MAYE GURBI Complete Hausa Novel

*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Shafi na goma sha biyu*
Washegari da misalin tara da rabi na safe, wani yaro ya rangad’a sallama a tsakar gidan, Mama da ke ‘ko’karin shiga kitchen ta amsa masa, sai ya ce”ana sallama da maigidan nan a waje.”
‘Dakin Baffan ta shiga ta sanar da shi, sannan ta koma kitchen don yin abinda za ta yi a ciki.
Lokacin da ya fita ya sha mamakin ganin mahaifin Hafiz da ‘yan uwansa ne masu sallamar, nan da nan ya kar6e su cikin mutunci ya shigar da su d’akin Usman.
Cikin gidan ya koma ya d’ebo ruwa mai sanyi don ya kawo musu, dai-dai lokacin da fito Malam Yahaya yayan Saratu ya zo, bayan sun gaisa sai ya umarce shi da su shiga gurin ba’kin tare, don ya na ganin duk abinda ya shafi Sumayya shima ya shafe shi.
Haka kuwa aka yi, tare su ka shiga gurinsu, bayan gaishe-gaishe da tambayar lafiyar iyali Alhaji Hamza yayan mahaifin Hafiz ya gabatar da dalilin zuwansu “wato ba komai ne ya ke yafe da mu ba sai akan maganar Hafiz, a shekaranjiya ya je har gida ya same ni akan yana son mu zo mu nema masa auren ‘yar uwar matarsa da ta rasu mai suna Halima.
Har cikin zuciyar Malam Yahaya ya ji dad’in batun nan ashe hasashen Saratu ya zama gaskiya kenan.
Sai da Malam Hamisu ya nisa sannan ya ce “ban ‘ki maganarku ba, amma ita Halima gaba ta ke da Sumayya, ba kwa tunanin hakan zai janyo surutu a gurin mutane, a ce Yaya ya auri mijin ‘kanwarta? Kun san yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba, kai ba ka damu da rayuwar kowa ba, amma wani na nan ya saka maka ido.”
Alhaji Hamza ya ce “ni ina ganin wannan duk ba wata matsala ba ce idan an duba a mahanga ta addini babu wani aibu ga wannan auren. Sannan a kullum idan mutum ya ce surutun mutane zai biyewa to ba zai aikata abin alkhairi a rayuwarsa ba, gara duk abinda mutum zai yi ya ri’ke Allah.
Wannan auren fatan alkhari mu ke yi masa idan har ya tabbata. Mace ta gari ita ce burin kowane d’a namiji, kuma mun tabbar gidanka gidan tarbiyya ne, don tun daga lokacin da aka auro ‘yar uwarta babu wanda ya ta6a kuka da ita har ta koma ga mahaliccinta, wannan ne dalilin da ya sa ba muyi ‘kasa a gwiwa ba muka sake zuwa da ‘ko’kon barar mu.”
Cikin yanayin gamsuwa da bayaninsa Malam Hamisu ya ce ” ni yanzu ba ni da abin cewa, domin maganar auren Halima ba a hannuna ta ke ba, sai dai ku sami Yaya Musa da maganar, duk irin hukuncin da ya yanke dai-dai ne a gareni.”
Duk wannan bayanin da su ke Malam Yahaya na zaune ya na sauraronsu, tabbas dole ya godewa Allah da bai kai ga furta maganar da ta kawo shi ba. Shi kansa ya tabbatar idan Sadiya aka aurawa Hafiz tafiyar ba za tai nisa ba, saboda babu abinda ta bari daga halin rashin mutunci irin na uwarta.
Da farko da suka fara maganar ya d’auka ko ita su ake nufi tun da duk Sadiya ai Halima ce, amma daga baya sai ya fahimci ba akan ita Sadiyan suke magana ba.
Wannan ne dalilin da ya sa ya ja bakinsa ya yi shiru, ba tare da ya tofa tasa a cikin manar ba.
Sun yanke shawarar a lokacin za su je gidan Alhaji Musa su same shi da maganar.
Bayan barinsu gidan bisa jagorancin Baffa, Malam Yahaya bai shiga ko da gurin ‘yar uwarsa sun gaisa ba ya juya ya koma gida.
Shi kuwa Alhaji Musa cikin farin ciki ya amince da ‘kudurinsu, nan take ta kar6i kud’in aure da sadaki, kuma ya yanke ranar da za’a yi addu’ar arba’in d’in Sumayya a ranar za’a d’aura auren in ya so daga baya sai a yi biki amarya ta tare.
Sosai su kai farin cikin karamcin da aka nuna musu, haka su ka tafi gida suna son barka, da alfarin irin gidan da d’ansu ya nemo aure.
A ranar Sadiya ta je wajen mahaifiyarta, kamar yadda ta saba duk bayan d’an lokaci, sai da su ka ‘kule a d’aki uwar ta ke sanar da ita hukuncin da ta yanke a kanta.
Nan take Sadiya ta yi amanna da wannan maganar, don tana ganin babu macen da Allah zai bawa miji irin Hafiz ta ce ba ta so, don haka ta ke ganin ta zarce sa’a.
Daga ‘yar har uwar uwar ranar a cikin farin ciki suka yini, don gani suke kamar Hafiz d’in ya amince an yi an gama. (Ni kuwa na ce ashe in ku ka san halin da ake ciki da magana kenan, wai gwari ya tsinci wasi’ka).
____________________________________________________
Hafiz d’a ne ga Alhaji Mansur da Hajiya Mariya, shine d’a na fari a gurin iyayensa, sai ‘kannansa uku biyu maza d’aya mace.
Sun sami kyakkyawar tarbiyya daga gurin iyayensu, suna zaune a unguwar ‘Kofar Nasarawa.
Ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa degree a cikin garin Kano.
Mahaifinsa ba wani mai kud’i bane amma ya na da rufin asiri dai-dai gwar-gwado, don babu abinda suka nema su ka rasa.
Tun tashin Hafiz mutum ne mai ‘ko’karin neman na kansa, don bai yarda ya zauna komai sai an ba shi ba, wannan halin nasa ya ‘kara masa martaba a gurin iyayensa.
Cikin ikon Allah lokacin da Hafiz ya kammala karatun dagree d’insa babu d’ad’ewa ya mallaki shago a kasuwar kwari, bisa taimakon yayan mahaifinsa Alhaji Hamza.
Cikin lokaci ‘kalilan Allah ya sawa kasuwancinsa albarka.
A wannan tsakanin ne mahaifansa su ka matsa ma sa da maganar aure, don ganin yadda ya ke kama manyan kud’i bai kamata ya zauna haka babu aure ba, duk da sun yarda da tarbiyyar da su kai masa.
Amma shi har lokacin bai ga matar da ta yi dai-dai da ra’ayinsa ba, kullum su kai masa magana sai dai ya ba su ha’kuri.
Da farko mahaifiyarsa da suke kira da Ummie ta so ya Auri ‘yar ‘kanin mahaifinsa Baba Ali ganin yadda ta mutu a son sa, amma sai ya nuna ba shi da ra’ayin aurenta.
Shi kuwa Abbansu ya ce abar maganar baya son abinda zai lalata masa zumunci da ‘yan uwansa.
Babu d’ad’ewa Allah ya had’a shi da Halima a hanyarta ta dawowa daga gidan Aunty Murja bayan an taso daga makaranta, ta je kar6owa Mama sa’ko.
Saurin da ya ke na ya je gida ya shirya kar ya makara a sallar juma’a ya sa bai tsaya wata doguwar magana da ita ba, sai ya kar6i number wayarta akan zai kira ta.
Abin tsautsayi a ranar bayan ya dawo daga masallaci ya nemi wayarsa ya rasa, an sace ta a masallacin.
Ya shiga damuwa sosai da tunanin inda zai sake had’uwa da ita. Sai da ya kwashe wajen watanni biyu ya na zuwa inda su ka had’u ko Allah zai sa su sake had’uwa, amma ko mai kama da ita bai sake gani ba.
Duk wahalar da ya sha ta nemanta tare da Mahmud suka sha ta, dole daga ‘karshe suka ha’kura.
Takurawar da Umma ta yi akan maganar aurensa ne ya sa, ya fara tunanin mafita. Cikin ikon Allah sai suka had’u da Sumayya a kasuwa. Da tare za su tafi da Halima, amma sai Aunty Saratu ta tirsasa Suma tafiya ba tare da ta jira Haliman ba, don kwata-kwata ba ta son mu’amalarsu tare.
Ganin farko ya ji ta kwanta ma sa a zuciya, duk da bai ji soyayyarta ba, amma ya na ganin zai iya rayuwar aure da ita.
*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Share_*
*_Vote_*
[10/20, 6:14 PM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*
*_UMMU AISHA_*
*Wattpad ummushatu*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com