MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Jin yanayin matsalar yasaka dr.ru’kayya zura fara kal ta rigarta gami da saka hijabi tafice dasauri tana barma dr.aysha sallahun cigaba dakula da bakinta kafin ta’iso.
Rafiyar mintuna ashirin tasadata da babbar asibitin,dakanta take driving abinda harta mance rabon datayi kenan.
Parking tayi inda aka tanada domin hakan,tafito dasauri dai-dai lokacin da A’a yake mikama dr.haisam hannu don tafiya wajen cukuiniyar visa.
Dakatar dashi dr.ru’kayya tayi,tana tambayar koshine yakad’e yarinyar?
Dr.haisam ya amsa “shine hajiya”
Tayi d’akin da aka kwantar da zahra,tura dakin tayi cike da kwarewa takutsa kai dakin idanunta suka sauka akan zahra wadda take kwance batare datasan waye akanta ba.
Dasauri dr.ru’kayya ta karasa tana dudduba fuskar zahra,lokaci guda ta shaida atamfar jikin zahra wadda itace dakanta tabada d’inki iri d’ayane dana hanan.
Saikuma y’ar siririyar sarkar gold mai kwad’on da’akama designed da harafin Z wato farkon sunan zahra tabbas zahrace to why meyasamu zahra garin yaya hakan ta kasance?
Bata tsaya ‘bata lojaci ba,ta fito a hanzarce tana shaidama dr.hisham yarinyarta ce ma ashe,yasha mamakin jin maganar don ayaranta babu wanda bai sani ba.
Sai dai basuda lokacin neman karin bayani ayanzu dasuke cikin hali na tunanin hanyar kubutar da rayuwar zahra daga halaka.
Kusan manyan likitoci hud’u suka nufi d’akin xahra da kayan gwaje2 don dr.ru’kayya tace sufara jaraba tasu sa’ar kafin ayi tunanin fitar da zahra kasar waje……
October 9,
Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah ��
4 comments 09078902304
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN ‘KWAILA*
_jinjina ga masoya lbrn mijin kwaila’gsky bnsan yama zan fasalta matsayinku awajena ba_ =luv yhu guys=��
editing aisha T.fulani.
*by maman meenat*
Chapter 17.
Cikin abinda baishige mintuna goma ba dr.ru’kayya tagama had’a kayan aikinta tare da kwararrun likitoci sundu’kufa akan zahra don gano ko tasamu matsalane a brain d’inta,
Abinda suka binciko shine yad’anso daga hankalin dr.ru’kayyan bawai matsalar zata shafi lafiyar zahra dun-dun-din bane,saidai hakan zai iya haifar da barazana ga lafiyar kwakwalwarta amma kuma muddin tana samun kula akwai tendencies na zata iya warkewa cikin kankanin lokaci.
Dukkan wani abu daya kamata likitocin suyima zahra sungama cikin ikon Allah kan natane kawai yasamu matsala ayanayin nasu binciken zata iya farkawa akowanne lokaci so abu d’aya dai dasuke ganin mafitane gareta shine idan tafarka tafara kallon abu mafi soyuwa agareta,wanda akowanne lokaci takeson kallo.
Saikuma abu na ‘karshe wanda takalla bawai kallo na razanarwa ba,watakila tahakanne zaisa ta’iya tunano abunda yafaru abaya,kenan bazata samu matsalar tunani ba.
Wannan kenan….
Isha’q kam dukkan bincikensu baikaisu ga gano ainahin inane zahra ta kurd’a ba,hakan yasaka shi kifa kanshi ajikin kujera zuciyarshi kamar zata tsage kirjinshi tafito don tashin hankali da damuwa,
Soyakeyi hawaye sufito daga idanunshi watakila zaisamu sassaucin tashin hankalin dayake ciki.
Abinda yafi daga hankalinshi baishige yanda zaisake rasa zahra akaro na biyu a rayuwarshi ba.
Yakira wayar mummy yafi a ‘kirga tana ringing sai dai babu amsa,sosai suka shigarda report wa police don binciko zahra.
Acan gidansu zahran ma hankalin duka atashe yake,kusan kowa zakaga babu natsuwa a tattare dashi,duk shirmen zahra a irin wannan halin datake ciki yakamata kowanne mai imani da hankali ya tausayamata.
Abba kam da aminanshi basu samu zamaba,bazama sukayi neman amarya zahra dafatan komai zaizamo cikin sauki da salama.
Sai wajen uku na yammacine motar dr.ru’kayya tayi fakin cikin harabar katon gidan nasu maicike da jama’a yan biki,dayawa sunamata sannu dazuwa dakuma tambayar maijiki takan amsa kawai sai dai babu natsuwa ko d’igo a tattare da ita.
Dakin dady tanufa da telephone din dake kan dan teburin tsakiyar dakin tasamu damar lalabo lambar dady wanda harzuwa lokacin yana fama da ba’ki,
Ganin kiran matarshi yasakashi kebewa gefe guda yana amsa sallamar datakeyi,
Cikin damuwa dr.ru’kayya takecewa dashi”abban hanan kana inane?”
Yabata amsa”inatare da ba’ki ince dai lafiya?”
Tad’anyi kokarin kauda damuwar dake tattare da’ita tace”kalalaboman number isha’q yanzu inason magana dashi ne”.
Dady yad’anyi jimm saikuma yace”akwai matsalane mummyn hanan,kidai bari in karaso gidan,don aurenma da har mahaifin yarinyar yace afashi kawai.”
Itama abinda takeson sanar dasu din kenan tawatso mashi tambayar”anfasa kokuwa ya’ake ciki?”
“and’aura mana,mezaisa afasa”.
Cikin raunanniyar murya tace”abban hanan matsala babba nahangowa isha’q,yanzu haka amaryar tana asibitina a kwance tasamu accident yuwuwar samun lafiyar kwakwalwarta shine abu mafi wahala,bana zato ko tsammanin cikin kankanin lokaci zata zama normal koda miliyan nawa aka barnatar don lafiyarta din,shikenan zamu zubama isha’q idanuwa yazama sakarai akan macene?inada tabbacin akwai zahra ko babu zahra isha’q dole zai iya rayuwa”
Tad’anyi jim tanason jin abinda maigidan nata zaiic Jin baitankaba yabata damar cigaba da maganarta”nikawai atawa shawarar a d’age bikinnan harzuwa lokacin da zahra zata samu lafiya,inyaso sai ayi auren shikuma isha’q yasakama zuciyarshi dangana tunda dama aurene kawai na jeka nayika bawani abu zai tsinta jikin yarinyar ba.”
Dady ya katseta dacewar”to naji naki batun idan shawarace ko umarni duka ina tayaki jimamin rashin samun karbuwarsu don yanzu haka anrigaya da andaure aure tsakanin zahra da isha’q,sannan koda cikin mafarki banzaci bakinki zai iyafurta wannan maganar ba,mutanen dasuka yimaki hallacci saboda batashi sukayi aurar da yarinyar suba,ganin kima da mutunci dakuma halinda isha’q ka’iya fad’awa yasaka suka aminta da aurar mana da ita amma kisani idan za’akai zahra turu ‘karewar hauka tofa bazamu dage dai-dai da second daya na biki ba.
Tunda har da lafiyarta iyayenta suka bashi ita,yakumace yaji yagani to lallai madamar ta warware zata tare d’akinta inyaso yayi jinyarta sannan banason nakuma jin bakinki akan maganar matsalar da isha’q zai shiga,idan yaro yadauki gatari rikemashi kota akeyi.”
Bai saurari mai zatace ba yadatse wayar,
Tafi minti uku tana kallon kan telephone dib dake hannunta kamar shine yake mata maganar,tagyad’a kai ita sam dady bai fahimci manufarta ba,idan soyayya ce bazai nunamata kaunar zahra ba amma abu daya dabazata dauka ba shine fadawar danta cikin wahala haka kawa.
Tana niyyar fitowa daga d’akin dr.aysherh tana kutso kai atare suka kalli juna,aysherh tafara magana”nadad’e ina sauraron shigowarki ga baqi sunata zuwa sai akace kina dakin dady bayan naga fitarshi tun dazu,ince dai lafiya?”
Tayi tambayar idanunta sunakan dr.rukayya,
Sauke ajiyar zuciya rukayya tayi dacewa”matsalar isha’q bansan har tsawon lokacin da zata dauka kafin warwarewar taba,”
Aysherh tace”sanar dani komai qawata,abokin kuka ba’a boyemashi mutuwa.”
“Hakane”
Dr.ru’kayya tafad’a lokaci guda tana warwarema aminiyar tata zare da abawa.
Wani mugun farin cikine ya ziyarci zuciyar asherh saitake ganin lokaci yayi dazata cilla kibiyarta wajen farauto ma tilon d’iyarta aneesa zuciyar isha’q wanda aneesan tayi matukar macewa akan kaunarshi.
Cikin kwarewa da hila dr.aysherh ta langwa’be kai dacewa”ayya gaskiya na tausayama zahra,sai dai kokusa isha’q yafi tsayamun araina yanda baligin mutum kamar isha’q zai tsaya a rayuwar kila wa kala don natabbatar matsalar zahra matsalace da take daukar lokaci kafin warakarta kobayaga haka abinda zaifi tayar da hankalina yanda kamalin mutum kamar isha’q wannan matsalar ka’iya kaishi ga aikata sabo na zina donshi ma lafiyayyene kamar kowa yanada feelings akan mace.sai dai na tabbatar matsalar zahra bazata ruguje komai ba Allah yabata lafiya “.