HAUSA NOVEL

MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

daga bisani tasaki dariyar dabatakai ciki ba tana kallon rukayya”hm mummy kibar aneesa da rikici wai tana fushine na hanata zuwa abuja,nace tayi hakuri sainan gaba.”

tayi maganar tana sake kyaftama aneesa ido,

aneesa kam gefe ta harara gami da kwace hannunta cikinna dr.rukayya tayi gaba abinta.

zata iya barkewa da kuka muddin zataci gaba da kallon salon tacewar da ishaq yakeyi da zahra agaban idanunta.

azuciye tagifta ishaq wanda baimasan tanayi ba,hankalinshi nakan zahra dake zubamashi surutu.

dr.rukayya kam bayan anee tabi da kallo,saikuma tasauke ajiyar zuciya tana kallon dr.aysher da idonta yasauya kala don tausayin tilon diyarta da Allah ya jarabta da *son maso wani*

[11:50AM, 11/25/2017] maman meenat????: sauke ajiyar zuciya tayi,kafin tasakala hannunta cikinna rukayya tace”bazan sake maimaita kalmar rokona akan cewar ishaq ya auri aneesa agareki ba,amma zanyi kuka mai yawa dakuma rataya alhakin hakan akanki duk ranar da’akace yau gashi wata lalura takama aneesa akan son ishaq.

zankuma dora alhakin rasa aneesa akanki matukar tarasa ranta tadalilin ishaq.”

tasharce hawayen dayake fita idanunta tadora dafadin”natabbata duk nagartar dan adam yanada makusa rukayya,taki makusar itace babu abinda kike fifitawa fiye da kanki.

kinason kanki dayawa,kinkasa nunamun cewar aneesa diyace awajenki,farin cikin ishaq yafi rayuwar aneesa muhimmanci agareki.

tadan tsaigaita kafin tadora dafadin”kitaimakeni kitallafi rayuwar tilon diyata aneesa, bana burin rasata kamar yanda narasa yan’uwanta kinsan komai rukayya.”

tausayinta yacika zuciyar dr.rukayya tasake makale hannunta cikinna aysher tace”tursasa ishaq ya auri aneesa bashine zai kawo maslaha acikin lamarin ba.aneesa tasamu kwanciyar hankali agidan aurenta shine abu mafi girma daya kamata ki tunkara,bana zato ko tunanin idanna matsa ishaq ya auri aneesa tahakanne kawai zai kwantar da hankalinta.”

jaye hannunta aysher tayi tana fadin”kizauna kiyi tunani yazakiji da’ace iyayen zahra sun hana ishaq aurenta,?

wanne kunci zakiji acikin zuciyrki,?

ki kwatanta hakan akan kaina,na tabbata zaki gane menake nufi.”

tana kaiwa nan tayi gaba abinta batare datasake koda waiwayar inda dr.rukayya take ba,

mota tashiga inda aneesa take zaune takifa kai tsakanin cinyoyinta tana gunjin kuka,zafi sosai zuciyarta kemata.

watakila damarta ta karshe zatayi amfani da ita akan zahra,irin dai damar datayi amfani da ita akan late zahra.

tasauke ajiyar zuciya jin andafa bayanta kobata waigoba tasan kowacec;

dago jajayen idanunta tayi tadora akan fuskar mahaifiyar tata tace,”dole zan mai-maita abinda na aikata abaya mummy,duk da alkawarin danayi akan natuba bazan sake ba,amma kisani bazan yarda ingama niqa wata takwashen gari ba.

naso ishaq tunkafin insan menene so,

mezesa insake rasashi akaro na biyu?

bana zato ko tsammanin zan’iya hakan mum ican’t.”

tafada har lokacin idanunta basu bar zubar hawaye ba.

“bazamu sake maimaita kuskuren mu ba aneesa, cewar dr.aysherh.

“amma kisani damata takarshe da itane kawai zanyi amfani;.”

gyada kai anee tayi,lokaci guda tabi motar su zahra data giftasu da idanuwa,ahankali tasaki gajeren murmushin daya fito tare da guntun hawaye ita kadai tasan abinda ta kudurta acikin zuxiyarta.

       *****************

Kwanci tashi asarar me rai,ahaka muketa cinye lokacin mu,guzurin mu nadada ‘karewa yayinda tafiyar take dad’a nisa.

gaduk mai hankali idan yadubi yanda lokaci yake gangarawa yanzu zaigane lallai tabbas duniya tana gudu.

acikin murginawar lokacin muka tsinci kqnmu asati nabiyu cif da sallamo zahra daga asibiti,

abunfa saidai hamdala don zahra kam tayi natsuwar dole,to tadolece mana tunda umma tasakamata takunkumin bashiga ba fita.

akoda yaushe dai tana makale gida tana kamama umma wasu ayyukan gida.

duk da harga Allah jitake tamkar tana prison ne musamman idan tajiyo zazzakar muryar ummilolo tana rera wakensu dasukeyi idan za’ayi wasa”liyoooo y’an wargi liyoooo,ya wasan dare darana yake,ke uwande kizo muna kira,ke dije kizo muna kira,ke zahra kizo muna kira inkinqi kisha bugun jiya……”

ai tunkafin ummilolo tadasa aya jikin zahra zaifara kyarma,so dayawa takanyi attempting fita amma dataje zaure saitaga ansakama gidan sakata, wannan yasa tadena fita kwata-kwata takanjiyo su ummilolo suna buga gidan amma sai umma taleka ta wargadesu aguje zatajisu ridididi sun ruga.

akan zauna wani lokacin tamike kafafu tayita barza kuka,amma umma saitaba banza ajiyarta.

saukinta daya dayake ishaq koda yaushe yakan zo musamman idan yatashi aiki da wuri,wannan tasa tarage kewa don zaunawa yake yabiyemata suyita tafka shirme.

ahaka bakaramin sabo tayi dashi ba.

itama umma sosai take nata bakin kokarin wajen jawo zahra ajiki tanakara nuna mata abinda yadace dakuma yimata nasiha musamman akan yawan jarabar fadanta.

todai kusan nasihar umma zamuce wata tana samun shiga watakan tanabi tanan????????tafita tanan din dai????????????…

Kwana biyu da dawowar alhj saifullahi mahaifin ishaq daga cairo ya tuntubi rukkayya da maganar tarewar zahra,

itadai cewa tayi batasan komai akai ba.

iyayen zahran basuce komai ba,

alhj saifullahi dakanshi ya tuntubi ishaq akan yakamata zahra tatare tunda ta warware,

ishaq jiyai kamar anmashi bushara da Aljanna don haka yabar wuka da nama a hannun dady din.

Dadare kuwa dady yasamu abba agida bayan sallar isha’i kamar yanda ya alkawarta.

Abba yaji dadin yanda suka nunamashi kulawarsu akan zahra don haka yace”Ai alhj da zahra da ishaq duka nakane don haka kayanke duk lokacin dakaga yakamata in Allah yaso zata tare.”

Alhj saifullahi bakaramin dadi yaji ba yace”totunda abun yqzama haka nasaka nan da sati guda,aiba wani dogon sha’ani za’atsaya yiba.”

Abba yace”kwaraima kuwa,kuma kasan aure yafi albarka idan aka takaita almubazzaranci aciki.”

dady ya gyada kai yadora dafadin”duk meke kawo wannan fituntunun idan ba saka riya acikin aureba,kaga masu kudi basu kira malamai sunyi wa’azi a auremsu ba amma sunkira mawaka fiye da ashirin.da’anyi magana ace ai zamanine.”

dariya abba yayi yace”to’ai gashi tun ba’aje ko’inaba anbama shedan lasisin zama na dundundun agidan ma’auratan karshe saikaga auren tun ba’aje ko’inaba anata samun matsala.”

musamman dama angama shashanci awaje to abu kadan saikaga zargi yana shiga tsakanin ma’aurata.

tun ba’aje ko’inaba saikaga anfara marin juna dq nuna ma juna yatsa.”

dady yayi tsaki yace”barta nunama juna yatsa yanzu gashi har anfara kisa,amma abin haushi mutanenmu sunma maida abun abun wasa da tsokalar juna dashi.”

Allah ya kyauta”

cewar abba dayake mama kin abun.

(nimadai nace amin)

koda abba yadawo yasanar da umma yanda sukayi da dady fatan alheri tayi,sannan taroki abba daya sanarma sauran yayun zahra zuwa da safe.

hakan kuwa akai ranar juma’a takama ranar zahra zata tare but umma tahanata gayyar kawaye.

*mum meenat*✍????

*for any corrections;comments or complain about this buk you should contact me as 07014709470.pls wtsapp only*…????

[8:02PM, 11/27/2017] maman meenat????: ​MIJIN ‘KWAILA​????????‍♀

chapter 23.

​written by maman meenat​????

​A​wannan ranar kam inkaga zahra sam bazaka shaidata ba don kyawon datayi,

donma matsalar duk yanda su anty lubnah suka dage akan tabari sumata kwalliya mekyau amma fir zahra kin amicewa tayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button