HAUSA NOVELMAYE GURBI Complete Hausa Novel

MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Tun lokacin Sumayya ke kaffa-kaffa da duk abinda ta san zai iya 6ata masa rai, tun da ya ‘ki sanar da ita damuwarsa.

 

 

*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Share_*
*_Vote_*
[10/10, 8:37 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*

*_UMMU AISHA_*

*_Wattpad ummushatu_*

*Wannan naki ne ke kad’ai AUNTY HAUWA S. ZARIA*

*Shugaba da’ya tamkar da dubu, Allah ya ‘kara fahimtar juna a tsakaninmu*
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Shafi na tara*

Ranar da Sumayya ba za ta manta da ita ba a tarihin rayuwarta ita ce tanar wata talata, tun safe da ta tashi ba ta jin dad’in jikinta, saboda cikinta da ya tsufa a lokacin don ya kai wata takwas.

Ranar da kyar ta yi girki, saboda kar Hafiz ya dawo gida bai sami abinci ba. Bayan ta gama ta ajje masa a dining table, kamar yadda ta saba.

Tun da ta shiga d’aki ta kwanta ba ta ‘kara fitowa ba, har zuwa lokacin da ya dawo. Bayan ya yi wanka ne ya shiga gurinta don ganin a wane hali ta ke, musamman da ya ga yau da ya dawo bai samu taro daga gareta ba. Sai y la same ta zaune a gaban dressing mirror ta na shafa mai, da alama daga wanka ta fito, don zuwa lokacin ta d’an ji dad’in jikinta.

Bai wani zauna ba ya juya zuwa parlour don yunwa ya ke ji sosai, shiyasa ya ke so ya ci abinci.

Yana fita parlour Mahmud na shigowa, nan ya gayyace shi da su hau table don cin abinci a tare, babu gardama Mahmud ya amince su ka zauna a tare.

Yanayin cin abinsa kawai zai tabbatar maka da cewa kawai ya na cusa abincin ne, ba don ya na son cinsa ba, lura da hakan da Mahmud ya yi sai ya fara yi masa nasiha kamar haka ” haba Hafiz me ya sa har yanzu ba za ka fitar da maganar nan daga zuciyarka ba? Duk abinda kaga mutum ya so, idan ka ga Allah bai bashi ba to wata’kila abin nan ba alkhairi ba ne a gare shi.

Kai kanka ka san ba zai yiwu ka auri yarinyar nan ba, tun da ‘kanwarta ka ke aure. Ba zan so Sumayya ta san menene dalilin damuwarka ba, saboda akwai kunya idan ta ji akan yayarta ka ke shiga damuwa har haka.”

“Har yanzu ka kasa fahimta ta Mahmud, ni kaina ba zanvso na kasance cikin damuwa ba, sai dai babu yadda zanyi da ‘kaddara ta, Allah bai ‘kaddara aure tsakani na da Halima ba, amma har yanzu na rasa yadda zan yi da sonta da ya ke neman zamewa rayuwata barazana.

Ka taya ni da addu’a Allah ya cire min soyayyarta daga zuciya ta, ko don na samu damar kyautatawa Sumayya, nasan rabon aure ne babu a tsakaninmu shiyasa a wancan lokacin ta ku6uce min na rasa duk wata hanya da zan bi gurin samun had’uwa da ita.”

Duk maganar da suke a kunnen Sumayya ne, wadda ta yi saurin shiryawa don ta zo ta yi serving d’insa, sai dai bata kai ga ‘karasawa cikin parlour’n ba ta ji maganar da su ke tattaunawa a tsakaninsu.

Da farko mutuwar tsaye ta yi, ta kasa ko da ‘kwak’kwaran motsi, zuciyarta cike da mamakin abinnda ta ji, sai da ‘kyar ta iya motsawa ba tare da ta ‘karasa cikin parlour’n ba ta juya.

‘Daki ta koma cikin tashin hankali, zuciyarta cike da tunani, sai yanzu ta dinga tuno wasu abubuwa da ya kamata ta tsaya ta yi nazari a kansu tun a baya, amma ba ta yi ba.

Idan ba ta manta ba rana ta farko da ta nunawa Halima hoton Hafiz, ba za ta manta irin firgitar da ta ga ita Haliman ta yi ba.

Sai kuma yadda ta ringa kawo uzuri, a duk lokacin da ta bu’kaci had’a su da Hafiz d’in don su gaisa, bayan kuma kafin hakan ita da kanta ta ke da burin ganin lucky man d’in da ya sace zuciyar ‘kanwarta.

Tabbas biri yayi kama da mutum, amma me ya sa ta kasa fahimtar komai a baya, bayan tabbatuwar maganar aurenta da Hafiz ta sha yiwa Haliman maganar saurayin da ta ba ta labarin had’uwarsu, amma duk san da ta yi maganar sai dai ta yi murmushi ta ce “me yasa har yanzu ba ki manta da shi ba Sumayya? Jikina ya na ba ni shi d’in ba miji na ba ne, shiyasa ki ka ga har yau bai zo gareni ba, ki taya ni da addu’ar Allah ya canza min da mafi alkhairi.”

Wani hawaye ne ya gangaro a fuskar Sumayya, bayan ta gama tuna wannan maganar, cikin muryar kuka ta ce “me ya sa za ki yi min haka Aunty Halima, me ya sa ki ka bari na auri mutumin da ku ke tsananin son juna da shi? Yau na zama azzaluma, na zama katanga ga farin cikin ‘yar uwata, alhalin ita kuma kowane lokaci burinta ta gan ni cikin farin ciki.

Ganin lokacin sallar magriba ya yi sai ta tashi ta shiga toilet da niyyar d’aura alwala, dai-dai lokacin Hafiz ya shigo d’akin don duba ta sannan ya sanar da ita cewa zai fita, ganin tana cikin toilet kawai sai ya juya ba tare da ya yi magana ba.

Bayan ta idar da sallah ta dad’e a zaune a wurin, kamar ta kira Haliman ta ke ji, amma sai ta ga wannan ba maganar waya ba ce, sai ta ha’kura zuwa wayewar gari, gara ta nemi izinin zuwa gida, in ya so sai su yi maganar zai fi, don ta na ganin dole ta nunawa Halima rashin jin dad’inta akan wannan al’amarin.

 

 

*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[10/15, 6:14 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*

*_UMMU AISHA_*

*_Assalamu Alaikum_*

*_Ina bada ha’kuri sakamakon jinkiri da na ke gurin rubuta ci gaban wannan labari, hakan ya faru sakamakon wani uziri, amma insha Allahu komai ya kusa daidaita._*
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Shafi na goma*
Kamar yadda ta bu’kata, cikin ikon Allah bai hana ta ba, duk da tsufan da cikinta ya yi, da kansa ya kai ta, sai ya wuce office, akan idan ya dawo da yamma zai biya ya d’auke ta.

Lokacin da ta je gidan tuni Halima ta dad’e a makaranta wannan ne ya sa ba su had’u ba sai bayan azahar lokacin da Haliman ta dawo gidan, don ranar da wuri ta gama lactures, kasancewar tuni ta koma karatu.

Sai da ta ci abinci ta huta, don ta yi sallarta tun daga makaranta, sannan Sumayya ta tunkare ta da maganar da ta kawo ta gidan.

A zaune suke lokacin suna hira sai Sumayyan ta ce “Aunty Halima ban ji dad’in abinda ki kai min ba, ban san me ya sa ki ka bari na auri mutumin da ki ka san shine muradin zuciyarki ba.

Duk da ba ki fad’a min ba, zuwa yanzu na fahimci Hafiz shine mutumin da muka dad’e muna fatan bayyanarsa a baya, amma ki ka 6oye min hakan.

Idan baki sani ba kamar yadda ki ke jin sa a zuciyarki, shima haka ki ke a zuciyarsa ko ma fiye da hakan. A yanzu haka Hafiz ya na da hawan jini kuma son ki ne sanadi…..”

“Dakata Sumayya, wai wace irin magana ki ke ne? Ni fa ban fahimce ki ba. Mene ne tsakanina da mijinki da zai kamu da hawan jini sanadina? Bana son irin wannan maganar, idan kuma kin san cewa ba za ki daina ba zan fita in bar miki gidan gaba d’aya idan kin tafi na dawo.”

Duk yadda Sumayya ta so su fahimci juna Halima ‘ki tayi da gan-gan, don ba ta ga amfanin yin maganar ba a wannan lokacin, dole sumayyan ta ha’kura.

Sai wajen biyar na yamma Hafiz ya zo d’aukar Sumayya, duk yadda ya dinga baza ido ko zai ga Halima bai samu wannan damar ba, don tunda ta ji shigowarsa ta ‘ki fitowa daga d’aki har su ka nar gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button