MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

So kadaisan yanayin kasar tamu bawai bamuda kwararrun likitoci bane saidai likitocin dayawansu basuda lokacin patient dinsu.”
Aliyu yasauke numfashi,lokaci guda yana cewa”matsalar bazata wuce yanda zan gano ainahin iyayen yarinyar ba,amma zanyi kokarin bada cigiya duk inda ya kamata inyaso sai ayi komai akan idanunsu.”
Kallon mamaki dr.haisam yakema A’a kafin yace”abokina wannan matsalar fa bawai matsalace da zamu iya jan time akanta ba,matukar munason rayuqar yarinyar tofa dolene aga yau zuwa gobe ya kasance tana ‘kasar cairo don ganawa da kwararruwuce wannan lokacin tamkar rasa yarinyar ne.so d only way inaga kafara processing yanda zakabar kasar da’ita nikuma zanmaka dukkan wani shige da fice daya dace don ganin kasamu manyan likitocin in time.”
Mikewa A’a yayi jiki babu lakka,
Aranshi yana raya”kai tsautsayi baya wuce ranarshi,
Dakin da zahra take yashiga tana kwance tayi plat bazaka ta’ba gane kamaninta ba,matukar bakasan taba.
Kanta gaba d’aya ya kumbura fuskarta tayi suntum idanunta duka sunzama kananu saboda kumburin fuskarta impact dai kamaninta gaba daya bakace zahra bace.
A’a jiyayi wani mugun tausayin yarinyar yashigeshi,idan banda taimakon oxygen aibazaka taba yarda zahra tanada raiba,
To ba motsi ba motsawa gatananan kamar gawa haka take.
Dasauri yajuya yafice yabar dakin hankalinshi yakai kololuwar tashi,number mum dinshi yaketa try amma bata shiga sam.
………………………………
Isha’q ango anata fama da jama’a amma sam hankalinshi baya tare dashi,saiyake ganin kamar akwai wani abu personal dazai faru.
Yanadai cijewa ne kawai bayason yanunama fans nashi cewar yarinyar data kwasa a guje itace amaryarshi amma a time din jiyake kamar ya bita ya rungume kayanshi yahana koda quda sauka ajikinta.
Duk jama’a sungama hallara liman yafara haramar d’aura aure,lokacin da su ummilolo suka ‘karaso wajen a gujesuna kuka da majina sha’be-sha’be,isha’q yafara lura da hakan dasauri yayi wajensu yana tambayar abinda yake faruwa saboda yanda jikinshi yabashi akwai wani mummunan labari dazai riskeshi.
Cikin kuka ummilolo take sanar mashi”wani mai motane ya banke zahra kuma yatafi da i..”
Bata ‘karasa ba,isha’q yajuya da saurin gaske ya fad’a motar dasukazo da abokanshi yajata aguje zuciyarshi tana wasiwasin anya zahranshi ce”?
Ganin yanda yafice cikin taron jama’a a kidime shine dalilin dayasaka mutane farga suka fara tambayar abinda ke faruwa.
Itakuwa ummilolo tana mayar da martani cewa zahra ce mai mota yabuge yakuma saceta,
Lokacin da ummilolo take maganar abba yafito daga cikin gida yana sa’ba babbar riga tsayawa yayi cik kamar wanda aka dasa.
Gaba d’aya ma’aikatun kwakwalwarshi sun dakata da aiki na wucin gadi…
Juyawa yayi cikin gida hankali tashe,yana sanarma liman adakata da d’aura aurennan tukunna…
Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha ��
4 comments, 09078902304
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����♀
BY MAMAN MEENAT
EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ) ��
Kuna raina mmn Fysal, mmn Amna ina alfahari daku yn uwana
Chapter16.
Yanayin yanda mutane sukaga abba yashiga gidanne ya d’aga hankalin kowa,umma tana bakin gado a zaune abba ya aika kiranta.
Da sallama tashiga d’akin cikin abinda baishige minti gudaba tagano damuwar dake kan fuskar mijin nata,
Tambayarshi take cikin taushin murya:”abban zahra lafiya kuwa,meyake damunka”?
“bani ruwa tukun”
Cewar abba wanda yake kokarin tu’be malunmalun d’in dake jikinshi,
Ruwan randar abba umman ta mi’kamashi,ya kafa kai sosai yasha ruwan sida yafara karantama umma yarda daduk wata kaddara ta alkairi kota sharri kafin sanar da ita abinda ya faru da zahran.
Umma kam zuface tagama rufeta,tami’ke da sauri tana kai kawo atsakiyar d’akin sai alokacin ta’iya watsama abba tambayar”yanzu zahran tana inane”?
Shima mikewa yayi yana tafiya yana amsa mata”takamaimai banace ga inda take ba,amma zamu bincika asibitoci muga halin datake ciki.”
Umma da ilahirin jikinta yagama yin sanyi ta’amsa da “Allah dai yasa abin yazo da sauki”.
Ameen”
Abba yace yasakai yafice hankali tashe,
Tuni mutane suke tambayar umma ba’asin dake faruwa kowa yaji halin da’ake ciki saigaka jikinshi yayi sanyi.
Kai tsaye abba yafito waje yasamu kebewa da alhaji saifullahi yana sanar dashi abinda ke faruwa da zahra,abba yaci gaba dafad’in”anawa ganin kawai a dakata da d’aura aurennen harzuwa yanda hali yayi Allah yaga zuciyata banyi niyyar hana isha’q auren zahra ba.amma babu yanda na’iya da kaddara haka Allah ya nufa dole ce zata saka inhana isha’q auren zahra don bazan kaimashi wahala ba.”
Ya tsagaita idanuwansa jajur,
Alhaji saifullahi kallon abba yakeyi da matu’kar mamaki akan fuskarshi yace da abban”amma malam adamu kabani mamaki kwarai da gaske,yanzu don *wata jarabta*tasamu zahra har kake tunanin zan’iya hana isha’q zama da ita?
Tokasani koda mungoyi da bayan hana isha’q auren zahra isha’q bazai lamunta ba,shine yaga zahra yaga tamashi a hakanta yake sonta na tabbata isha’q yanama zahra soyayya ta gaskiya yanama zahra *so d’aya tak*son da babu kiyayya koda yaya zahra takoma,zahra ta isha’q ce abadan da’iman don haka matu’kar dai babu wani dalilin personal acikin ranka to kawai a d’aura aurennan inyaso zahra taci gaba da samun kulawa daga maman ta wato *dr.ru’kayya*.”
Abba ya gyd’a kai cike da gamsuwa,yana sake godiya ga Allah daya hada zahra da surukai na gari yanakuma fatan Allah ya tashi kafad’un zahra yabata ikon yima iyayen mijinta dama mjin shi kanshi biyayya.
Haka kuwa akayi take aka sanarma liman yakuwa dage ya tamke igiya uku ras tsakanin zahra da isha’q aurekam ya d’auru bisa sadaki mafi karanci don aure yafi albarka da karancin sadaki.
Umma tana cikin gida taji ana shafa fatiha sai lokacin wasu zafafan hawaye suka sauka akan kumatunta,wato dai shi tsautsayi baya wuce ranarshi.
Yanda isha’q ya kid’ime yasaka sadi’q binshi da mota yakara mashi motar yasha gaban isha’q duk suka fiffito daga cikin motar suna rokon isha’q yayi hakuri yabi komai a sannu,
Kasa motsawa yayi kamar wanda ya daskare haka yakejin jikinshi indai ba bayada rabon aure a duniya ba,mezaisa yarasa zahra akaron farko yad’auki dangana awannan karon yakuma sake rsa zahra?anya wannan kaddarar dake watangaliliya da rayuwwarshi kuwa.
Haka kawai yasakejin soyayyar zahra kamar ana ninka mashi ita,tabbas soyayya ba karya bace kuma amana ba wasa bace,
Abokanshi wajen biyar suka rufar mashi da rokon bude motar hakan ysakashi budewar kuwa,yanda yafito saika rantse yasha giyane saboda yanda jiri yake kwasarshi dakyar ya’iya furta”sad’iq zahra tazama tawa kokuwa ayauma nasake rasa zahra?”
Wani irin tausayin isha’q ya tsilga dukkan abokan nashi,
Dafa kafadarshi sadi’q yayi”haryanzu zahra adam ta isha’q ce,banga dalilin dazaisa afasa kulla auren da Allah yanufi saiya wanzu ba,isha’q bana tunanin akaf duniya akwai wanda yafi dacewa da zahra kamar ka.already zahra tana karkashin kulawarka isha’q”.
Wata ajiyar zuciya isha’q yasaki,sai lojacin yasamu kwarin gwuiwar shiga motar da su sadiq suke sauran abokan suka shiga motar isha’q sukayi gaba suna sake kwantar da hankalin isha’q din.
.
Duk tarin yawan mutane gidan baihana dr.ru’kayya ficewa dag gidan ba, sakamakon kiran gaugawa data samu daga dr.haisam akan wata yarinya dawani yakad’e wadda take bukatar agajin gaugawa inma da haki sunason saka hannun dr.ru’kayya wajen fitar da yarinyar zuwa kasar cairo.