MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Haka aka ci gaba da cud’awa har zuwa lokacin da aka yaye su.
Kusan a tare suka ‘kara haihuwa, wannan karon ma Mama Rabi ce ta fara haihuwar d’a namiji, sai aka saka ma sa suna Yusuf, daga baya kuma itama saratu ta haifi ‘yarta mace wato Sumayya.
Tun da ta haihu kullum cikin neman fitina ta ke da Mama, Amma ba ta kula ta, sai ta rasa abokinyi.
Rannan Saude ‘kanwar Malam Hamisu ta je gidan, ta sa Mama ta yi ma ta shimfid’a a tsakar gida, saboda yanayin zafin da ake ciki, sakamakon gabatowar damuna.
Suna zaune su na hirarsu, sai Yusuf da ke rarrafe ya rarrafo zuwa gurin Saude, sai ta sa hannu ta d’auke shi ta na yi ma sa wasa, yaro ya dinga 6angala dariya.
Ai kuwa sai Saratu ta fara sakin maganganu, akan ana nuna banbanci akan yaran. Da farko Saude ta so ta fahimtar da ita, cewa babu wani banbanci, su duka abu d’aya ne a gurinta, amma da taga abin na ta babu arzi’ki sai ta biye ma ta sukai uwar watsi, abinda ya kai harda zagin iyaye a ciki.
Ai kuwa Saude ba ta bar gidan nan ba, sai da ta jira d’an uwanta ya dawo ta zayyana ma sa duk abinda ya faru.
Shi kansa ya so ya sasanta su, amma daga baya ya fuskanci rashin mutuncin saratu ya zarce tunaninsa.
Daga ‘karshe dai wannan ne ya yi sanadiyyar mutuwar auren Saratu.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Share_*
*_Vote_*
[10/1, 9:43 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na shida*
Hankalinta ya tashi sosai akan sakin da ya yi ma ta, don ba ta ta6a tunanin zai iya sakinta ba, ganin ta na da d’aurin gindi a gurin Goggo, amma sai ya shammace ta.
A gidan ta bar Karima ta tafi da iya Sumayya da ta ke goyo, sai Mama ta had’a ta da Halima ta ri’ke su babu banbanci.
Duk yadda Gaggo ta so ya maida Saratu gidansa abin ya gagara, musamman da ya samu d’aurin gindi daga mahaifinsa, dole ta ha’kura.
Tun daga lokacin bai sake sha’awar ‘kara aure ba, dama can shi ba mai son aure-aure ba ne.
Sosai Mama ta dage wurin kula da tarbiyyar yaranta, daga mazan har matan. Bayan Yusuf Mama ta sake haifar Salman, Jamilu sai auta Aliyu. Daga Halima Allah bai sake bata mace ba, sai dai lokacin da Aunty Saratu ta yaye Sumayya ta dawo da ita gidan, sai ta shiga cikin ‘yan uwanta
Tun su Halima na SS1 wani abokin Yayanta Usman mai suna Auwal ya nuna ya na sonta, da farko abin ya fara ne kamar wasa, suk inda ya ganta sai tsokane ta, daga baya kuma abin ya juya zuwa soyayya a tsakaninsu.
Bayan kammala secondary d’insu sai Baffa ya umarci ma su son su ita da karima da su fito, don Aurar da su zai yi, nan da nan kuwa kowane 6angare su ka fito.
Auwal da Halima sun so juna kamar ran su, Allah cikin ikonsa sai ya d’auke Auwal saura sati uku bikinsu sakamakon ciwon ciki.
Lokacin da labarin mutuwarsa ya iske ta sumewa ta yi, a gurin, kowa na gidan hankalinsa ya tashi don an san irin soyayyar da ke tsakaninsu.
An sha wahala da ita sosai kafin ta dawo daidai, don har akai bikin karima tana cikin d’imuwa, sai da akai ta yi mata addu’o’inta sannan ta dangana.
Tun bayan nan sai ya kasance babu saurayin da ta ke kulawa. Ganin yadda result d’inta ya yi kyau sai Baffa ya yi tunanin gara ta koma makaranta, ko hakan zai d’ebe ma ta kewa.
Cikin sa’a ba’a sha wahala sosai ba aka sama ma ta admission a Sa’adatu Rimi Collage of Education, cikin lokaci ‘kalilan aka yi ma ta registration aka gama, aka jira lokacin da za su fara d’aukar lacture.
Tun da ta fara karatun sai ya d’auke hankali, ya zama ba ta da lokacin tunani da shiga damuwa.
Ta maida hankali sosai akan karatunta, ba ta da lokacin sauraron wani d’a namiji da a
Sunan soyayya.
A haka lokaci ya yi ta tafiya har zuwa lokacin da su ka shiga NCE 2, sai ya kasance karatun ya ‘kara d’aukar zafi. A wannan tsakanin ne kuma Karimah ta haifi ‘yarta mace.
Cikin shekaru uku ta kammala karatunta cikin nasara. Sai dai har lokacin babu maganar aure a gabanta, don duk saurayin da ya zo da sunan ya na son ta, to zai zama kamar ya yi manta wani fami ne a zuciyarta.
Gani ta ke duk wanda ya zo bai kai Auwal ba, don Auwal mutum ne mai tarin ilimin addini da na zamani, gashi ya na da kyakkwawar mu’amala tsakaninsa da mutane.
Ba ta dad’e da kar6ar result ba ta sami aikin koyarwa, a wannan tsakanin ne kuma Baffa ya dawo da Aunty Saratu gidansa, bayan mutuwar mijin da ta aura bayan rabuwarsu, harda yaranta hud’u.
Duka maza ne sai Sadiya da ta kasance babbarsu, ita kad’ai ce mace. Don haka duk yaran sai dangin babansu su ka kar6e su, aka bar ma ta iya macen, shine ta dawo gidan da ita.
Wannan lokacin ma Goggo ce ta matsa, gashi kuma tuni Allah ya yiwa Malam Bala mailhaifinsa rasuwa, bare ya taimaka masa.
Tun lokacin da ta dawo ya fahimci babu abinda ya sauya daga halaiyarta, sai ya zamanto zaman ha’kuri kawai ya ke da ita.
________________________________________________
Tun da safe da Halima za ta tafi makaranta, Mama ta ba ta sa’ko ta kauwa Aunty Murja, wadda ta kasance ‘kanwa ce ga Maman.
Lokacin da aka tashi daga makaranta sai ta wuce aiken da Mama ta yi ma ta, duk da ba ta so ba, kasancewar ranar juma’a ce.
Bayan ta gama uzirin da ya kai ta, ta ce tafiya gida za ta yi, sai Aunty Murja ta ce “haba Halima, kamar wadda ta je wani ba’kon guri? Me zai hana ki zauna zuwa can yamma sai ki tafi.”
“Ki yi ha’uri Aunty, wallahi akwai abinda zan yi yanzun ne shiyasa, gashi Baffa bai san zan zo nan ba, bana so yayi fad’a.”
“Shikenan ki gaida yayan.” Cewar Aunty Murja.
Ta amsa mata da “insha Allahu za ta ji.”
Tana tsayawa a ba’kin titi kamar wadda ake jira wata Corolla XY ba’ka ‘kirin sai d’aukar ido ta ke, ta yi parking a gabanta, sai ta d’auke kai ta na ‘ko’karin matsawa daga gurin.
Cikin nutsuwa matu’kin motar ya fito, ya ‘karasa kusa da ita. Duk yadda yadda ta kai da iya shariya, sai da mutumin ya birge ta .
Cikin taushin murya ya ce “Assalamualaiki”
Ciki-ciki ta amsa sallamar kamar anyi mata dole.
“Don Allah baiwar Allah idan ba za ki damu ba in son ki bani number wayarki, don bai kamata na tsayar da ke a titi ba, sannan ga lokacin masallaci ya na ‘kara matsowa.”
Ba tare da tunanin komai ba ta karanto ma sa number ta shi kuma ya saka a cikin wayarsa, dai-dai lokacin da ta yi nasarar tsayar da adaidaita.
Bayan ta shiga ya le’ka tare da zaro naira gubu daga aljihunsa ya bawa mai adaidaitan, ya ce ma ta “sai kin ji kirana.”
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Share_*
*_Vote_*
[10/2, 8:44 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na bakwai*
Tun da ta koma gida tunanin mutumin ya ‘ki barin zuciyarta, har zuwa dare. Ita kad’ai za ka ga ta na murmushi, sannan duk lokacin da wayarta ta yi ‘kara da sauri ta ke d’auka, don ta na tsammanin kira daga gareshi. Tun Sumayya na sharewa har ta gaza ta ce “Aunty Halima wai don Allah wane abun farin ciki ne ya same ki a yau? Tun da kika dawo gidan nan kike murmushi ke kad’ai, ko dai mun samu Yaya ne?”