ta ci karenta babu babbaka.
Abin tsautsayi ranar wata lahadi kasancewar babu makaranta, Halima ta zauna ta yiwa d’akin na su kwalema, sai da ta ga ya yi yadda ta ke bu’kata sannan ta fito ta koma d’akin Mama don shima ta gyara.
Sai da ta gama aikin tas, sannan ta dawo d’akin da niyyar shirin wanka, abin mamaki sai ta sami d’akin kaca-kaca, kamar ba shine ta gama shan wahalar gyara shi ba d’azu, don rashin mutunci har da tu’kar rake zuzzube a d’akin.
Abinka da mai ha’kuri bai iya fushi ba, a fusace ta dubi Sadiya da ke zaune ta na jin wa’ka a waya, ta na wani karkad’a ‘kafa, ta ce “ke Sadiya wannan wane irin salon rashin mutunci ne? Ta yaya zan 6ata lokacin na gyara d’aki amma ki hargitsa min shi, duk iskanci da ki ke min fa ina sane da ke rabuwa na ke da ke……”
Cikin rashin kunya da izgili ta ce “Au rabuwa ki ke da ni? To wa ya nemi ki rabu da ni d’in, me zai hana ki d’auki mataki a kaina? Don kin yi kwantai kin rasa miji shine za ki huce haushi a kaina? To wallahi babu matar da ta isa ta takura min, yadda na ga dama haka zan yi……”
“Amma ba a nan gidan ba ko?” Ta ji an amsa ma ta daga bakin ‘kofar d’akin. Ko ba ta waiwaya ba ta san wannan muryar Baffa ce, don haka sai ta yi shiru ba ta tanka ba.
Itama Haliman ganin Baffa ya yi magana, sai ba ta ‘kara tankawa ba ta fice daga d’akin, don in ta zauna takaici zai iya sawa ta kaiwa Sadiyan duka, ko da ba ta shirya hakan ba.
Ran Baffa ya kai matu’ka gurin 6aci kan abunda ya ke faruwa a gidan na sa, wannan dalilin ne ya sa ya ‘kudurce a ransa wannan karon sai ya yiwa tufkar hanci.
Sai dare Baffa ya kira Aunty Saratu akan abinda ya faru. Sosai ya nuna ma ta 6acin ransa , kuma ya ce a gobe ya ke so Sadiya ta tattara ta bar ma sa gidansa, don wallahi ba zai yarda da wannan rashin mutuncin a gidansa ba, itama da ya ke ha’kuri da da ita don dai zamansa ta ke ne, babu yadda zai yi da ita.
Wannan magana ta tayar ma ta da hankali sosai, don ba ta zaci zai d’auki irin wannan matakin ba, da tun farko ba ta saka Sadiya a cikin maganar ba, gashi idan ya yi magana zai yi wuya ya canza.
Ha’kuri ta dinga bashi don ya ha’kura, amma ya rufe ido, ya ce idan Sadiya ba ta bar gidan ba to tabbas za su bar shi a tare. Dole ta baro d’akin cike da takaici da danasanin ingiza ta da ta ke, akan ta ci mutuncin Haliman.
Dole ba don zuciyarta ta so ba, washegari ta tattara Sadiyan ta kaita gidan Yayanta, ta yi masa bayanin ‘karya da gaskiya na abinda ya faru.
Bai mu sa ba akan zaman Sadiyan a gidansa ya kar6e ta, duk da bai yarda da bayananta ba. Wannan ne ya sa ya yi takakkiya takanas har gida, ya sami Malam Hamisu (wato Baffa) ya ji ta bakinsa akan abinda ya faru.
Shi kansa bai ji dad’in abinda ‘yar uwar ta sa ta aikata ba, kuma baiga laifin Baffa akan irin hukuncin da ya yanke ba, don a ganinsa yanzu ne zata san duk wanda ka ta6awa d’a ba dad’in hakan ya ke ji a zuciyarsa ba, sai dai ya yi maka kawaici, ya rabu da kai.
*TUSHEN LABARIN*
Asalin Malam Hamisu Haifaffen cikin garin Kano ne a unguwar Soron ‘Dinki. Su biyar iyayensu su ka haifa, biyu maza uku mata.
Yayansa mai Suna Musa ne babba sai shi, sai ‘kanwarsa Hajara, sai Asabe, da ‘karamarsu Saude. Dukkansu mahaifiyarsu d’aya.
Mahaifiyarsu mai suna Goggo, mace ce mai son ta haifi ‘ya’ya maza, don a ganinta duk wadda ta haifi ‘ya’ya maza ai ta zarce sa’a, wannan dalilin ne ya sa ba ta kara akan duk abinda ya shafi Musa da Hamisu tun su na ‘kanana.
Ta sha fita har ‘kofar gida don tare mu su fad’a gurin yara ‘yan uwansu, sai da mijinta mai suna Malam Bala ya nuna 6acin ransa, sannan aka sami lafiya.
Tun suna yara Hamisu mutum ne mai sanyin hali da ha’kuri, shiyasa uwar ta fi takaura ma sa, ba kamar Musa ba, da baya biye mata idan ta zo ma sa da maganar da bai gamsu da ita ba.
Auren soyayya suka yi da matarsa mai suna Rabi, ita kuma ‘yar Yakasai ce, suna zaman lafiya da fahimta juna.
Shekararsu d’aya da aure ta haifi d’anta na farko, ranar suna yaro ya ci suna Usman, bayan an yaye shi sai ta haifi Nura. Tun sannan Goggo ta fara ‘korafin wannan so ta ke ta gaje gidan, tun da ba ta da aiki sai haihuwar ‘ya’ya maza.
Lokacin ta yi haihuwa ta uku kuwa, ta haifi d’anta mai suna Adam, sosai Goggo ta tada hankalinta, wannan ne dalilin da ya sa ta tursasa shi ‘kara aure, wai kar Rabi ta mallake ma ta shi.
Duk da bai so ba, haka ta tursasa shi, ya auri ‘yar ‘kawarta wato Saratu, cikin lokaci ‘kan’kani akai biki, amarya ta tare a gidan mijinta.
Saratu mace mai fitinar tsiya, shiyasa tun da ta zo zaman kafiya ya yi ‘karanci a gidan, don ma Mama Rabi ba ta kula ta, a haka har Allah ya ba ta ciki.
Kusan tare su kai goyon cikin da Rabi, Allah cikin ikonsa wannan karon sai Allah ya bata haihuwar ‘ya mace.
Sosai ta yi murna da wannan ‘karuwa da ta samu, ranar suna yarinya ta ci suna *Halimatussa’adiyya*.
Tun daga irin murnar da Malam Hamisu ya nuna lokacin da aka haife ta, sai wannan ya dasa ‘kiyayyar yarinyar a zuciyar Saratu, ko d’aukar yarinyar ba ta ta6a yi ba.
Watan Halima hud’u itama ta haifi ‘yarta mace, mai suna Karimatu, ba ‘karamin haushi ta ji ba, don itama namiji ta so ta haifa sai Allah ya ba ta mace.