HAUSA NOVEL

MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Chapter 13.

Ummilolo takuwa dage taci gaba da wankin nama saida naman yafara zaganyewa tsabar azabar dayasha,

Tajuyo da robar da naman yake ciki tana tambayar zahra “yayi haka?”

Zahra tagyad’a kai”yauwa ummilolo shiyasa kike burgeni wayo gareki kinfi uwande wayo.”

Ummilolo tahau washe baki zahra ta yabeta,

Tace”tome zanyi yanzu”,

Zahra dake juya shinkafa cikin mai tabata amsa”kitsiyayi mai kawai kici gaba da soyawa”.

Hakan ce kuwa takasance,ummilolo ta antaya uban mai a cikin kaskon tuya tawatsa naman ciki man baikoyi zafi ba,hakanan bata tafasa naman ba bare zancen su gishiri da magi da sauran tarkacen kamshi.

Zahra dake juya shinkafa saida ta tabbatar shinkafar tacanja kala daga light brown zuwa dark brown sannan tadebo tulin kayan miyan data jajjaga tawatsa ciki,taci gaba da soyawa tana bama ummilolo labarin “ina kallon yanda anty murja take soya shinkafa wai sunanshi ko frad race ne komenene oho mata,(fride rice)amma yanada dad’i irinshi zanmana. “

Ummilolo tagyd’a kai idanunta jajawur saboda yanda mai yake fantsalomata yana ‘konata amma takasa sanarma zahra saboda tsoron masifar zahran.

Saida kayan miyan da zahra take soyawa yafara sarqesu sannan ta antaya ruwa yashanye kan shinkafar gaba d’aya,

Takuma dunbuzo maggi star da already anty hafsa tadakeshi ta ajiye a mazubi mai kyau,xahra tazuba yafi cokali biyar wai yanda zasu sha dad’i.

Takoma akan gishiri shima batayi zubawar wasaba,hakanan curry tace dole ta zuba mai yawa yanda abincin zaiyi dadi na hakika.

Saida ta kammala tajuyo wajen ummilolo tana bata labarin”yarinya idan yayi dad’i har ummanmu zan d’iba nakaimawa,ance babu kyau kaci abu mai dad’i baka kaima mamanka ba.”

Ta tsaya cik da maganar sakamakon hango naman da ummilolo ke soyawa yakusa zama gawayi saboda tsabar baqin dayayi,

Wani wawan naushi ta sakarma ummilolo a baki,cikin rashin sa’a bakib ummilolo ya fashe sai jini.

Duk da haka zahra saida tarufeta da masifar”dalla can dubeki wawuya baki iya komaiba,kalli yanda kika qona naman,donkinga ba gidan y’an uwanku bane.”

Idanun ummilolo suna fitar da hawaye tace”tokuma saiki kama dukana”?

Zahra dayake tana ‘kaunar ummilolo saita rage murya”tokiyi hakuri nadena,mushirya.”

Tami’kama ummilolo yatsa suka sar’ke cikin na juna,

Saida suka gama girki zahra tazuba masu a plate,

Sai daifa loma guda ummilolo takai bakinta lokacin zahra taje d’ebo masu ruwa.

Da’kyar ta iya had’iyeta tsabar mai acikin mai take tsamo shinkafar gawani minahikin gishiri da masifaffen yaji,

Naman kuwa aiko dutse ya shafa mashi lafiya.

Zahra ta ‘karaso da sauri tana masifar”ummilolo kefa munafika ce,shine kika faraci tun kafin inzo ko?”

Ummilolo cewa tayi”Allah yabaki ha’kuri”,

Zahra tazauna tana hararta,

Lokaci guda takai yankan nama bakinta saidai duk iyakar hikimarta da kokarinta nama yace baisan zancen taunuwa ba.

Hakan yasakata furzar dashi babu shiri,lokaci guda tarufe ummilolo da ruwan masifa wai itace bata iya soya nama ba,

Itadai ummilolo tundaga lomar farko tatsame hannayenta tace ta koshi.

Zahra takai cokalin shinkafa a baki,cikin abinda baifi daqiqa gudaba ta furzar dashi a’kasa lokaci guda tana guntsar ruwa abakinta don jitayi yaji yana neman daskare mata halshe,

Idanu tawatsama ummilolo wadda dariya ke kokarin kwacemata tace”hegiya kece zaki cinyeshi aike kika saka na girka.”

Idanun ummilolo tuni sun kawo ruwa,tafara rokon zahra dakyar zahra tace “jeki samo almajirai kice suzo suda yawa.”

Ummilolo baki har kunne ta falla waje tana kiran almajirai,saikuwa gasu sun tasarma goma har suna turereniya,

Cikinsu babu wanda robarshi bata cika da abincin ba ga tulin nama kamar hauka.

Amma koda kyalla idanu sukaga mugun man dake yawo cikin shinkafar saida jikinsu yayi sanyi,

‘karshe a zaure suka zubar da abincin don tundaga lomar farko suka tabbatar masu girkin basuda lafiyar kwakwalwa.

Tiles din anty hafsa yasha mopping amma haka sukayi mata dama-dama dashi bacikin gidan ba hatta zauren saida suka la’anta karshe sukayita jifar su zahra.

…………………………………

Ankawo lefen zahra abin yabama kowa mamaki,amma kuma ba’abun mamaki bane duba da irin dukiyar da mahaifan isha’q suka tara dama shi kanshi isha’q din.

Saitin akwati shidda ne,sha’kare da kaya na burgewa duka mfi yawan kayan English wears ne,hadaddun tops gasunan lesuna da atamfofi dayawa duk an dinkasu,

Kai hatta da takalma size dinta aka kwaso,musamman mummy taje dubai tayoma zahra siyayyar,

Mutanen unguwafa sai mamaki suke da kayan lefen zahra,ahaka taro ya watse dangin mummy suna ganin ankwaso zahra diyar talakawa kuma karama sosai,saidai sun yaba da irin tarbar mutuncin da akayimasu.

Yan unguwa kuwa zuga guda sukayita zuwa kallon lefen zahra balbali zahra bala’i.

Zahra kam koda suka dawo gida taga kayan kasa dena kallonsu tayi,babu abinda yafi bata mamaki da umma tace mata wai duk natane………

real mum meenat.

[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����‍♀

BY MAMAN MEENAT

EDITED:AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ)

Muna tare daku masoyanmu, Allah yabar so sa qauna ��

Chapter 14.

Zahra ta gwada wasu daga cikin kayan yafi a ‘kirga musamman takalman sunyi mata kyau a idanunta harwani canja salon tafiya takeyi wai yanda zata dinga yimasu uwande yanga take gwadawa,

Tun umma na korarta harta gaji ta zura mata idanu.

Mata kuwa har dare basu dena sintiri gidan umma kallon lefe ba.

Kwanci tashi bawuya gamai tsawancin kwana,cikin juyawar lokaci dare yakan wanzu yabada safiya safiya tazama maraice maraice yakoma dare,

Acikin wannan juyin na lokaci Allah yakawo mu ranar da take d’aurin auren zahra.

Abun kamar yaune akafara zancen amma dayake komai baida wuya awajen Allah saigashi lokaci yayi,shiyasa bahaushe yake cewa komai akasama rana tozaizo,hakanne kuwa tabbas!.

Ango isha’q cikin d’anyar shaddar githzener dinkin boda wanda ya masifar fito da tarin baiwar kyau da kwarjinin da Allah yabashi,gefe guda yakwafa hula kalar shaddar jikinshi mayen turarenshi yana aikin fitar da ‘kamshin da’akoda yaushe yake manne jikinshi,

Akwai bakin takalmin Gucci akafarshi sai siririn glass dake kuma ‘kayatar da kyakyawar fuskar tashi,

Lokacin daya fito cikin gidan ta’ke yake da mata y’an uwa da abokan arziki,gefe guda mummy da tarin ‘kawayenta anata hada-hada da abincicika.

Ratsa mutanen yajeyi har yakai inda mummy take,yana zuwa ta bayanta ya rungumeta,turarenshi kadai ya shaidamata isha’q d’inta ne.

Juyo dashi tayi a hankali lokaci guda wasu siraran hawaye suka sauka akan fuskar isha’q dr.ru’kayya tasan me hakan yake nufi don haka tafara shafar sumar kanshi tana zuba mashi addu’ar fatan nasara dakuma dacewa akan auren nashi dayasa gaba.

Taron abokananshi duka suna waje suna jiran fitowar ango fuska kamar wanda akayima kyautar gonar auduga haka bakin isha’q yaki rufuwa,dayawa mutane suna mamakin yanda isha’q ya ‘kallafa rai akan mace haka soyayya mai zaifi yakeyima zahra so bana wasaba.

Dady ma yana tare da manyan abokananshi wanda sune zasu amshi auren isha’q,sai dai ya aliyu dabai samu zuwa ba,saboda yanayin aiki dayasha karfinshi.

Gidansu zahra kam shina cike yake da mutane anata girke-girke,zahra kam musamman anty lubnah ta gyareta cikin wata atamfa super atamfar jace mai manyan fulawowi dinki doguwar riga bubu tamatukar daukar zahra, musamman jan abu ga ba’ki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button