HAUSA NOVEL

MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shidai ishaq gaba yayi baisake tanka taba,sai dai harga Allah bayason wannan sakarcin da tsohuwar takeyi,aganinshi  ragema kanta daraja take.

Yo danma zahra yarinyace,da’ace babbace taleko taga abinda Rabin takeyi aitsaf zata wanketa soso da sabulu.

Yaja tsaki shidaya yana takaicin halin kakar tashi.

*real mum meenat*

Maman muhamman Naseer ba????

*MIJIN ‘KWAILA*????????‍♀

Chapter 27.

*writing by Maman meenat*????

Sai wajajen karfe bakwai yashigo gidan,bangaren amarya zahra yafara lekawa,kwance ya isketa ta kudundune cikin bargo.hakan yabashi tabbacin bacci takeyi,yaja mata kofar yanufi bangaren iyayen nashi.

Gwaggo rabi itace uwar zaman falo to yaudai bata falon don haka kanshi tsaye yanufi dakin mum din,tana gaban dressing mirror tana gyara zaman kallabin kanta lokacin dayayi sallama hadi da sawo kai cikin ni’imtaccen dakin nata dabai rabo da kamshi.

Murmushi tasaki tana amsa sallamar tashi, karasawa yayi inda take yadafa kafadunta hadi da d’an kwantar dakai bisa bayanta yace”morning momma.”

Tasaki karamar dariya dacewa”haba ishaq kaiwai meyasa har yanzu sam kaki ka girmane,yanzufa kazama babba kafara aje zuri’a saika rage wannan shagwabar taka.haka yayanka zasu taso suganka gotai-gotai kana yimun shagwaba ko?.

Dariya yayi sosai yace”mummy niko yara d’ari na ajiye ai bazan dena yimaki shagwaba ba,kefa mumma dina ce.kuma wacce akoda yaushe Idan nakalleta nakanji dadi mara misaltuwa so why zandena langwabe wa momma alhalin har yanzu am still young. “

Gyada kai tayi tana dariya tace”to aikaga saika bada himma,ina d’iyata zahra baku shigo tare ba mu gaisa.”

“Naleka na’iske tana bacci,inaga bayan tayi sallah ta kwanta.”

Yabata amsa lokacin dayake goge mata takalmin data fiddo zata saka.

Mikewa tayi tace”to aibari intasaka gaba muje kugaisa da dady,saimuje mugaisheda gwaggo rabi,mumata bangajiyar biki ko?.

Ishaq kai yasoma sosawa yace’am haba,gwaggo ai tuni mun gaisa,sai dai ko dady din.”

Itadai mummy gaba tayi,tana cewa”to aisaika bada himma,dafatan baka mance yau Saturday ba.kace kunada meeting appointed da shugaban NTA akan tafiyar ka ko.?”

Narke idanu yayi yakoma kalar tausayi,yace”ina sane mum but ina tunanin yanda zantafi inbar zahra banmasan iya adadin tym dazanyi a can kasar ba.”

Kallonshi mum din tayi tace”wannan aiba abun damuwa bane ishaq, anawa ganin wannan riba biyu ce.natabbatar kafin kadawo zahra takara girma takumayi hankali,da ikon Allah.kaima zakafi son hakan ai.”

Sadda kai kasa yayi kawai.

Har akasan zuciyarshi bayason tafiya yabar zahra,haba toma menene amfanin auren matukar baya tare da ita.”?

Kai tsaye bangaren dady suka nufa,yana zaune bisa sallaya yana karatun Alqur’ani sukayi sallama.

Saida yakai karshen ayar dayake karantawa yadago kai yana kallonsu hadi da sakar masu mutmushi,

Suma murmushin sukeyi mai,musamman ishaq dayakejin tamkar an nunkamai farin cikin shine.

Mum tafara gaidashi,sannan ishaq shima yabada tashi gaisuwar.

Dady dake shafa kan ishaq yace”babana angirma,naga kwana guda harka kara kiba,me zahra y’ata dafa makane haka”.

Mummy data kyalkyale da dariya tace”ah to tambayarshi dai.”

Shidai ishaq dukar dakai yayi kawai yana smiling,

Kamar daga sama suka jiyo muryar gwaggo rabi,tana fadin ina mesunan malam din yakene.

Wato nizaka mayar shashasha ko,inzauna tsayin lokaci ina jiranka ashe kainan kataho wajen uwayenka kabarni baki sake,tunda ni ba uwarka bace ko?”

 Takare maganar tana shigowa dakin,

Ishaq aranshi banda Innalillahi babu abinda yake mai-maitawa.shikenan yau tsohuwar nan zata mashi fallasa kuwa iri-iri.

Gwaggo rabi data nemi waje tazauna tace”dakai nake,kayimun kasake,nace ina kyallena ko uwayen naka kafara kawomawa sugani.tunda naga ai kabanbanta tskanina dasu,todai kasani tushiya itace mafarin dawa.daban haifi ubannakmeida kaima bai haifeka ba.tomezaku boyemun,inma yarinya bata kawo matancinta gidan miji ba aigwara kufada tunda wuri tagane inda dare yayi mata.”

Zufa sharkaf tagama rufe ishaq yace”haba iya,waike meyasa kike hakane don Allah? Nace ai kijirani ina zuwa ko?”.

“Injiraka ina?.

Cewar gwaggo rabi dake runtse idanu saboda tsabagen masifa.

Taci gaba” kaga daka ganni nan,duk da banyi boko ba tofa bawata bariki dadan boko zaiyi inkasa ganewa.inma zaka fito da sheda kafito da’ita kowa yagani.nan dai dagani saiko iyayenka gasu,bawani bare acikinmu.”

Dady daya kasa gane kan inda zancen yanufa yace”shin tsaya gwaggo, waidon Allah duka wannan tada jijiyar wuyan dakukeyi ta mecece,meke faruwa ne.?

“Ka tambayeshi,”

Cewar gwaggo rabi dake nuna ishaq da yatsa.

Dady yajuyo wajen ishaq dya dukar dakai kasa yace”babana ya’akayine,meke faruwa tsakaninka da mutiniyar taka kuma.”

Ishaq ya sauke ajiyar zuciya yace”no dady,bawani Abu bane kawai dai….”

“Kawai dai me?..”

Gwaggo rabi ta katseshi,

Taci gaba”inma zaka fito fili ka sanar dasu gaskiyar zance kafito,donni ba’a munafurci dani kasani.”

Dr.rukayya da tunda ake maganar sai yanzu tasa baki tace”gwaggo inaga idan yaki fadi kawai kirabu dashi kisanar damu abinda ke faruwa.”

Zumbur ishaq yace”but Mumm.”

Da hannu ta dakatar dashi,tace munajinki gwaggo.

Aiko gwaggo rabi kamar dama jira take,tasoma wassafa labarin yanda komai ya wakana AtoZ.ba dady da ishaq ba hatta mummy saida abin yabata kunya.

Tace”gwaggo inaga don-dai bakisan wacece amaryar ba yasa kike wannan maganar,amma duk meenat*a anawa ganin yanzu andena wannan al’adar ai tuni. “

“To gwanar na’iya.”

Cewar gwaggon,”aiduk abinda yaronnan yakeyi da daurin gindinki yakeyinshi.amma bari inje wajen amarysr dakaina”.

Tamike tana dafa kafa tayi gaba,bata saurari kiran dasukeyima taba.

Ishaq yamike zai bita,dady yace”barta taganota watakila idan tagantan zata dena maganar datakeyi.”

Dole yakoma yazauna hadi da dafe kai kawai,yana tunanin rikici irinna wannan tsohuwar.

Da sababi tashiga sashen amma jin anyi tsit yasakata cewa”to lallai y’ar mai,kyaci ubanki kuwa.wato agidan jikana zaki kawomana lalata,to munfi karfinki munrigaki munce Allah kina ina fito algunguma.”

Still dai shiru taji,don haka ta nufi dakin datake ktautata zaton na amaryar ne ,tana tijara.

Wayam dakin ba kowa,

Hakan yasakata rike baki dace”ah lallaifa,amaryar kinsamu sake .”

Bata karasa maganar ta ba,tajiyo  abu saman kanta racacau…

Tazabura dasauri tace”mun shiga uku,ruwa kuma adaki me rufi?..”

Sauran maganar ta makale afatar bakinta hango zahra datayi can koli bisa wardrobe tana tsotsar magarya.

Fuskarnan tasha shegiyar kwalliyar nan tata mekama data aljanu.

Goruba tadauko tafara gwaguya,bayan tafesoma gwaggo rabi yayan magaryar data tara abakinta.

Tanaci tana gwalo idanu,dayake barakumullah akwai manyan idanu saita kara tsorata gwaggo rabin.

Aiko aguje ta ufa,tana fadin wayyo ku agajeni, jama’a aljana a dakin amarya….

Zahra jin an ambaci aljana yasata durowa Dirk, kamar wacce aka jeho ta rufama gwaggo rabi baya….

*mum meenat*????

Maman Nasirudden dinku????????

*

*mum meenat

*MIJIN ‘KWAILA????????‍♀*

Chapter 28.

*Writing by Maman meenat????*

*Edited by Aisha Abdullahi T.Fulani (Umman farouq)*

*Wannan shafin d’ungurunhun na sadaukar dashi gareki Ameena Muhammad’meenat faxy novel????.*

*Dakuma Ameenat shamsu,my meenat Ameena Abdullahi kai dama dukkan wata mesuna Amina,hakika mum meenat tana kaunarku sosai*.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button