MAYE GURBI Complete Hausa Novel

Da farko ta shiga damuwa akan al’amarin, sai da ta sami Karima da maganar, sai ta yi ‘ko’karin kwantar ma ta da hankali, musamman ganin yadda abin ya dame ta.
Ta nuna ma ta cewa Halima ‘yar uwa ce ta gari wadda za ta iya sadaukar da farin cikinta saboda farin cikin ‘yan uwanta, amma duk da haka fa tun farko Allah ne ya ‘kaddara ita ce matar Hafiz ba Halima ba, don haka ko da sun sake had’uwa dole sai wani akasi ya gifta wanda zai hana yiwuwar aurensu, dole ta ha’kura da maganar, masamman da ta fahimci babu abinda yin maganar zai jawo sai dai ya ‘kara musu damuwa daga ita har Haliman.
Haka ta ci gaba da rainon cikinta har zuwa lokcin da kowa ke sa ran haiwarta.
Duk wani tanadi da ya kamata su yi don tarbar haihuwar sunyi, ranar haihuwar kawai su ke jira.
Sau da yawa in sun yi waya da Halima ta na son su yi maganar Hafiz, amma sam Haliman ta ‘ki ba ta dama, saboda gani ta ke hakan sam bai kamata ba, sannan duk ranar da idanunta su ka yi tozali da Hafiz, ko akai ma ta maganarsa to cikin damuwa ta ke kwana. Ita kanta ta rasa wane irin jarabar so zuciyarta ta ke yiwa Hafiz d’in, da har yanzu ta kasa fitar da shi daga zuciyarta.
Ranar wata litinin Sumayya ta tashi da na’kuda, nan da nan su ka garzaya asibiti. Tun safe ake faman abu d’aya amma har zuwa biyar na yamma ba ta haihu ba, gashi ta wahala iyakar wahala, wannan dalilin ne ya sa likitan ya yanke shawarar yi ma ta CS.
Kafin a shiga da ita theatre room sai da ta nemi ganin Halima, cikin ikon Allah ta na asbitin, don tun da ta koma gida bayan barin makaranta tana samun labarin halin da Sumayya ta ke ciki ta tafi asibitin.
Tun da ta shiga d’akin ta ga halin da ‘yar uwarta ke ciki hankalinta ya ‘kara tashi. Da kyar ta d’ago hannu ta yiwa Haliman alamar ta zo inda ta ke.
Da sassarfa ta ‘karasa inda sumayyan ta ke kwance kan gado cikin mawuyacin hali, har an sauya ma ta kayan jikinta.
Cikin muryar da ke bayyanar da irin matsananin ciwon da ta ke ji ta ce “Aunty Halima, na ro’ke ki don Allah ki ro’kar min yafiya a gurin Mama da Aunty, ki ce su yafe min duk wani abu da nayi musu har Baffa.
Sanna don Allah ina neman alfarma a gareki da ki auri Hafiz, na tabbatar idan Hafiz bai same ki ba, ba zai ta6a samun farin ciki a cikin rayuwarsa ba.
Ke ce burinsa kuma ke ce farin cikinsa……”
“Haba Sumayya! Me ya sa zaki dinga irin wad’annan maganganun? Kar ki manta fa cuta ba mutuwa ba ce, insha Allahu zaki haihu lafiya, har ki aurar da abinda za ki haifa da hannunki…..”
Maganarta ta katse sakamakon tura godon da wata nurse ta fara, da sauri Halima ta biyo bayansu, har zuwa ‘kofar d’akin theater. Su na tsaye su na kallo aka shige da ita theater room aka rufo ‘kofar. Nan suka zauna jigun-jigun suna zaman jira, kowa zuciya fal da zullumi.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Shara_*
[10/17, 3:14 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na goma sha d’aya*
Cikin abinda bai fi kamar mintuna goma sha biyar da shigar da ita ba, ‘kofar d’akin ta bud’e, gaba d’ansu sai suka zabura zuwa gurin likitan da ya fito, nurse biye da shi daga baya.
Kallonsu ya ke cikin nutsuwa sannan ya ce “ina mijinta?”
“Gani” Hafiz da ke ‘karasowa gurin ya amsa, don tun da akai sallar la’asar ya na cikin masallacin asibitin bai fito ba, ya na zaman jiran tsammani. Ganin sam hankalinsa ya ‘ki kwanciya ne ya sa shi fitowa a lokacin don ya san halin da ake ciki.
Yanayin fuskar likitan kad’ai ta sa ya ‘kara sanyayar musu da jiki.
Wata nurse ce biye da shi, hannunta d’auke da jariri.
Cikin nutsuwa likitan ya fara yi musu bayani kamar haka “Allah cikin ikonsa kafin mu kai ga fara yi mata aiki ta haihu da kanta, sai dai babyn bai zo da rai ba…..”
“Ita wane hali ta ke ciki?” Halima da karimah su ka had’a baki wurin katse likitan daga bayanin da ya ke musu.
“Sai dai ha’kuri Allah ya kar6i rayuwarta bayan ta haihu.”
Yana gama fad’ar haka ya bar gurin cikin sauri.
Innnalillahi wa Inna ilaihirraji’un, ita ce kalmar da gaba d’ayansu su ke furtawa cikin tashin hankali.
Kafin wani dogon lokaci labarin mutuwar ya gama yad’uwa, zuwa kunnen duk wanda ya kamata ya ji.
Duk wanda ya bud’e baki ba zai fad’i sa6anin alkhairi akan Sumayya ba, saboda nagartattun halayenta.
Cikin kwankin har rashin lafiya Halima ta yi, saboda ba ‘karamar sha’kuwa ce tsakaninta da Sumayya ba, don tun farko sun fi shiri da ita akan Karimah, sabida sanyin halinsu ma d’aya ne, ita kuwa Karimah ba’a nuna ta da yatsa.
Zaman makokin kwana bakwai akai kamar yadda aka saba a al’ada.
Wannan mutuwar ba ‘karamin rud’a Aunty Saratu ta yi ba, don gaba d’aya ta yi laushi, sai ta koma wata abar tausayi.
Bayan sati uku Aunty Saratu ta shirya zuwa gidan Yayanta da son su tattauna game da wata shawara da ta yanke a zuciyarta.
Tun bayan rasuwar Sumayya zuciyarta ta kwad’aitu da son ganin ta bashi Auren Sadiya don ta *Maye Gurbin* ‘yar uwarta, don gudun kar suruki irin Hafiz ya ku6uce ma ta.
Cikin sa’a lokacin da ta je gidan ya na nan bai kai ga fita ko’ina ba, bayan sun gaisa da matansa ne ta shiga gurinsa.
Sai da ya gama saurararta ya ce “kina ganin ita Sadiyan da shi Hafiz d’in za su amince? Ina gudun kar a zo a sami matsala daga gurin d’aya a cikinsu, sannan su dangin uban yarinyar ki na ganin za su aurar da ita yanzu, alhali ko Secondary ba ta kai ga gamawa ba?”
Cikin ko’in kula ta ce “nasan Sadiya ba za ta ‘ki amincewa ba, kuma shima Hafiz ina ganin ai sai dai su gode mana, karka manta Sadiya ‘yar uwar Sumayya ce, in dai har zai so Sumayya ina ganin babu abinda zai hana shi son Sadiya.
Dangin mahaifinta kuma ba za su zama matsala ba, in dai an je musu da maganar na tabbata ba za su ‘ki aurar da ita ba.”
Sai da ya jinjina kai sannan ya ce “shikenan, yanzu gobe idan Allah ya kaimu zan samu lokaci na zo gurin Malam Hamisun, sai mu sami dangin mahaifinta da maganar, idan sun amince sai a sami su iyayen yaron da maganar.”
“Amma Yaya ina ganin ai wannan maganar ba ta shafi Malam ba, mutumin da ya kasa ri’ke yarinyar shine kuma yanzu za’a saka a cikin batun aurenta? Ni a gani na kawai ka rabu da shi, karma a saka shi a cikin maganar.”
Murmushi mai sauti ya yi sannan ya ce “banga ranar da za ki yi hankali ba Saratu, yanzu shi Malam Hamisun ne ki ke cewa ya kasa ri’ke miki ‘ya? Duk karar da ya yi miki ke da ‘yarki sai da ku ka ‘kure ha’kurinsa ya ce ta bar ma sa gida. Na tabbata bayan fitinarku ke da ‘yarki babu yadda za’a yi ya hana Sadiya zaman gidansa, kuma ko waye irin hukuncin da zai yanke kenan, ta yaya agola zai hana d’an gida sakewa.
Tun wuri ki gyara hakinki Saratu tun lokaci bai ‘kure miki ba, ki zo kina nadamar da ba ta da amfani.”
Nasiha ya yi Mata sosai don gyara zamantakewarta a gidan aurenta, sannan suka rabu.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[10/18, 12:55 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*