HAUSA NOVEL

MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zahra ta turo baki gaba saiga hawaye,umma tayi tsaki”kyaji dashi shagwa’babbiyar banza magana ba magana ba kin iya hawaye amma idan masifarki ta tashi zakice sam bakisan wani lamari waishi kuka ba.”

Zahra dai tayi gum,bata tankaba.

Anty murja ta kwad’a sallama suna tare da anty hafsat, umma tace “lale marhaban kamar kun had’a baki ga ‘bakin kano can ma sunxo,anty hafsa tace ai umma tunjiya mukasan dazuwan ta baba yayimana waya cewar yanason magana damu musameshi gida da yamma”.

Umma tari’ke baki”halin malam sai shi,nadaisan bazata wuce akan auren zahra bane,”

Duka suka kalli umma darashin fahimta dai dai lokacin da anty lubnah tafito daki ta rungume kannen nata”oyoyo my sisters yakuke.”

Sukam yaranta suka amshe suna cirawa sama,anty murja nacewa”gaskiya anty lubnah yarannan kara kyau kawai sukeyi kinga yara kamar wasu jinsin larabawa.”

Anty lubnah dariya take sosai”kedai murja bakya rabo da shirme “

Duk suka saka dariya,

Anty lubnah amsar hinan tayi daga wajen hafsat tana mata wasa duk suka shimfid’a tabarma waje saboda zafin garin.

Sai lokacin anty hafsa takula da zahrah wacce tayi kicin kicin darai kamar bata gansu ba.

Kamota tayi”oh my sister waya ta’bamun ke,halan umman muce ta bugeki?

Zahra ta idasa saka kuka hada turza kafafu akasa”ba anty lubnah bace taki sayoman alawar kano,kuma umma batayimata fad’a ba”

Anty lubnah dake zuge hand bag ta jefeta da alewar dake cikin ledar “amshi fitinanniya kada ki taramun makwabta.”

Zahra tasoma tsalle tana godiya,don duk abinta tasan ka kyautatamata tayi maka godiya.

Tashi sukayi suka kamama umma aikin gidan tas aka gama,lokaci guda umma tana d’an tsegun tamasu yanda zancen aurar da zahran yataso.

Duk sukayi shiru kowacce da abinda take sakawa acikin ranta,can dai hafsat tagaza ha’kuri tace anya umma kunyi tunani wajen yanke wannan d’anyen hukuncin?

Zahra haryanzu yarinya ce karama koma baga hakaba halinta yasha banban dana sauran yara sa’anninta gaskiya batada natsuwar daza’ayimata aure yanzu,sannan shi isha’q meyake nema jikin zahra dayake rawar jikin auren ta umma.”

Anty lubnah ta amshe”ato tunda sunyi alkawarin bazai kusanceta ba harsai takai munxalin hakan gud and fine,nadai san zaiyi *auren reno*ne,kuma atleast umma taji saukin bari-bari,nasan dr.ru’kayya inada labarinta asibitinta ‘kanwar abban ammar take aiki gaskiya matar so simple umma batada matsala sannan zansaka asake bincike akanta dama family dinta gaba daya,tunda akwai wadda tasanta.”

Umma ta gyad’a kai cike da gamsuwa”hakan yayi allah yamaku albarka”.

Duk suka amsabda amin,

Itadai anty murja bata tsinka ba,

[9/30, 2:08 PM] mum meenat: Tunaninta yafi karkata akan yanda zaiyiyu ace zahra za’ayima aure tab bazata mance abinda zahra ta’aikatama jamil d’inta ba,lokacin yana zuwa zance wajenta.

Tasauke numfashi dacewa”umma na tabbata isha’q dakanshi zai maido zahra gida batare da ansakashi ba,cox zahra tawuce dukkan tunanin mai tunani yarinyar nan bataji umma,saita sakama isha’q hawan jini watakila.”

Umma ta harareta”bakinki dai ya tsaya can,kidena mana wannan fatan cewa akayi zahran bazata kimtsu bane ta tabbata a mai wauta da masifa? Haba ku sakarma autata mara tayi fitsari mana.”

Anty lubnah takwashe da dariya tace “uhm..uhm..umma

,zahrafa karshe ce,gashi kiri kiri zahra ta hana abban ammar zuwa kaduna idan ba kwakwaran daliliba,”

Umma sai alokacin ta kwashe da dariya tana girgiza kai,”abar tada maganar data riga tawuce dai.”

Wuf anty hafsa tayi tace pls sister halan me zahran ta aikatama abban ammar ne,umma kam mikewa tayi tana murmushi”badani za’a maimaita wannan abun kunyar ba.”

Cikin dariya anty lubnah take basu labari”ina lokacin da’akayima ammar shayi(kaciya)duka suka ce eh” taci gaba,kunsan nan kaduna na dawo saboda shine d’an farina bansan yaya’akeyi ba,

Duk sun za’ku sukace munsani mana haba,

Anty lubnah taci gaba da kwasar dariya tana cewa”abban ammar yazo dubashi,ranar wata weekend,ga abbanmu zaune akan kujerar umma,itakuma umma tana bakin gado zaune nikuma ina kusa da abban ammar gefenshi yayinda zahra take zaune tajingina jikinta da nashi .

Shikenan sai bayan angama gaisawa sai abbanmu yakada baki yace”ammar an girma allah ya raya,

Abban ammar yana jin kunya ya’amsa da amin.

Nakira ammar na d’age mashi riga abbanshi yaga kaciyar,yace aikuwa ta warke Allah yakaro lafiya duka muka amsa da amin.

Zahra dake gefe saitayi caraf tace”aikuwa abban ammar baka ganiba kaciyarshi ta warke kuma tadena jini,

Yace mata nagani mana.

Saita sake kada baki tace dashi”abban ammar kaima anyima kaciya?,

Anty hafsat da murja suka kwashe da dariya sukace kai zahra batayi ba.

Anty lubnah tace,aimu dake zaune saimuka daskare awajen saboda kunya,

Shikuwa abban ammar kasa d’aga kanshi yayi saboda kunya,

Umma tanama zahra tsawa amma ina sake tambayarshi takeyi “kaji anmaka kaciya?

Cike da jin kunya yace mata”anyimun zahra.”

Zahra ta gyad’a kai cike da rashin yarda saikuma tace”me ‘karya”?

Abban ammar yabata amsa “d’an wuta,

Kanshi yana ‘kasa.

Abba dake zaune baisan sanda yakaima zahra dukaba,

Amma dayake batada wayo saitace “abbanmu naga kanata dukana menayi maka.?”

[9/30, 2:25 PM] mum meenat: Taci gaba da tambayar abban ammar”to kaciyar taka ta warke?”

Yad’aure fuska kamar zaiyi kuka yacemata “eh ta warke,”

Amma zahra bata ‘kyaleshi ba, saida tace “to indai da gaske kake ta warke bud’e ingani …..

Abban ammar tuni zufa tagama rufeshi,yari’ke hannayen zahra dake ‘kokarin kwance mashi zariyar wando,wai zataga kaciyarshi idan tawarke ,

Gaba d’aya dariya suke she’kawa,cikin dariya anty hafsa tace”thanks god,lokacin dana kawo nawa habibin zahra tana islamiyya thanks Allah”.

Anty lubnah tace kinsan Allah saida umma tazaneta sannan ta ‘kyaleshi amma duk da haka,saida tala’be abakin kofa tana cewa dama ashe ba’ayimashi kaciya ba yace anmashi .

Ke ranar baiyima su umma sallamaba,yasa kai baisake zuwa kaduna ba har yau.

Suma su umma ranar kamar zasu nutse don kunya.

Anty murja tace to itadai zahra watakila aljanunta nason ganin meke cikin jiki gareta,hakafa tayima jamil yazo wajena fira allah yasaka ba’agaban su umma bane,

Shida abokinshi na shimfid’a masu tabarma azaure tazo har zata wuce jamil yakirata irin ga ‘kanwar budurwa d’innan yace wai tazauna suyi fira.

Zahra tazauna kusa dashi tanata wasa da duwatsun hannayenta shikuma yana tsokanarta.

Can idanunta suka sauka akan abokin jamil wanda yasaka dogayen kaya,gashi riga ta tattare sai gaba d’aya halitar jikinshi ana ganinta.

Zahra ta lura don haka ta kalleshi lokaci guda takai hannunta idanunta waje alamar mamaki tace”yaya menene acikin wandon abokinka, ,

Gaba daya su anty lubnah suka saka salati,anty hafsa tace dama kince ‘kaniyarkice aciki ,

Murja tace “anty ina nake da bakin magana,wlh gida nashige nabarsu zaure suma suka sa’be babu shiri.

Har yau abokin baya iya hada idanu dani

**************

Bayan sati guda aka saka ranar auren zahra da isha’q watanni biyu masu zuwa…

Zahra itace mai raba minti,duk inda taje akace na menene saitace nice za’ayima aure,ummana tace kuzo mata biki……

[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����‍♀

BY MAMAN MEENAT

EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ) ��

ALHAMDULILLAHI ALA KULI HALIN

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button