MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Kallonta ta ke fuskarta cike da murmushi, sannan ta ce “oh Sumayya yaushe kika koma sa min ido? Ashe duk wani motsina akan idonki ya ke.”
“A’a wallahi Aunty Halima, yanayinki na yau ne kawai ya banbanta da na ko yaushe, don na dad’e ban ganki cikin irin wannan yanayin ba.”
Labarin had’uwarta da mutumin d’azu ta kwashe ta fad’a ma ta, sannan ta ‘kara da cewa “tun lokacin da na rasa Yaya Auwal ban sake had’uwa da mutumin da ya kwanta min a zuciya irin wannan ba, duk da har yanzu ban tabbatar da manufarsa a kaina ba.
Abu d’aya na ke so da ke Sumayya, don Allah ki taya ni da addu’a, idan tarayyarmu da shi alkhairi ne Allah ya tabbatar, idan kuma babu alkhairi a cikin tarayyarmu Allah ya cire min shi daga zuciyata.”
Cikin d’oki Sumayya ta ce, don Allah Aunty Halima ya sunansa? Duk da ban ganshiba na san zai had’u, zan so ganin wannan me sa’ar da ya yi nasarar sace zuciyarki cikin ‘kan’kanin lokaci.”
Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ganin haka sai Sumayya ta ja bakinta ta yi shiru, don ta fahimci ba ta so aci gaba da maganar.
Cikin kwanakin kullun hankalinta na kan wayarta ko zai kira ta amma shiru, tun tana jiran kiransa har dai daga ‘karshe ta fitar da rai da samun kira daga gareshi.
Tabbas ta shiga damuwa don tun farkon ganinta da shi Allah ya jarrabe ta da wata irin ‘kaunarshi, sai dai sanin babu yadda za ta yi sai ta ba wa kan ta ha’kuri.
Shi kansa Baffa a lokacin babban burinsa Allah ya fito ma ta da miji nagari ya aurar da ita.
Ita kuwa Aunty Saratu sai ta sami abin gorantawa Halima da mahaifiyarta, don a ganinta Haliman ta rasa masoya ne, ba ta san ita ke ‘kin bada fuska ga duk wanda ya zo ma ta da magana da ta danganci soyayya ba.
Sumayya na gab da yin candy Allah ya had’a ta da Hafiz, cikin ‘kan’kanin lokaci sha’kuwa mai yawa ta shiga tsakaninsu, sai ya kasance kowane lokaci ba ta da magana sai tasa.
Babban abinda ya tayarwa Halima hankali shine, ranar da ya kawo wa Sumayya waya, bayan gama murnar samun wayarne Sumayya ta dinga shige-shige a ciki.
Tana shiga gallery ta ci karo da hotunansa da sukai matu’kar tafiya da hankalinta, don ba ‘karamin kyau hutunan su kai ba.
Cikin d’oki ta nunawa Halima hotunan, hankalinta ya tashi sosai da ganin mutumin da har yanzu ta kasa cire zuyarta daga kansa, a matsayin saurayin ‘kanwarta.
Bata bari Sumayya ta fuskanci halin da zuciyarta ta shiga ba, sai ta taya ta murna, da irin mijin da Allah ya bata.
Wannan ne dalilin da duk yadda Sumayya ta so su had’u su gaisa Haliman ta no’ke, don ba ta san abinda had’uwarsu da shi zai haifar ba, duk da zuwa yanzu ta tabbatar cewa ita kad’ai ta ke wahala akansa, shi tuni ya manta da ita a babin rayuwarsa.
Cikin lokaci ‘kan’kani iyaye su ka shiga cikin maganar, aka tsaida ranar auren bayan ta gama zana S.S.C.E d’inta da wata uku.
Kullum addu’ar Halima Allah ya musanya ma ta da mafi alkhairi a rayuwarta, don Hafiz kam ta tabbatar ba rabonta ba ne.
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[10/5, 6:55 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na takwas*
Lokacin da aka kawo lefen Sumayya, kuwa har Mama sai da ta dinga danne zuciyarta, don habaici ta dingayi sosai da yarda magana a tsakar gida.
A haka har akai biki, babu wanda ya kula ta, bare ta sami abokin yin fitina.
*Ci gaban labari*
Tun lokacin da Baffa ya kori Sadiya daga gidan, sai Aunty Saratu ta ‘kara tsanar Halima, amma don dole ta ke danne ‘kiyayyarta a zuciyarta, don tana gudun abinda nunawar zai haddasa ma ta.
Ita kuwa Halima tuni ta mi’ka al’amarinta ga ubangiji, ba ta da wata damuwa.
A shekarar ne kuma ta cike D.E form, don burin da ta ke da shi na komawa karatu, saboda ta sami degree, an so dai a sami matsala da Baffa, amma daga baya ya amince ma ta da al’kawarin idan ta sami miji dole ta bar karatun ta yi aure.
A wannan lokacin ne kuma Allah ya fito ma ta da manemi mai suna Anas, ba ta tsaya wani dogon tunani ba ta kar6i batunsa, tunda ta san wanda ta kewa tanadin kanta d’in zuwa yanzu ya fi ‘karfinta.
Ya so ya fito a lokacin, amma sai ta dakatar da shi, don ta na son su fahimci juna tukun, kuma ‘karin farin cikinta ya yi mata al’kawarin ba zai hana ta komawa karatunta ba.
__________________________________________________
Da farko Hafiz ya saka damuwa a zuciyarsa, amma yawan nasiha da Mahmud ya ke masa kowane lokaci ya sa ya saki zuciyarsa.
A kullum ya zauna tunani, ya kan d’auki kansa a matsayin mutum marar sa’a a duniya, don duk mutumin da mace kamar Halima ta ku6uce ma sa, to tabbas ta tabbatar marar rabo a duniya.
A haka Sumayya ta fara laulayin ciki, sai dai abu d’aya da ke damunta yanayin damuwa da kowane lokaci ta ke ganin mijinta a ciki, kuma ta tambayi dalili ya ‘ki sanar da ita.
A 6angaren soyayyar Halima da Anas ma babu wata matsala. Duk da ba ta jin sa har cikin zuciyarta, amma ta na ganin za ta iya aurensa kuma ta zauna da shi.
Shi kansa Baffa ya yi amanna da maganarsa, don tun farkon zuwansa, ya yi bincike akansa, kuma Alhamdulillahi, ba’a sami tawa matsala daga gare shi ba.
Tun da a kai bikin Sumayya sau uku Halima ta ta6a zuwa gidanta, Shima duk da dalili, don bayan zuwan da su kai da Karima sai duba ta da ta je yi har sau biyu, sakamakon laulayin ciki, da tai ta fama da shi.
Sau da yawa Sumayya na yiwa Halima ‘korafi akan ba ta son zuwa gidan ta, sai dai ta yi murmushi kawai ta ce mata “ke kanki ai kin san bai kamata ba, shikenan kullum sai a ganni a hanyar gidanki, don na zama babbar banza.”
Zuwa wannan lokacin cikin Sumayya ya kai watanni bakwai, amma har lokacin ta kasa fahimtar damuwar da mijinta ya ke ciki, don a kwanakin wata rashin lafiya da shi Hafiz d’in ya yi, abin ya ba ta tsoro, lokacin da su ka je asibiti likita ya tabbatar musu da cewa jininsa ne ya hau.
Musabbabin ciwon kuwa, ranar ya kai Sumayya gida kamar yadda ta bu’kata don gaida iyayenta. Tun da ya shiga layin gidan ya ji gabansa na fad’uwa, haka dai ya daure, har su ka ‘karasa ,’kofar gidan, bayan ya yi parking su ka fito daga motar, suka nufi cikin gidan, kamar yadda Baffa ya ba shi umarni da ya daina tsayawa daga waje idan ya zo, shima d’an gida ne.
Ya na sanya kai a zauren gidan idonsa ya sauka a kan Halima da ke zaune, ita da Anas, fuskarta d’auke da murmushi.
Da fara’a Anas ya mi’kawa Hafiz hannu da nufin su gaisa, amma ga mamakin sa sai ya share shi, ya yi wucewarsa wucewarsa ya bar shi tsaye da hannu a mi’ke, da ya mi’ka ma sa da nufin su yi musabiha.
Da ‘kyar ya iya ‘karasawa cikin gidan, don har duhu-duhu ya ke gani a idanunsa.
Bayan sun gaisa da matan gidan ya fita ya tafi, a nan ya sake wuce su, ba tare da ya sake ko da kallon inda suke zaune ba.
Tun da ya je gida ya kwanta kansa na yi masa matsanancin ciwo, daga ‘karshe sai ‘kaninsa Ja’afar ne ya d’auko sumayyan daga gida.
Zuwa washegari da abin ya yi tsanani, shine aka kai shi asibiti, bayan binciken likitoci aka tabbatar mu su da cewa jininsa ne ya yi mugun hawa.