MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

*MIJIN ‘KWAILA* ����♀
sabon salo daga labarin *zahra adam ishaq*
“-chapter one-“
Ahankali yake tafiya da motar sakamakon yanda ya iske saitin bakin makarantar yaran yacika yakuma batse da dandazon yaran da’aka riga aka taso daga makaranta,ya d’anja gajeren tsoki lokaci guda yana kallon tsadadden agogon dake hannunshi ya taka burki kamar yanda sauran masu ababen hawa y’an uwanshi sukaja nasu burkin sakamakon dakatar dasu da yellow piper yayi.
Ranshi ‘kwarai yana a dagulene koda yake ba abin mamaki bane ganin fuskar tashi babu walwala kusan dukkan na tare dashi sunsan dahakan duk da yake mutum mayen barkwanci lokaci kankane yakoma kamar wani horror abin tsoro ga kowa saboda yanda yakecin magani kullum idanunshi suna manne da farin gilashi saboda yanda ya matsama idanun nashi da kuka wanda har yazuwa yau d’innan yakasa dena kukan,
Baya zato ko tunanin zaidena kukan rasa jigon rayuwarshi dayayi a cikin watanni shidda dasuka gabata.
Yazuwa wannan lokacin yazama abin tausayi ga kowa to ai dolene dukkan mai imani ya tausayama d’an sangirin saurayin maicike fal da ‘kuruciya akan fuskarshi da dukkan sassa na jikinshi,
Rashi yayi babba rashin dayake ganin bazai ta’ba samun tamka ko madadin taba.ZAHRA ADAM ISHAQ cikakkiyar budurwar dasuka sha’ku tun yarinta shine yaci kashinta da fitsarinta ya goyata a gadon bayanshi yamata soyayya dabai ta’ba yima wani mahalu’ki a duniya irintaba rana guda ciwon mara yayi fatali da rayuwar zahara yazuwa barzahu,
Adai dai lokacin da yarage saura kwana uku rak!
Daurin aurensu,
Yashiga rud’u mara misaltuwa dayawa yawa anzata ya haukace,amma dayake allah gafurune kuma rahimu saiya tashi kafad’unshi yakuma saka mashi dangana duk da ikirarinshi na dena kallon kowacce y’a mace da gashi tunda yarasa zahra.
Y’amma dayawa sunsha kawo kansu gareshi wasu iyayensu zasu kawo talla wasu text zasumai amma haryau baiga mai maye gurbin zahra ba,
Yashafi gefen fuskarshi daya tuna aneesa wacce tanace mashi kamar chewing gum saboda so,
D’iyar ‘kawar mummy ce,
Ya girgiza kai batare daya ankare ba.
Kamar ance dashi ya kalli gefen damarshi ya hangota cikin dandazon yara sa’anninta kamar sauran yara akwai uniform bulu da farin hijabi jikinta sai y’ar jakar makaranta saqale a hammatarta,
Wata mummunar fad’uwar gaba ta riskeshi lokaci guda ya cire gilashin fuskarshi yasake murza idanu gabanshi na bugun goma goma,
Dai dai lokacin data tsallako gefen dayake yara sun ragu sosai,
Tana tafe tana tsokanr yaran dake gefe da ita.
Caraf idanunta suka sar’ke cikin na ishaq wanda tuni anbasu hannu amma tsabar kallonta baimasan anbasu hannunba.
Tarin ababen hawa dasuke bayanshi suka addabeshi da horn hakan yasakashi waigawa da sauri, lokacin wani har yayi mashi overtaken yana fad’in “amma kai wawane,idan kallon mata kazoyi toka bamu hanya mu wucewa zamuyi “
Ishaq bai tankaba yagyara parking mota zuciyarshi kamar zata tsage saboda tashin hankali.
Ganin ita yaketa kallo yasata cewa da ‘kawayenta”ummilolo kukalli d’an ‘kauye yanata kallona kutsaya kuga yanda zanmashi gobe bazai sake kallonaba,ummana tace mai kallon mutane mayene.”
Saita lalla’ba kamar zata wuceshi sai dai tana zuwa saitinshi inda ya sauke glassa d’in motar ta tofa yawu, cikin sa’a kuwa ya sauka akan fuskarshi.
Sauran students y’an uwanta suka saki baki suna kallonta duk sun kasa tafiya,
Yayinda su ummilolo suka hau tsalke suna kyalkyala dariya.
Itama dariyar take don asukwane tabar wajen da gudu,
Tana zuwa tami’kama su ummilolo hannu suka tafa, kafin tacigaba dayima ishaq gwalo tanasaka hannayenta saitin kunnuwanta almar eho…ya numshe idanu yana tunano zahranshi a irin wannan lokacin tayi makamancin hakan gareshi, lallai batada maraba da zahra, hannu yasaka ya lakace miyon,ya sumbata zahra daban take, komai nata so yakeyi.
Bai ankareba ya hango zahra can kusa dawani matashi irin masu tallar agwaluma d’innan,
Ta mararaice fuska tace dame agwaluma “kai don Allah bani d’aya?
Me agwaluma cikin mamaki ya kalleta yace”kibada kud’i sai abaki agwaluma yammata.”
Sudai su ummilolo sun ‘kunshe baki sunason dariya suna tsoron bala’in zahra don sunsan akwai daru.
Ta murgud’a wa mai agwaluma baki,”nace kabani d’aya kawai.”
Me agwaluma ya fusata yace”tunda ubanki yabani jari meze hana inbaki d’aya.”
Tazaro idanu”la la la..kazagi ubana?
Me agwaluma yayi tsaki,
Aikafin ya ankare tuni ta duma wawa uku ta sura ta fece aguje da fad’in “pdp!!!”
Sauran yara dasuke tsaye sukace “wawaaaa!!!”
Tuni sun duma hannaye suna dumbuzar agwaluma,
Ganin yara sun kwashe agwaluma yasaka me agwaluma binta aguje bayan ya jefar da tiren dayazama empty.
Shegen gudu gareta ko barewa ta shafa mata lafiya,
Sauran yara sukad’au ihu “sai zahra !!sai zahra!!!!
Gaban ishaq dake kallon duk abinda yafaru yabuga da karfi.
Ya maimaita sunan ZAHRA???
��������
Aunty y’ar charas��
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN KWAILA* ����♀
chapter 2.
Gudu take kamar wacce zata tashi sama,
Ahaka tasha kwanar layinsu da yawa y’an unguwar sunsan halinta don haka suna ganinta suka fara dariya,
Wasu nafad’in “mai hali baya fasa halinsa zahra.”
Saida ta kutsa d’an sirdad’en lungunsu kana ta dakata da gudun tana luliya agwalumar abango dafad’in”luliya-luliya danya awakin baba da dad’i.”
Sai dai batayi auneba ta hango mai agwaluma a three thirty ya kutso lungun,
Hakan yasakata idasa fad’awa gidan kamar wacce aka cilla da kibiya .
Umma dake tsaye bakin band’aki da buta a hannu, zahra batamasan ta angije ummanba,ta danna d’akinta gami da gar’kama sakata.
Umma tabita da idanu,
Yayinda anty hafsat dake tsaye gefe tabita da tambayar lafiya zah….
Bata ‘karasaba sukaga me agwaluma ya fad’o gidan,
Baikobi takansuba yarufama zahra baya zuwa d’akin datake ciki.
Anty hafsa cikin mamaki ta tareshi dafad’in”lafiya malam bakada hankali zaka fad’o cikin gidan matan aure bako sallama.?”
Yayimata kallon banza ranshi yana zafi kafin yace”aiba sallama ta kawoniba,wlh sai anbiyani kud’ina kokuma in karya yarinyarcen,
Yanuna d’akin da zahra take ciki.
Yayinda take lekowa ta window tana mashi gwalo,
Yakuma ‘kufula,
Anty hafsat itama hararshi takeyi tana nuna mashi kofa”get out”
Ya kalleta da jan idanunshi”bansan wannan yaren ba.”
Anty hafsa itama akwai masifa don haka tamike dafad’a,
“nizakama rashin kunya,wato kashigo gari ka waye haryanzu jahilcin kauye bai sakekaba,idan laifi akamaka kai ataka basirar da wannan cin maganin dakakeyi zaka kwatarma kanka y’ancine,?
Tajuya a fusace ganin yanda yake harararta,yana mata qunquni.
“bari inkira police idan yaso idan kaje bayan kanta zakayi bayanin abinda yashigo dakai gidan matan aure.”
Umma tariketa tana fad’in”me yayi zafi hafsat,bansanki da hakaba,
Kifara tambayar abinda zahra tayimashi don bana raba d’aya biyu itace ta tsokanoshi..”
Umma tasake kwantar da murya tana tambayar me agwaluma abinda yafaru,
Idanunshi taf da hawaye, yake bama umma ba’asin yanda komai ya farun.
Umma tagyad’a kai tana fad’in”nasan za’a rina ai,
Nidai zahra bazan maki bakiba sai dai ince allah ya shiryeki,abinda kikeyi amma nagaji nagaji da halinki bari babanki yadawo a tattara amaidake can kauye inyaso kici gaba da halinki a can am.a nikam nagaji.”
Tajuya afusace tanufi d’akin da zahra tuni ta danna mashi sakata.