HAUSA NOVEL

MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Anty hafsa tazuge jakarta tafiddo da dubu d’aya tamikama mai agwalumar tana hararashi dafad’in”next time kasan yanda zakayi magana da nasama dakai “.

Shima hararta yayi,

Sai dai bai tankaba.

Anty hafsa tadafa kafad’ar umma wadda tazauna zugwui da damuwar da zahra ke sakata akoda yaushe,

Tace”umma pls banason ganin damuwarnan taki,kina sane da lalular dakike fama da ita,

Umma kamata yayi kinama zahra addu’a bawai yawan damuwaba.”

Umma tasauke numfashi”toyaya zanyi kinasaje da halin yarinyar nan,khatta da sunan da yaran unguwa suke kiranta dashi wai *zahra’u mala’ikar yara inkin mutu ba ruwan Allah walakiri ya jibgi kayanshi*.”

Umma taci gaba”sam idan kinga nasamu naji sa’ida to kuwa zahra tatafi makaranta toyanzu hatta da makarantar abin yaci tura iya shege kullum sabon salo take fiddowa,jiya Monday tafara zuwa makaranta js 1,take amma wai baifi wata biyu da shigartaba yara bakwai ta fasama kai da dutse,dacirema wata yarinya ha’kori,

Principal ta bugeta shine tatara yara bayan antashi makaranta sukayima motar principal ature,da ‘kasa har suka fasamata glass din mota.shine fa akazo hargida dakorarta sukayi dakyar babanku yasamu ya mayar da ita suka amsheta ,amna saida yabiya kudin duka asarar dasukayimata kinga ayau har ta dakko wata maganar.

[9/20, 1:16 PM] mum meenat: Anty hafsa ta sauke ajiyar zuciya,

“nidai umma sainake ganin kamar lamarin zahra fa akwai sa hannu wannan abin datakeyi bafa normal abu bane,gaskiya is abnormal ne umma yakamata mutashi tsaye,yarinya saikace ana kad’ata da ruwan hanji sam zahra bata d’auko halayyarmuba.”

Umma tace “kema kya fad’a ai,nida ace ba’a gida na haifi zahraba tozan iya rantsewa da Allah anyiman musayar tane batawa bace ba.gata sam bata d’auko kamanni dakuba,hakanan bata dauko halayyarkuba.

Ku shidda na gaifa allah ya dauki ran maza biyun dasuke cikinku sai kumata guda hud’u da allah yabarmun,duk na aurar daku ku ukku akan matakin karatun zamani dana addini dai dai gwargwado bamu tauyekuba,gakunan duka cikin rufin asiri amma zahra sam tazamo zakka acikinku,itabaga karatuba baga natsuwar ba,itakenan kamar tunkiya duk inda ta gifta sai ance kayya.”

Umma ta’kare maganarta kamar zata fashe da kuka.

Da’kyar anty hafsa ta shawo kan umma,ta lalla’bi zahra ta bud’e dakin tanufi kitchen tadauko abincinta wanda tuni ya sandare saboda hucewa,

Tazauna kamar wata saliha tanacin abincin anty hafsa namata fad’a akan rashin jinta.

Itadai bata tankaba,

Har lokacin sallar la’asar yayi tatashi tayi wanka akaja wata kwasheshiyar jagira wadda tasamu matsugunni a gefen kunne,

Tad’auko janbaki jajawur ta dafsa bayan ta zagaye bakin nata da tarin ba’kin kwalli.

Tajuya da fuska tanama madubi murmushi tana tsuke d’an matsakaicin bakinta aganinta ba nabiyunta wajen kyau.

Duk da tana cikin ‘kunci baihanata ganin kyawon nata ba

Sai dai aranta kullum tanajin haushin meyasa anty hafsa da anty salma kai harma da anty lubna duka suke farare tas,

Amma ita saitayo duhun fata,

Taja tsoki ita d’aya dafad’in”nadaisan dama ummanmu ba sona takeyiba shiyasa ta haifoni ba’ka.

Tasaka uniform na islamiyya check blue dasuka d’au guga sukayi luf dasu,

Tafito har lokacin umma bata dena fushi da itaba,

Takalli umman cikin kukawa tace”umma natafi,”

Umma tace”adawo lafiya sauran yauma akawomun ‘kararki kinyi fad’a dawani mutum zaki bani labari.”

Ta turo baki gaba,batare da tatankaba,

Umma tayi tsaki dafadin”shashasha kawai shekaru shabiyu amma fitinarki tafi ta masu shekaru ashirin.”

Itadai gaba tayi abinta kamar yanda tasaba,

Tafito lungunsu tana gunaguni,charaf idanunta suka sauka akan na ishaq wanda ya sar’ke hannayenshi a kan kirjinshi yakafe kofar lungun nasu da idanu,

Duk da rashin tsoro irinna zahra saida gabanta yafad’i,amma dayake tsiwa gareta saita murgud’a mashi baki dafad’in”kurwa

ta kur namana d’aci,me d’a yaci d’anshi mara d’a yaci ‘ko’kon tsuliyarshi.”

Ishaq duk da baya jiyo abinda take fad’i shidai komai takecewa ahakan burgeshi tayi,

Yanason d’an murgudennan nata,

Ya numshe idanu daya tuno da zahra gaf da bikinsu yakafeta da idanu tayimashi murgud’e dafad’in “kallonfa,

Alokacin murmushi yasaki yanace da ita”nanda wata biyu saina tsotse bakin murgud’enanna naki.”

Alokacin dariya tasaki dacewa”kai yaya ishaq,bakajin kunyata nifa kanwarkace”.

Ya runtse idanu,kamar zai fashe da kuka afili yafurta “i really luv yhu zahra,inason koda mace mai sunankine bare kuma mai kammani dake.”

Post everyday nsha Allah

September 20, 2017 at 7:31pm ·

         ��������

      by

Anty yar charas ����

[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN ‘KWAILA*����‍♀

*to you maman Aliyu this page is for you*��

Chapter 3.

‘karfe hudu na yamma dai dai lokacin da matashin ya cinna hancin motar tashi yazuwa cikin tanqamemen get d’in gidan,tare da matsa horn wanda yasaka megadin tashi da sassarfa yaxuwa bud’e katon get din.

Kamar almara ko mafarki haka baba yusha’u yake kallon fuskar ubangidan nashi dake cike da zallah nishad’i,

Yasake murza idanuwa aranshi yana ayyana’shin anma oga kyautar d’an mutum ne da kayanshi kome,?

Ganin yakasa aiwatar da aikinshi yasaka ishaq sake matsa horn da ‘karfin gaske wanda yasaka baba yusha’u tale get din yana washe hakora dafad’in”barka ubangidana barka dazuwa isyaku na zahra baban zahra kaga angon zahra’u…

Isha’q ya numshe sexy idanunshi lokaci guda yanajin wani yanayi yana tsalga ainahin ‘kasan zuciyarshi,

Ya’isada shigoda hancin motar lokacin daya saka hannu a aljihun jeans dinshi ya dumbuzo kud’in da bazai tantance adadinsuba ya dam’kasu ga baba yusha’u wanda tuni ya warcesu yana sake jinjinama isha’q d’in.

Yafito daga motar bayan ajiyeta a mahalinta,yana cilla key’s din motarshi sama yana cafewa a tattare dashi akwai zallah nishad’in daya kwashe watanni shidda gam batare dayayi makamancin hakan ba.

Yakutsa kai acikin ‘katon falon dayakai ma’kura wajen tsaruwa,dagani babu tambaya yasamu tagomashin dukiyarda tsayawa ‘kididdigeta ‘bata likacine.

Da sallama yashiga cikin falon idanunshi suka sauka akan ‘katon kyakyawan hoton zahra wanda tayishi alokacin datake saukowa daga cikin jirgi,ajikinta akwai ba’kar suit saitayi roling white gyale akan wuyanta harzuwa kanta.

Fuskarta akwai full make’up don ita gwanar kwalliyace abinda yake karama isha’q kaunarta don yanason mace y’ar gayu.

Tasaki silent smile dake ‘kayata fuskarta mai matsakaicin kyau.

Duk da ganin doctor ruqayya (wato mahaifiyarshi)

Baihanashi ‘karasawa ga hotonba yasaka yatsanshi guda ya xagaye gefen kumatunta dake murmushin,lokaci guda idanunshi suka canja kala,

Yajuya kamar zaifashe da kuka,muddin zaidinga kallon hoton zahra bazai ta’ba kallon wata d’iya mace da gashiba,

Face zahra mai kamanni da zahransa.

Yadad’e tsaye jikin hoton yanason tabbatarma kanshi banbancin dake tsakanin waccen zahra ‘karamar dakuma real zahramshi,amma yakasa gane koda abu d’aya dazai iya tabbatar mashi cewa bafa zahranshi ce takoma ‘kan’kanuwaba.

Doctor ruqayya tatako a hankali zuwa kusa da d’an nata tadafa bayanshi cikin sanyin jiki da’alamar tausayawa kamar yanda tasaba.

Sa’banin da ayau fuskarshi fayau take babu tarin damuwarnan dake ‘boye kyawon fuskar tashi.

Kama hannayenta yayi duka guda biyun idanunshi cikinnata duk da nata idanun suna manne da siririn farin glass din (medical).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button