MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Saida ya ‘kawata fuskarshi da murmushi sannan yace”mummyna nasamu zahra..zahra tadawo gareni mummy awannan karon bazatayi nesa daniba,d’iyarki tadawo gareki mum….!
da hannu ta dakatar dashi”isha’q wai sai yaushene zakasan wanda yamutu baya dawowane,ayaushene zakasan cewar allah daya d’auki zahra yafimu ‘kaunarta.saiyaushene zaka dena takura tunaninka da lafiyarka akan wadda babu ita a doron duniyane?
Zahra ta mutu, a gaban idanuna aka wanke gawar zahra.zahra d’iyar ‘kanwatace nice na reneta tundaga ranar da mahaifiyarta ta haifeta batakoga fuskartaba takwanta tamutu,naso zahra na tausayama zahra nasani bayagani kaine mutum na biyu dayasha d’awainiya da zahra amma kasani zahra ba rayayya baceba.
Mutayata da addu’ar gafara dabeman dacewa don zahra mutumce guda harda ‘kari
Ama yamuka iya’allah yafimu ‘kaunar zahra ya amsheta a daidai lokacin damukafi bu’katarta,saimu bita da add’ua kaikuma kasaka dangana wa ranka ka rungumi ‘kaddara matsayinka na musulmi nagari.”
Bai katsetaba har saida ya tabbatar da takai aya,sannan yaaja hannayenta yaxuwa d’aya daga cikin kujerun falon yazauna yana fuskantarta,bayan yagama saita dukkan natsuwarshi gareta don ta yarda dashi takuma gane baizo da wasaba a wannan karon.”mum wlh kiyarda dazancena mum,naga zahra ganin idanuna,zahra dai mum tana cikin students mum, a tattare da ita akwai yarinta nasani bawai ainahin zahrata baceba.amma inada tabbacin wannan itace zahran da zahrana take gayamun akoda yaushe,itace wacce zahra kefad’amun cewar _isha’q zaka samu zahra madadina koda bayan raina,zakasamu xahran da zata d’auke maka kewata.naro’keka da kobayan babu raina kajirayi xahra,kasota kamar yanda kake sona koma fiye da hakan._ _inamai tabbatarmaka itace alkairi a gareka._
Yaci gaba dafad’in”mum dani dake daduk wani ahali na gidannan yasan dahakan,mum kinatsu kituna maganganun zahra don allah kada kice wai bana cikin hayyacina.”
Doctor ru’kayya tami’ke cike da tsantsar tashin hankali,tana zagaye katon falon hannunta goye a bayanta akan fuskarta akwai zallah damuwa dakuma rud’ani.
Sai dai kuma batasan tayaya zata’iya ‘karyata isha’q a ‘irina wannan lokacin dayazo mata da magana sahihiyaba.
A dukkan nazarinta dakuma hasashe irinnata tanada tabbacin isha’q yana cikin natsuwarshi ne.
Tasauke numfashi,itakam a dukkan tarihi ko’a mafarki kai a film’s ko fili bata ta’ba ganin soyayya zahirinta irinta isha’q da zahraba,
Idan zahra tayi ciwo isha’q ko baya ‘kasar shima saiyace bayada lafiya,
Kuma dsame inda zahra tafad’a yana mata ciwo.
Kai tasha jaraba soyayyar tasu tana ganin ko plane ne suka had’a mata amma inaaa,saitaga zahirin ‘kaunane kawai dakuma had’uwar jini.
Sam bazata iya wancakali da bu’katar isha’q a wannan lokacin dayake neman taimako daga garetaba.
Tataka a sannu ta’isa gareshi tadafa kafad’arshi”bazan kiraka da wanda baya cikin hayyacinshi ba isha’q,nasani soyayya ba ‘karya bace ba.
Koma dai menene kaci gaba da bibiyar yarinyar,nikuma zansamu lokaci kakaini har gidansu inganta da idanuwa don tabbatar da gaskiyar zancenka,kafinnan kasamama zuciyarka salama.zahra adam ta isha’q ce.”
Yawani d’ane bayanta yana fad’in”tnx so much my luvly mother.”
Ta murmusa kawai,gami da kama hannayenshi yazuwa dining don bin abinci.
**************
Zugar su zahra da’aka taso makaranta,kai dagani babu tambaya kasan yau akwai masifa,itada ‘kawayenta duka zasu tseremata a shekaru amma tafisu yanayin girma,saboda jikinta irin ga’ba-ga’ba dinnan yake.
Su shidda reras duka suna fadanci wa zahra wadda keta ruwan bala’i ta d’aura kallabi saman hijabi taci d’ammara da dardumar dasuke xaunawa kanta a makaranta.
Bakinta har kumfa yake tana bamasu ummilolo labarin yanda zasuci uwar dije ali,wacce tasaka malam yayimata bulala biyu d’azu a aji.
Taraba yaran gida uku tace”ke ummilolo kune da hinda zaku shiga gidan saikuce a sammaku ruwa zakusha,daganan saikuce ina dije ‘kawarmu tazo ta rakamu tana zuwa mukuma zamu la’be zaure mu’kunshe mata baki,mujawota aje lungun bata kashi.
Wlh saita gane batada wayo.”
Sauran yaran sukace”eeeefaa haka za’ayi kuwa.”
Sukatafi d’uuuu kamar garken tumakai,
Kafin sukai gidansu dije yamma tayi sosai,
Can wani kango suka hango almajiri yana kashi,
Zahrace tafara hangoshi taja dabaya da sauri,tace da sauran ‘kawayennata”kutsaya kai ga al’majiri yana kashi,asamu d’an dutse a jefe takashin kashin.”
Suka la’be suna lekenshi,can ummilolo ta dau dutse sauko a qeyyar almajiri,suna fad’in amma ka’iya kanannad’a maciji.”
Kowando baigama sakawaba yabiyosu a guje,dayake ko barewa nan tagansu ta barsu almajiri ko ‘kurarsu baiganiba.
Basuyi burkiba saizauren su dije,
Saida suka huta sannan suka gyara kamar natsattsu,ummilolo ce tashiga da sallama,innar dije na alwalar mangarib ta’amsa da kallon rashin sani akan fuskarta.
Ummilolo ta gaisheta ta amsa,sanna tace”don allah a sammun ruwa zansha”.
Matar mai fara’a ta debomata ruwa a randa mai sanyi,ummilolo baki kawai ta d’ofana, ta mikamata kwanan dafadin “angode”
Matar tace”yauwa”.
Tana juya baya ummilolo tayimata gwalo,
Sannan tace”ina dije yau banganta a makarantaba.”
Matar tajuyo da fara’a tace”aiko na aiketa siyen manja aitadad’e da dawowa.kema naga kinmakara ko aikenki mamanki tayine.?”
Ummilolo tayimata gatsine dafad’in “uhm”.
Matar tace “to ayimaza akai lada gida ko.?”
Ummilolo tajuya dasauri,tafita donyima ogarsu zahra albishir amma saita hango zahra ta nad’e ‘kafar wando tacire hijab ta’ajiye gefe guda.
Tana turza ‘kafafu a’kasa
Sauran yaran sunja masu layi ‘atsakaninta da dije,
Dagudu ummilolo ta ‘karaso ta bugi ‘kirjin dije,sannan ta bugi na zahra tace”wanda yaji zafi ya rama.”
Aikafin kace miye,zahra ta kaima dije duka”ninaji zafi.”
Dije da tuni jikinta yad’au rawa tace”nidai bafad’a nazoyiba uwata ta aikeni,kuma inajin maganar uwata.”
Zahra ta fidda manyan idanunta dafad’in”lalalala towaye bejin maganar tasa uwar?”
Dije da ido yacika da hawaye tace”kigane”.
Zahra takaimata duka,
Nanfa fad’a yasar’ke,zahra ‘karfi kamar doki nan danan tadunga sunkuta dije da ‘kasa,
Yara sunamasu wa’kar “bamu rabawa sai dai mu’kara zugawa bugi cikin.”
Zahra ko harwani ‘kara za’kewa takeyi tana nusar ruwan cikin dije.
Isha’q daya dawo daga gidan abokinshi sadiq suna takowa a’kafa saboda hanyar batada kyau yayi parking motarshi acan farkon unguwar.
Yaci gaba dabama sadi’q labarin “abokina kai idan kaganta sam batada maraba da zahrata,”
Sadi’q yace”gaskiya abokina kakamu sosai wlh.”
Isha’q yasaki dariyar ‘kasaita dacewa”kawai kamanninta da zahrane yasaka naji wani mayen sonta,kai bayaga zahra banta’ba ‘kaunar wata d’iya mace kanartaba.”
Sadiq ya kwashe da dariya”gaskiya abokina koda banga girl dinnanba nasan mai zafice,don nasan bakayi da ‘kwaila.”
Isha’q ya murmusa…
Maganarshi ta ma’kale cik,
Sakamakon hango zahra dayayi da bataliyar yara suna dambe,zahra har ‘kara over acting takeyi.
Sadi’q dake duban yaran yace”kai yarinyarcan badai masifa ba,allah tsine ranar da zata fito takoma ga allah batare da anrabata fad’a da yaraba.
Yarinya saikace shed’aniya,
Wannan zanga wandanzai kwasheta yakwashi bala’i.
Isha’q yaji ‘kirjinshi yabuga dam.
muje zuwa guy’s
September 21, 2017 at 12:05pm ·