MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Chapter 12.
Acikin kaf dangin umma dama na abba babu wanda baisan da maganar auren zahra ba,
Kowa mamaki yakeyi nayanda abba zai aurar da kankanuwar yarinya kamar zahra abun saikace a film kokuma a novels.
Maganganu kam umma da abba suna shansu amma dayake abba kaifi dayane saiya saka tsumma ya toshe kunneshi daga maganar mutane yariga ya’amsa cewar yabada zahra tokuwa bazai mayarda hannun agogo baya ba.
Wannan kenan..
Zaune take cikin office dinta,gabanta akwai tulin files na patient wanda take dubawa sai dai azahiri kallo daya zakama kawayar idanuwanta kagano tsintsar damuwar dake makale cikin dattijuwar fuskar tata.
Fara tattara files din gaban nata takeyi bayan tamanna dan glass din idanuwan nata,
Gafe guda tana makala hand bag dinta a hannu,
Jin kwankwasa kofa yasata dakatawa lokaci guda tazubama kofar idanuwa bayan umarnin shigowa data bayar.
Kyakyarwar macen tashigo itama kamar dr.ru’kayya sam babu uniform na asibiti jikinta,farace tas da ita,doguwa sosai tanada manyan idanuwa dakuma yalwar gashin kai.
“dr.aysheh “,
Dr.ru’kayya takira sunanta idanunta fes akan fuskarta,
Matar ta karaso bayan tasamu matsugunni a kujerar dake fuskantar ta dr.rukayya,
Atare suka sakarma juna murmushi kafin dr.aysha tafara gaida dr. Ru’kayya,
Duka suka danyi jumm suna duban juna,
Dr.aysha ta kawar da shirun dake tsakaninsu tahanyar tambayar dr.ru’kayya damuwar datake yawan gani kwance a fuskarta cikin kwanakinnan.
Numfashi dr.ru’kayya tasauke kafin tace”abokin kuka shi’ake gayama mutuwa aysherh hakika ina cikin damuwa dangane da aurennan da isha’q ya jajibo,anawa ganin kamata yayi isha’q ya natsu,yasamu macen dazata kwantar mashi da hankali amma zahra kam tayi kankanuwa dayawa a matsayin matar isha’q wanda yakeda akalla shekarun dasuka tayarma talatin.”
Saida tadan tsagaita dr. Aysherh tad’ora dafadin”nifa ru’kayya sainake ganin duka laifin abinnan yana akan wuyankine,bayag
a haka nisam banga dalili kokuma hujjar dazaki biyema isha’q akan aurennan ba,yaso zahra kuma yarasa zahra kamata yayi yahakura ga yammata dayawa dasuke kaunarshi kamar zasu mace akan soyayyarshi”.
Tad’an tsagaita tana kallon yanayin karbuwar maganar tata awajen aminiyar ta din.
Saikuma tadora dafadin”ga aneesa nan haryau takafe akan bazatayi aureba matukar ba isha’q tasamu matsayin mijiba,ni anawa ganin kobayan auren zahra mezai hana ki aura mashi macen dazata kawar mashi da kewa da zaman zullumi don gaskiya duk da banga zahra ba nasan ayanda kike kwatantawa karamace “,
Dr.ru’kayya tasauke numfashi dayin kankanen murmushi don sarai tagane inda zancen kawar tata ya dosa,”kigane bawai nahana isha’q ya nemi auren aneesa vane don bana kaunarta a’a saidon bashi damar zabin ranshi wanda tun ayanzu nake ganin wautata dakuma gangancina,bawai nafara tsanar zahra ko kiyayyartaba, saidai ina hango yanda isha’q dina zaizama *mijin raino*saiya raini mace karshe tazo ta bijirema soyayyarshi abinda yaketa damuna kenan.
Murmushi aysherh tayi dacewa”bazakiyi gaugawa ba ai,kamata yayi kibama auren nasu lokaci nakuma tabbatar dacewar zaki iya renarma isha’q mata ayanda kike mashi soyayya ta gasken gaske kiyita addu’a allah yasa hakab shine yafi alkairi.”
“Ameen”
Dr.ru’kayya ta amsa lokaci guda duka suka mi’ke suka fice daga office din suna sake maimaita matsalar dakuma hanyar maganceta.
: Farin ciki awajen isha’q tsayawa fasaltashi ma ‘bata lokacine,dukkan abokanshi na gida Nigeria dama na kasashen masu jajayen kunnuwa babu wanda baisan da zancen auren isha’q ba,
Sau tari idan yazauna yana labarin zahra saika rantse wata babbar budurwa ce,sai daikuma haryau a cikin abokan nashi babu wanda zaice ga fasali ko kammanin zahra.abu daya dasuka sani zahra ta isha’q ce.
…………………………………
Bayan sati biyu………
Shirye shirye gadan gadan gidansu umma sukeyi akan auren yar auta zahra wacce haryau a halinta babu abunda yasauya illa iyaka ace yama ‘karu don dai hali zanen dutsene,abba kwarai yayi rawar gani wajen bayarda tsabar kudi anty lubnah dasu anty hafsa suka gwangwaje amarya zahra da saitin furnitures y’an gaske masu kyau matuka,
Abba hatta da kayan kitchen da sauran tarkace saida yabayar asiya duk da umma tahana cewarta zahran aiba girki zatayiba,
Acikin wannan lokacinne dr.ru’kayya take sanarma umma cewar zasu kawo kayan lefen zahra,don haka umma tasanar ma abba dakuma yan uwa da abokan arzi’ki.
Mutanen unguwa kuwa da gayya sukayo runduna zuwa ganin lefen zahra don wasu suna zaton indai zahra ba mahaukaci zata auraba to lallai kauyene za’a aurar da ita,cewarsu wanne sakaran namijine zai auri zahra da sanin shi.
Dabara umma tayima zahra ranar daza’a kawo lefen tace da’ita taje gidan anty hafsa ta tayata aiki anty hafsa zataje unguwa.
Kamar abin arziki zahra ta shirya bayan tagama dafsa kwalliyarta taban mamaki,
Ahanya ta had’u da ummilolo tana d’ibar ruwan famfo.
Tun daga nesa ummilolo tafara wagema zahra baki dacewa “ahh amarya ansha kwalliya ina zakije?”
Zahra aka wani yi fari da idanuwa kafin tace”jekikai ruwan kizo ki rakani gidan anty hafsa”.
Ummilolo jiki har tsuma yakeyi taji zuwa gidan anty hafsa don tanason zuwa gidan kullum sukaje sai anty tabasu nama.
Don haka dasauri tashige gida tanacema zahra “jirani yanzu zan fito,”
Mintuna kadan kuwa saigata tasha tsaka tsami fuskarnan har shining take saboda Vaseline data sha,
Jerawa sukayi da zahra suna tafe sun labarin boko.zahra nagayamata yanda taci uban wata prefect dinsu jiya sunata kyalkyala dariya,
Sanda suka isa gidan anty hafsa tagama gyara gidan tsaf,tashirya zaman jiransu zahra kawai takeyi.
Da sallama suka shiga,zahra tuni tafara bude-buden fridge wai zatasha exotic saida anty hafsat ta wona zahra sannan tabar gidan tana sake jadadda masu akan kada suyi mata ‘barna.
Sundad’e zaune afalo suna kallo,kafin ummilolo tad’an yamutsa fuska dacewa”ni yunwama nakeji,dama banci abinci ba nataho”,
Zahra tami’ke tana binciken kitchen din anty hafsa amma bata samu abinci ba,coz ta’boye duka abincinta saboda tasan halin zahra.
Ganin babu yasaka zahra cewa”kawai kizo mu girka da kanmu,”
Ummilolo tad’an zaro idanuwa,saikuma tace”to”.
Fridge zahra tafara budewa dan’kare yake da nama dakuma kifi,hakan yasaka zahra kwaso uban nama tabama ummilolo wai ta soya masu ita bari ta d’ora shinkafa.
Haka kuwa akayi,
Zahra dake kokarin kunna gas tace da ummilolo”yarinya ki wanke namannan yafita tas naji ummana tanacewa nama ‘karnine dashi.”
Ba gardama ummilolo ta zuba uban ruwa acikin nama tasoma durza kamar tana wanke kayan sawa,saida ta tabbatar naman yacanja kala daga jaa zuwa fari ‘kal sannan tanunama zahra wadda tazuba mai yakusa kwalba acikin tukunya tanata banka mashi wuta,
Saida zahra ta sunsuna naman kafin tace”yawanku amma kid’an kara durzashi naji yana ‘karni ,
Ummilolo takuwa dage iyakar karfinta taci gaba da wankin nama.
Zahra bayan soyuwar man shinkafa ta dumbuzo batako wankeba ta afka cikin man…
Kuyi hqr nagaji yau
Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah ��
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN ‘KWAILA*����♀
*by maman meenat*
edited by Aisha T.fulani (umman faruq)
*wannan shafin cigiyane*
*inakuke my dada.aisha tasi’u yamel.kuna ina maman meenat na gaisheku.bilkisu gudaje ur page is here*��