HAUSA NOVEL

MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

shigewa daki tayi abinta tajawo tarkacen kwalliyar tazauna bakin gado tasoma dankarama fuskar tata foundation yakama fuskar yayi shanana dashi don bawai tayi blending dinshi bane.

powder ta dauko no 1.memakon number 3,matsayinta na baqa tadora saiya kasance kalar powder din yafita davan da kalar foundation.

kwallima data shafa hawayen masoyi tayi;wato tajawoshi har gefen kunnenta.

asannan tasoma tsara eyebrow dinta,dafarko tafarashi kamar abin arziki sai-dai mamadin tayi using eyepen wajen yin brow din saita dauki kwalli kajal tasoma zanawa akan girar tata data kasance mefadice datsayi bayaga yalwar gashi da Allah ya yalwanta mata.

Agaban giran tayishi mefadi sosai yazarce kima saikuma tayi tsakiyan dan siriri dashi karshen girarma sai tayishi kwalele,don haka shape din yafita kamar tabarya.

ja sosai na lipstick tasakama lips nata masu taushi,

bayan tagama zageye bakinnata da bakin kwalli

 tsuke bakin tayi tana karkata fuska aganinta babu yana biyunta wajen kyau.

dankareren leshin jikinta dayasha dinkin riga da sket yamatukar amsarta.

kalar flwers na less din shine kalar siririn mayafinta hakanan takalminta duk kala dayane cikas dinta kawai kwalliyar.

yanda tafito tana takawa das-das yajawo hankalin matan gidan,duk da kasancewar umma batayi gayya ba illa yan uwanta dana abba hakan baihana gidan xika da yan ganin kwakwaf ba.

wata daga cikin abokanan wasan zahrance ta rangada guda lokaxin da idonta yasauka akan zahra metahowa cikin tafiyar yanga.

sahura ta sake rangada guda dafadin”tofa ga amarya agidan ishaq nan tafito,barka dazuwa sarauniyar isiyaku.,”

zahra ta farfara mata idanu dazummar wucewa,amma sahura donta tsokaleta tace”wai wannan kwalloya haka saikace wata ba’indiya zahra.”

zahra ta juya manyan idanunta dafadin”aidai nayi kyau ko?.”

sahura tace kwarae ma kuwa,don wannan da angon zaiganki wata kila tun daga yau ali zaiga ali.”

sauran mata suka kwashe da dariya,

wata daga cikinsu tace”aifa lallai,yaganta tu’bul-bul yazata wata gara zai kwasa;Allah sarki inama inzama sauro inmakale insha kallon gwagwarmaya.”

sahura tacafe,”yo ni amaryar banmayi zaton tasan harkar ba ai.”

umma tafito daga daki tanama sahura dakuwa tace”kinci gidanku sahura,yazaki sakamun yar auta agabane wai eye.”

sahura tana dariya tace”allah umman zahra kibani ita insakata daki

 inmata yar nasihar nan tamu ta manya watakila ashawo kanta.

umma gaba tayi”kyaji dashi dai.”

su anty hafsa ne suka shigarma zahra akayita caccakar juna.

hakan yabama zahra damar sulalewa tafita babu wanda yasani.

akofar gida tayi kacibis dasu ummilolo anrasa gwanin dazai ahiga gidansu zahra kowa yana tsoron unma.

dasauri zahra takarasa ta basu hannu suka kashe tadubi uwande datasaki baki tana kallonta tace”dalla lafiya kike kallona,konaci ban biya ba.”

uwande ta washe hakora tace”uhm ganinai kinzama yar gayu wlh.”

dariya zahra tasaka kafin tace”yara kuma bakuda wayo kuce aimuku aure irinnawa,yara gidan bene zankoma inta kwana acan.”

ummilolo tadanyi sakale,saikuma tasaki dariya”su zahra yan gayu za’asha dadin bene.”

zahra ta kyalkyale da dariyar jin dadi,

ummilolo tace”dama ace nice zahra yaseen indinga hayewa kan bene inayin sululu.indinga shan dadina.”

sauran yaran suka dinga dariya dafadin”ahegiya zahra za’asha dadi????.

zahra jin ana zugata hadacewa”aidama d’arewa zanyi har abinci akan bene zandinga ci,idan yara sukaje shan dadi inkorosu yanda akeyi gidan alhaji canji.”

duk yaran suka goya mata baya akan haka zatayi.

yar purse din hannunta tabude tafiddo dari biyar din da abba yabata da safe kafin yafita yace yaudai tasha shagalinta.

nunama su ummilolo tayi,nanfa uwande uwar shawara tace”taf danice zahra kasuwa zanje insiyo magarya da aduwa da kukar yin kwarbebe indingayi inashan abuna wlh.”

aiko zahra tace efaaa.azo aje kasuwa asiyo hada farama.”

hakan kuwace ta kasance,duk tarkacen dasuka lissafa seda suka siyo hada goruba,zahra jinta take kamar yau take sallah don yau tana watayawa son ranta.

gidan su uwande suka shige,gidan bakowa sunacan gidansu zahra.

dayake gidan ginin kasane katangar duk ta gwanbale hakan yasaka zahra d’arewa akan katangar tana gwaguyar goruba hankalinta kwance.

sauran kawayen suma suna tsaitsaye gefenta,tadaiyi abin kirki tabama duk mutum biyu daya su raba.

itakuma uwar gayya tadumtse ledar a hannunta.

acan gidansu umma kam hankali yatafi bawanda yafarga da zahra tafice daga gidan.

***”***bangaren ango ishaq kam yau farin ciki bqya misaltuwa kallo daya zakamashi ka tabbatar da hakan.

duk da ayyuka sun sakashi gaba yau yaso ace shine dakanshi zai dauko little zahranshi,amma bayanda ya iya dole yayi handling komai awajen sadiq dasauran friends dinshi.

Dr.rukayya ma gida yagama cika da baki,su aysher ne kan gaba wajen hidima.

gwaggo rabima kakar ishaq ta’iso tun jiya hakan ba karamin dadi yama dr.ayaher ba.

[8:18PM, 11/27/2017] maman meenat????: wadda keta kaiwa da kawowa,

gwaggo rabi ancakare da wani leshi me dankaren kauri,

gwaggoro tayi da kallabin tadauko kujera tadasa kofar dazata sadaka da sashin da zahra zata zauna tahana koda yara su gifta.

duk wanda zaishiga zata soma sababi”kaga munafurci wato anga isiya zaiyi amarya shine akeso a’bata mashi dakin amarya to naga me wucewa nan.”

yanda ta kwama gilas afuska kamar aku kuturu shine zaibaka dariya????????.

ganin hakan yasaka dr.aysher neman kujera tazauna gefenta dafadin”bari intayaki gadi gwaggo naga yara sunason bata dakin amaryar.”

gwaggo rabi tace”kemadai kya fada yannan,ita waccan(tana nufin rukayya)dayake bata kishin danta aikinga tazuba masu ido,salon akawo amaryar tace dakin yayi dauda.”

dr.aysherh tace “nimadai haka nagani gwaggo”.

gwaggo rabi tawangale hakoran dawasu sunfara zubewa tace”ainakosa inga wannan amaryar nasam saitafi ta dan’uwanshi,dayaje yakwaso kafura gashinan jikokina sunzama kamar basu sanniba da anyi magana su turanci,ke ko sallah basayi fa.kinga yanzu ita wannan datazo ta haifomun nawa nasu ko kallo basu isheni ba.”

dariya takama dr.aysher taguntse baki.

nima dai dariyar nayi nace ” ​mata ku qame qam​????

​mum meenat​????

[12/12, 4:31 PM] ‪+234 814 483 2069‬: *MIJIN ‘KWAILA*????????‍♀

Chapter 24.

*written by maman meenat*????

*edited by Aysha abdullahi (umman faruq*????

*Inasake jaddada godiya gareku masoyana masu kaunar rubutuna hakika kunada gurbi na musamman acikin zuciyata.*

*inasonku fiye da ynda kuke sona,naga sakonninku masu tarin yawa akan tambayar maman meenat lafiya.masu kirana masu text messages damasu taboni ta watssapp hakika ina jindadin haka tare da dinbin godiya,Alhamdulillah meenat tasamu lafiya jazakumullah for the special prayers*????

Wuraren 5:pm yan daukar amarya suka iso,zahra dakecan tana wasanta dasu ummilolo tahango anty lubnah ta nufosu a fusace.hakan yasakata dira daga kan guntuwar katamgar dasauri,karasawa tayi kusa da anty lubnah kafin tayi wata mgna anty ta tareta dacewa”da iznin wa kika fito daga gida?”

Idanun zahra dasukayi narai-narai tasoma kwabe baki danufin kuka,anty lubnah tamaka mata harara tace”kika yimun kuka a swear saina baki mari stupid din yarinya kawai.”

Zahra ta kauda kai taji haushi anty taamata fada agaban kawayenta.

Tasa keyarta antin tayi,uwande tabiyota da sauran tarkacen data siyo tana cewa”zahra ga magaryarki”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button