HAUSA NOVEL

MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

mikewa yayi saida ya rufe mata office din yanufo harabar asubitin,

akoridon dazai sadashi da farfajiyar asibitin yacikaro da aneesa wadda ta tsuke cikin riga da sket nawani jan material,

asamansu tad’ora siririn gyale kalar flowers din kayan.

fuskarnan with full make up.

bayaga katon sun-glass daya mamaye rqbin fuskar tata,

tun daga nesa kamshin turarenta yagama bud’e hancin ishaq.

kallo d’aya yamata yasake tsuke fuska,tatako tamkar tarwada yanda take kada jiki.

gilashin fuskarta tacire ta kafe ishaq da shu’uman idanunta datake wana maza dasu,ganin yasake hade rai yasakata sakin karamin smile tare da tare hanyar dayake kokarin ratsewa ya wuce.

karyar da wuya tayi,cikin salonta namatan dasuka kwankwadi karatun yahudu tace”hada ya ishaq don allah yanzu da gaske saika wuceni bako gaisuwa”?

yanda tayi maganar a shagwabene yasakashi kallonta.

sarqa idanunta tayi cikin nashi kafin tace”waito miyene laifine,kawai donnace inasonka?”: “haba ishaq,wlh inaji kamar bazan iya rayuwa ba idanna rasa ka.”

tayi shiru don tuni muryarta tafara rawa,

ganin bai tankaba yatsareta da gold eyes dinshi yakara sakar mata da jijiyoyin jiki.

jitake kamar takamashi da karfin tsiya tayi hugging nashi,duk idan ta kalleshi takanyi imagining yanda zatayi luf a faffadan kiejinshi.

“ishaq,”

takirashi dai-dai lokacin data rungume hannayenta akan kirjinta.

kallon daya batane yasakata hadiye miyau bata shiryaba.

idanunta suka kawo ruwa cikin taushin murya tace”don Allah na rokeka katsakurarmun koda kankanin gurbine axikin zuciyarka.nasan kasan menene so,babu bukatar saina fayyacemaka menake ji dangane dakai.sonka azuxiyata natabbata jarabane don nakasa samun matsayi daga gareka.

jiyayi tabashi tausayi,amma daya tuna zahra saiyaji sam bama zaifara kwatanta sonta dana wata ya mace ba.

ya runtse idanu lokacin dayake tunano kalaman late zahranshi’’ _ya ishaq kasani zahra takace kai kad’ai inason kaima ka’ajiye aranka cewar kai kadaine  na Azahra don banajin zan iya sharing dinka dakowace mace.ina tsananin kishinka yayanah_.

sauke ajiyar zuciya yayi,yad’ora da fadin”kiyi hakuri aneesa natabbatar kinada masoya da yawa kibama wani dama acikinsu.ni amatsayin kanwata na daukeki.”

kallonshi take kasa-kasa,acikin zuciyarta tana ayyana ishaq amatsayin mutum mara tausayi dakuma sanin darajar soyayya.

sam batayi auneba ta hangoshi ya wuce abinshi

bin bayanshi tayi da kallo;lokaci guda tajingina da vango don jirin datakeji yana barazanar kayar da ita.

juyawa tayi da sauri ta nufi ofis din aysherh wadda take zaune tana duba patients, cikin shagwaba da sangarta aneesa tafada ofiz din batare da tunani ko daukar izini ba.

bata damu da ganin mara lfyr da aysrh ke dubawa ba tafada kan cinyarta gami da sakin kuka me tsuma rai,harga Allah tanama ishaq so mai zafin gaske.

adaburce ayshen tagama duba mara lafiyan da bada iznin kada wanda yakuma shigowa tanada uzuri,

rungume aneesa tayi tanadan bubbuga bayanta ahankali tace”meyake faruwa ne baby?”

anee cikin muryar kuka take magana”haba mum sai yaushene zaki tabbatarma duniya cewa ishaq nawane? sai yaushene zaki nunama duniya cewar dani ishaq yafi dacewa, yaushene sunanshi na *mijin kwaila* zai dusashe yazamo mallakina”,pls.mum inajin kamar lokacin mutuwa tane yazo muddin narasa ishaq,bqna zaton sake farin ciki arayuwata madamar bana tare da ishaq mum pls help…”

kuka yaci karfinta takifa akan teburin ofis din tana tsiyayar da hawaye sosai.

dr.aysher tamike tasoma zagaye ofis din cike da tashin hankali;saqawa take tana warwarewa dolene tacikama anee burinta koda shine abuna karshe dazata aikata aduniya, kai koda duk abinda ta mallaka zai kare saita nunma dr.rukayya karshenta don tasan inda rukayya ta’amince da auren ishaq da anee toda bai isa ya bijire ba.

komawa tayi ta zauna ahankali gami da dafa kan diyar tata xike da rarrashi.

: zahra kam harta shiga mota tana waiwayen ta’inda ishaq zai bullo,

can ta hangoshi yana doso motar dasuke.

dasaurinta ta balle marfin tafita kaitsaye runguneshi tayi,tsayinta baikokai a kirjin ishaq ba.

cikin dariya take fadin”shine kaje  ka ‘boye ko? hmm damunyi tafiyarmu bazaka sakeee ganina ba.”

tafada tana sakarmashi murmyshi,

kama hannayenta yayu,yasaita tsawonshi danata tahanyar durkusawa yace”kalleni zahra”.

qura mashi idanu tayi batako kyafta ba.

ya sauke numfashi ahankali yace”i love yhu,i love yhu with all my hrt zahra, ican’t life without you zahra,”

zahra ta kwashe da dariyarta da fad’in “hu’umn,kainifa ban iya turanci ba.mudai anty dinmu tana mana karatun reader ne kawai,barima kaji a father and his son….”

bata karasa ba ishaq yasake matse hannayenta yace”zahra kiyimun alkawari zaki rayu dani rayuwa ta har abada.zaki kasance abarin damana aduk matsayin dana kasance bazaki gujeni ba?”

zahra kwalalo idanuwa tayi saikuma tama’ke kafada tace”amma inka yarda zaka dinga goyani yanda  ummana takeyimun da banida lafiya?”

tafada hadi da tafa hannayenta dakuma birkicesu tahada gaban hannun da bayan,yanda yara sukeyi idan abu ya kayatar dasu.

ishaq dariya tabashi ya lakace hancinta dafadin”zangoyaki abayana zahra,zanmaki dukkan abinda kike bukata dangane dani,zan maki koda wankane da wank….”

bai karasa ba zahra ta katseshi ta hanyar cewa”kuma zamu dinga hawa bene inka yarda,”

ya gyada kai.

“hardama kwamfutar wasa zan siya maki.”

yadai lura akan zahra babu komai sai tulin kuruxiya.

tsalle.tayi tadare bayanshi.

dai-dai lokaxinne anee da dr.ayaherh suka karaso wajen.

wani kallo aneesa ta watsama zahra mecike da zallar kishi da tsana….

*maman meenat*✍????

[10:36AM, 11/25/2017] maman meenat????: *MIJIN ‘KWAILA*????????‍♀

Chapter 22.

*written by maman meenat*

*edited aysha abdullahi* (umman faruq)

*Hakika kalaman baki basu isa furta matsayi da girman kimarki a idanuna ba,aysha umman faruq kedin ta dabance.matsayinki da kwazonki gareni hakika sune suka taka muhimmiyar rawa wajen bani kwarin gwuiwar himmatuwa akan rubuta wannan labarin,kin nunama maman meenat kaunar da bazata taba mantawa dake ba.Allah yaraya maki yaranki yaahirya su ubangiji yabarki da abban hyidar aci gaba da soyewa*

*wolla sister ina kaunarki,wujiga-wujiga*????????.

*Anty hajjaris mtn*

*Anty badiyya*

*kuna ina?, this page is dedicated for u sisters.tnks for ur luv and care am really appreciate.*????

wani kallo aneesa ta watsama zahra me cike da zallar kishi da tsana.

jitake kamar tamakure zahra don takaici,

kallo daya zaka mata ka tabbatar da ainahin abinda ke zuciyarta.

itadai umma ganin abinda zahra tayi yasata juya kaida sauri donkunyace ta rufeta.

dr.rukayya kam dariyq sosai take musamman ganin datayi damnata yashiga nishadi cikin kankanen lokaci.

hango dr. aysher datayine yasakata tsagaita dariya takarasa wajenta da sauri,kama hannun aneesa tayi wadda ke.kauda kai cikin daure fuska,duk da sanin da dr.rukayya tayi cewar tatsuniyar gizo bata wuce koki bai hanata sake tambayar aneesa damuwarta ba.

anee kam gani take dr.rukayya tama raina hankalinta don haka saita kauda kai gefe amma har lokacin tanajin zafin yanda zahra tawani dane bayan ishaq saitake ganin kamar da gayya.zahran ta aikata haka,itadai zahra ko ajikinta wai antsikari kakkausa.

dr.aysher da dabara tatake yatsun kafar anee dana hararta kasa-kasa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button