MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

[06/12 1:11 pm] Maman Meenat: Ishaq kasa magana yayi don tsananin mamaki,amma daya tuna jaraba irinta gwaggo rabi saiya saki murmushi yace”shikenan matar,ai duk abinda kikace shi za’ayi,
Bari inje kada amarya tagaji da jirana ko?”
Yakare maganar yana haramar wucewa.
Gwaggo rabi data rangada guda tace”jeka sabon ango Allah yabada sa’a,bance ka sasdauta mataba.
Don banson ta rainamun kai.
Bayanma bikin yazo ina umara ai naso ace dakaina namka hadin uban maza,”.
Dariya kawai ishaq yayi yashige abinshi.
Gwaggo rabi ta bi bayanshi da addu’a harya bacema ganinta.
Komawa ciki tayi ranta fes,addu’arta daya daren yau tasamu jikoki.????
Zahra amarya tuni tasoma baccinta da kayan dake jikinta, ta takure akan kujerar datake zaune.
Hanan dama tana ganin zahra tfara bacci itama tayi dakinta abinta,don dama atakure take.
Da sallama yashiga dakin,
Ba’a amsaba,sai kamshin turaren wuta kawai dake tashi.
Yakarasa ciki ahankali,
Idanunshi sukayi tozali da zahra dake kudundune tana kwasar bacci abinta.
Ajiye ledar hannunshi yayi,ahankali yasaka yatsanshi ya zagaye round face dinta dake kara kyau intana bacci.
Tsuramata idanuwa kawai yayi,ahankali tunanin late zahra yasoma ziyrtar zuciyrshi,
Ya numshe idanunshi dasuka ciko da hawaye,
Baitaba ganin kamanni zallar kammani kalar na zahra da zahra ba.
Yanada tabbas dakuma yakinin Allah ne ya canja mashi little zahra da waccen late zahra din.
Wani mugun sontane yake ratsa dukkan sasan jikinshi,
Kama hannunta yayi ahankali yasaka cikin nashi yana murzawa ahankali.
Hakanne ya farkar da zahra dake bacci tabude idanunta tar akanshi.
Donma sa’arta daya batada magagin bacci.
Idanunta ya gauraya dana ishaq, tamike dasauri tana murmushi,tace”lah kadawo?.
Shima smile ya sakar mata yace”nadawo zahra,haka kike bacci da wuri dama”.
Dariya tasaki kawai.
Kamo hannunta yayi yace “zokici abinci ko?”
Tadan langwabe tace “aina koshi.”
Namaci wanda mummy takawo.
Kallonta yake cikin ido yace”nawa special one ne ai.oya zokici”.
Bamusu tamike,dakanshi yakama hannu ta har toilet saida tawanke baki,
Shine ya yanka mata kazar,zahra wadda tasaki baki tana kallonshi sam bata tankaba.
Ganin ya nufi bakinta da naman yasa tace”tab!nidai kabani inci dakaina,saikace banda lafiyane zaka bani abaki.”
Dariya kawai yayi yamika mata plate din,datake batajin yunwa bataci wani me yawaba ta ture.
Dakanshi ya hada mata ruwan wanka tawatsa tana korafin”nidai ummana batacewa sainayi wanka idan ina bacci.”
Kayan baccinta yafito mata dasu,nanma bata musaba tatube riga agabanshi tasaka ta baccin.
Kirjin Kama’s kamar siminti???? .
Bai damuba,shidai kallonta kawai yake.
Saida tagama tahaye gado takwanta abinta.
Shima wankan yayo yagama shirinshi dayake na al’ada,
Ahankali yahawo kan gadon,yajawo zahra jikinshi.babu komai aranshi kawai yanason jinta kusa dashi.
Zahra kam bigit tamike idanu waje tace”anan zata kwanta,”
Bai tankataba,illa smile daya sakarmata.
Mikewa tayi,tana yayimar batgo tace”tab!nidai wallahi bazan kwanta kusa dakai ba,niba ‘yar iska bace.”
Ishaq yarike wuya yana kallon zahra dake murguda baki.
*mum meenat✍????*
*for any correction,comments or complain you should contact me at 07014709470*????
*MIJIN ‘KWAILA*????????♀
*written by Maman meenat*????
Chapter 26.
*Ina baku hakuri masoya akan jina dakukai shiru jiya,nayi typing har nayi post abun haushi WhatsApp din yasamu matsala wannan yasaka gaba daya nayi missing komai nawa saida nasake installing kuyi hakuri pls*.
*Wasu zasuga sunman magana banyi responds ba,tokuma kuyi hakuri matsalar tashafeku kuma,don gaba daya chats dina suka ‘bace.I luv you guys’????*.
Ishaq wanda yasake hannayenshi ya tallafo wuyanshi kallon zahra kawai yake yana smiling, wai ita ba yar iska bace.Chaii,shikam inbanda soyayyama mezai tsinta ajikin zahra wadda ko irin yar kirgan danginnan nayara ma bata fara ba.
Sakkowa yayi ahankali yatako zuwa inda zahran take kwance,gaba daya ta takure jikinta tasaka kafa duk ta tattake bargon datake ciki lullube aganinta babu tayanda ishaq zai iya budewa.
Acikin ranta kuwa tana ayyana ishaq amatsayin dan iska,to dan iska mana inba iskanci ba nameye zaice wai zai kwanta kusa da ita?”
Tai kwafa daga kwancen datake aranta taraya tadena sakar mashi fuska tunda d’an iskane dama,kai gobema zatayi tafiyarta gida tafasa shan dad’in bene.
Da tulin tunane tunane babban barawo bacci ya sureta,batayi aune ba.
Ishaq dake tsugune gabanta yanajin alamun tafara bacci yasauke ajiyar zuciya,aranshi yaraya “zahra hukumace saida lallashi.
Kacokam yadauketa itada bargon ya shimfide bisa gado,yagyara mata kwanciya yaja pillow yadora kanta akai,gashinta yasauka bisa pillon.
Yadan jima yana kallon fuskarta kafin yashafi tattausan gashintan yayi addu’a ya shafa mata gami da sumbatar goshinta.
Yajuya ahankali yarage hasken dakin daga full light zuwa dim light yafice daga dakin bayan yaja mata kofar.
Kai tsaye dakinshi ya nufa,yagama shirinshi yakwanta abinshi aranshi yana karajin kaunar zahranshi jini da tsoka.
Yadau tsayin lokaci kafin bacci yayi gaba dashi.
Washe gari karfe 4:30am yatashi kamar yanda yasaba koda yaushe,a’aldarshi yakan tashi ya gabatar da nafiloli yayi karatun Alqur’ani kafin kuma yayi sallar asubahi.
Hakance ta kasance kuwa don saida ya kamalla komai yayi shirin masallaci,dakin zahra yanufa danufin tayar da’ita tayi sallah.amma ga mamakinshi ya’isketa tana sallar.
Wucewa masallaci yayi abinshi aranshi yana raya uhm lallai zahra anfara hankali koda yake gaduk wanda yasan Abba dakuma tarbiyar gidanshi yasan wasa da ibada baya daya daga cikin dabi’unsu.
Abba mutum ne jajurtacce daka tsaya tsayin daka wajen gina rayuwar iyalinshi abisa koyarwar kitabu wassunah donma Allah yabashi zahra datake neman gagararsu.
Ishaq bud’e kofar part din nasu yayi danufin wucewa masallaci, amma kuma saime?
Gwaggo rabi yagani rakabe jikin glass din window takasa kunne bagalo,ko motsin kirki batayi gaba daya hankalinta yana kan abinda takeyi.
Gaban ishaq yafad’i,aranshi ya ayyana gwaggo rabi amatsayin jarababiyar tsohuwa,to jaraba mana,inba jaraba ba mezai kawota kofar taga da asalatun fari.?
Wato tana labene taji abinda yake wakana tsakaninshi da zahra.
Kwafa yayi kafin yakarasa inda take gami da dafa kafadarta.
Azabure tajuya tana cewa”wa’innahu min sulaimana…..”
Sauran maganar tamakale afatar bakinta ganin ishaq ne,tasauke ajiyar zuciya cike da borin kunya tace”Amm,af…dama cewa nayi bari inzo inji ko kuna bukatar wani taimako,kasan yaran yanzu badai raki ba.daga sun kwana da namiji saikaji sun langwabe wai basu da lafiya.”
Takare maganar tana gyara daurin zanenta dayake kokarin kwancewa gami dajan majina sharab,tawaige gefe ta fyace feeet.ta durje hancinnata da tafin hannu,bayan tahad’e hannun na dama da hagu ta mutsuke kamar wacce ke shafa versiline.
Ishaq ya watsa mata harara cike da kallon yanda take kazanta yace”to ai saiki koma inda kika fito,dondai bawani taimako naki damuke bukata.”
Wangale baki tayi tace”to ai shikenan ma,fitomun da kyallen ko.”
Juyawa yayi yana tafiya jin anfara tada sallah yace”kije kiyi sallah abinda zan dawo ne.”
Aiko bamusu tajuya itama tana sambatu dafadin”to Allah dai yasa Anfara asa’a ai haka muke bukata,kafi yayanka hankali me auren kafura.kaga da’ace yanajin maganata Aida tuni yasaki kafurar nan yazo nan gida yayi aurenshi abinshi.