MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Basu saka mata relaxer aka ba,saidai sun gyare mata gashinta ya kwanta luf yasauka har akan gadon bayanta,duk yanda taso subarta tayi kwalliyarta sun hanata kwalliya maikyau suka tsara mata wanda tayi matu’kar fito da kyan zahran.
Gidan anty hauwa nan kusa da gidan su zahran nan zahra ta tara ‘kawayenta sunfi goma sha biyar..
Umma ce ta’aiko masu da abinci,zokaga yanda su ummilolo aka cakare da kayan sallah bikin babbar aminiya sukutum da guda.
Farko abun kamar abin arzi’ki zahra bata tokali kowa fad’a ba,
Saida lami tazo gidan ana cin abinci ana fira uwande ce tafara cewa”yauwa natuna ke lami bayan gulma da munafurci maiya kawoki gidanaanan bayan kince mun wai mamanku tace ko anyi auren zahra babu inda auren zaije tunda zahra batada hankali”?
Lami datakai lomar shinkafa abaki batasan sanda ta ‘kware ba,ta fiddo idanu waje dacewa”kai uwande Allah yatsine uwar mai ‘karya yaushe nace maki haka?”
Uwande wadda taci d’ammara tace”kada kimaida karuwa y’ar iska,ranar nan da aka aikeki shagon habu cheese zaki siyo maganin sauro da daddare konayi ‘karya”?
Ta’tambayi lami tana fiddo idanuwanta waje,
Lami takasa motsi duka jikinta yad’au rawa.
Zahra kam aituni tacire d’an kwali tayi d’ammara tafara turza ‘kafafu ‘kasa dacewa”aidama nasan babbar munafukace lami,kuma saikin gayamun gidan ubanda nazama mahaukaciya”.
Lami idanu suka kawo ruwa,amma dayake itama badaga bayaba wajen iya masifa tayi tamaza wajen cema zahra”gidan ubanki,kika zama mahaukaciyar kodan kinga nayi shiru,shiru shiru ba tsoro bane gudun maganane.”
Aitun kafin takai aya su ummilolo sunfara zuga zahra da ri’ke baki”yanzu ke lami zahran kike zagi?wlh zahra kici ubanta rigima uban wata kashe?”
Aiko zahra jiki har tsuma yakeyi ta bugi ‘kirjin lami,itama lamin takuwa dage iyakar karfinta ta mangaje zahra har saida kan zahra yabugi bango tafad’i ‘kasa.
D’agowar da zahra zatayi idanunta yasauka akan jamila tana mata dariya,
Aiko koda zahra ta d’auki lami saita sunkuta da ‘kasa,tahaye tana bugu iyakar karfinta.
Yara suna sake tura zahra,azabar duka yasaka lami cizon zahra a yatsa,aiko zahra kamar jira takeyi tafara naushin bakin lami iyakar karfinta cikin rashin sa’a hakorin lami ya fita baki yayita jini.
Koda zahra taga lami tari’kr baki tana ‘buratin kuka,sapita d’aga lami tace dawa Allah ya had’ata bada jamila ba?.
Kama jamila tayi da kokawa,rigima kica-kica aka yaga rigar zahra,abinda ya’kara fusatata ta ri’ke kitson jamila d’aya iyakar karfinta su ummilolo suna jan jamilan amma saida zahra ta fincikeshi fitt kitson ya fita.
Hakan yasaka jamila fashewa da kuka,ta kwashi kitso tayi gida tana kuka itada lami,
Gidansu jamila gidan yawane gasu masifaffu hakan yasaka sukayo zangi guda saigasu sunyo gidan anty hauwa,zasu bugi zahra.
Ganin hakan yasaka zahra ware iyakar karfinta ta angije jamila wadda ke maida ba’asin yanda akayi,waje tayi aguje yayinda sauran yara suka rufa mata baya…
Dai-dai lokacin da motar su isha’q ta iso kofar gidan,tare da manyan abokananshi,
Gefe guda waliyyan isha’q ne cikin fara qal ta shadda.
Zahra nazuwa batare datasan waye gabanta ba,tasaka iyakar karfinta danufin angije kowaye ya tare mata hanyar shigewa gida.
Idanun isha’q ya sauka akan nata idanun,cik tatsaya takasa motsawa bayan hakin datake ajiyewa.
Sauran yaran harsun iso wajen,sadi’q ya kalli isha’q yana tambayar wacece wannan kuma?”
Baikai ga tankawa ba,zahra tasake kwasa aguje tajuya don ganin hanyar gidan nasu a cunkushe.
Gudu sosai takeyi yayun jamila suna biye da’ita dai-dai zata tsallake titin mandawari cikin tsautsayi da baya wuce ranarshi wata ‘katuwar prado ce taxo wucewa sam idanun zahra a rufe suke,jikake ‘kuuuuu karar buge mutum da motar tayi kasantuwar itama motar a guje take….
Yayun jamila na ganin haka suka juya aguhe waidon kada ace sune,
Zahra kam babu alamar rai a tattare da ita,
Sai jini dake kwaranya akanta harzuwa bakinta da hancinta,akid’imen matashin dake driving motar yafito cikin tsananin tashin hankali ya sunkucin zahra…..
Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah
4 comments 09078902304
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����♀BY MAMAN MEENAT
EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ)
Wannan shafin naku ne yara manyan gobe Allah ya shirya mana ku baki daya meenat, saleem �� ismaeel, nasir, aliyu hydr zakin fama, my little haneef, umar farauq adon gari, fysal, little angel aisha
Chapter15.
Tsananin tashin hankalin ganin halin da zahran take ciki yasaka saurayin turata kujerar baya yabama motar wuta sosai yana gudu,addu’arshi d’aya kada yarinyar ta mace a hannunshi.
Wata tsadaddiyar private hospital yakaita,wanda anan suka yanki kati,nan likitansu yake muddin sukazo kasar shine yake kula dasu.
Dr.haisam siririn likita fari ‘kal dashi yanada sanqo akanshi,
Shine yafito da sauri don already saurayin daya kad’e zahra yakirashi awaya.
Da nosing guda biyu suka taho suna turo gadon da zai d’au zahra,
Yanda jini ke zuba yafi sake d’aga hankalin matashin.
Kasa natsuwa yayi musamman lokacin dayaga anshige da zahra emergency room saiyake ganin kamar bazata tashi ba,
Zagaye asibitin kawai yakeyi yana naushin iska,gami da furzo da zazzafar iska daga bakinshi yatambayi kanshi fiye da sau d’ari how coms hakan ta faru shikam ko kaza baita’ba kadewa ba barantana dan mutum.
Kusan 2hours yakasa natsuwa,saiyake danasanin zuwanshi kasar Nigeria yazo a rashin sa’a lallai.
Ganin dr.haisam yafito da sauri yasaka saurayin nufarshi idanu jajur yake tambayar “doctor yajikinta bana fatan tamutu sanadiyya ta doctor pls”…
Likitan yayi gaba yana bashi amsa”biyoni muje office dina ko?”
Bamusu yabi bayan likitan jikinshi duka a sabule yake,
Akujera mai fuskantar ta likitan ya zauna yana matsar yatsun hannayenshi d’aya bayan d’aya.
Yan rubuce-rubuce likitan yayi kafin yakai dubanshi akan sauran yakira sunanshi a tausashe” Aliyu ahmad(A.A).
Aliyu ya kafeshi da jajayen idanunshi da babu d’igon walwala acikinsu yabama likitan amsa”sunana kenan,likita sanar dani halinda patient dinnan take ciki kasani sarai banason jan time inabama lokacina muhimmanci fiye da komai”.
Gyad’a kai likitan yayi dacewa”hakane”.
Yasake numfasawa akaro na biyu”A.A bazan ‘boye maka halinda yarinyar nan take ciki ba,hakika tana cikin hali na tsaka mai wuya,babbar matsalar kantane yasamu matsala akwai yuwuwar kozata samu kanta lallai zatayi loosing memory nata.”
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un,abinda A’A yake maimaitawa kenan,
Saikuma ya marairaice fuska kamar ba A’A da dr.haisam yasani ba,A’a da magana ma ta fatar baki wahala take bashi amma yau shine yake zuba surutu yaga wahala na tunkaro shi.
Cigaba da magana A’a yayi”doctor pls babu wata hanya da yarinyar nan zata zama normal,banason wani abu ya faru da ita ta sanadiyyata.
Natureta da mota kuma ace tayi losing memory what’s wrong with me doctor”?
Dafashi dr.yayi dacewa”calm down my friend,wannan matsalar zamu iya solving nata ta hanya mafi sau’ki ammafa sai kabada hadin kai”.
Cikin za’kuwa A’a yace”komenene doctor zanyi kokari nidai kada yarinyar mutane ta salwanta dalilina “.
Likitan ya gyad’a kai”d only thing shine a fitar da yarinyar nan waje shine kawai hanyar da nake ganin zamu iya controlin din matsalar tun kafin ta mamaye kwakwalwarta,jinin dake zuba a kanta shine bamaso ya ta’ba kwakwalwa da yawa hakan zai’iya zama sanadiyyarta korasa hankalinta gaba d’aya,