MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

‘yar kyakyawar fuskarta dabata tsufa tana manne da glass din daje kuma kayatata.
Isha’q da hanan atare suka mi’ke dukansu suna sakarmata murmushi
Tazare wayar dake kunnenta tana sakarma kyawawan yayan nata murmushi,
Ta kalli isha’q dafad’in”yayankane muke maganar yarinyar dakake bani labari,yace kamata yayi mushirya muje muganta ayi komai da lissafi,sannan yakira wayarka tana a kashe.”
Isha’q yasaki dariya yace”nakashetane nasaka charge mum”.
Yami’ke da sauri yana fad’in”mum kice kawai inshirya yau saigidansu pretty,yawani dun’kule hannuwa da naushin iska,wlh mum saikin ganta she’s very beautiful nd younger.”
Mum tace “kome kakeso isha’q aibaka ganin muninshi,haka kake tun kana yaro.sa’banin yayanka dayakeda a’kida dakuma ra’ayinshi na santseni.”
Ya shafi gefen fuskarshi yana murmushi,”Allah mum tanada kyau,iluv zahra very much mum.”
Zaunawa tayi tana canja channel”idan kagama surutunka inajiranka,haka zakaje kana rawar jiki ai yarinyar saita raina class dinka,ya murmusa yana tafiyarshi ta ‘kasaita yace”haba mum kada kisa wannan ta’kwalar ta rainani mana.”
[9/23, 10:00 PM] mum meenat: Yanuna hanan wadda ta zubama yayan nata idanu tana kallonshi,
Dasauri ta tashi ta la’be bayan mum dafad’in “mum zakije dani”.
Doctor ru’kayya tamurmusa tace”kibari dai watarana saikije lokacin kinsamu hutun makaranta,yanzu kam ai zaki takuratane.”
(tazata zahra babbace )
Isha’q kam fakaitarta yayi yasaki dariya dafad’in”sai mumcy”,
Tana zaune tana kallon wani series yafito cikin hadadd’en yadinshi filtex mai yal’ki ruwan madara,
Kanshi yasha hular zanna bukar baqa,
Kafarshi cikin bakin takalmin daya matu’kar dacewa da shigar tashi.
Handsome and giant,
(abinda na raya kenan.)
Hadadd’en ‘kamshin turaren American crew yakasa barin jikinshi,
Still akwai farin glass a idanunshi,
Ita kanta doctor ru’kayya tana alfahari da isha’q matsayin d’anta very handsome guy.
Yanada dukan qualities daya kamata mace taso a tattare dashi,
Dogone irin tsayin hadaddun maza d’innan,yanada fasalin ‘karfi da jarumta a tattare dashi don ‘kwarae mayen exercise ne.
Yana rud’a makwad’aitan mata da kamfacecen ‘kirjinshi dakuma murdadden jikinshi.
Wankan tarwad’ane wato ya d’auko kalar doctor ru’kayya ne,
Sa’banin yayanshi aliyu dayake fari tar yad’auko kalar mahaifinsu.
Isha’q gogaggen matashine wayayye daya samu shedar kammala karatunshi na degree mataki na biyu akan mass communication ma’aikacine da gidan talabijin ta ‘kasa wato NTA sosai yake samun sa’konnin yammatan dasuke mutuwar ‘kaunarshi musamman don fara’arshi,
Dakuma iya zama da mutane don isha’q bdai iya kyautatawa ba.
‘karasowa yayi jikinta ya tallafi fuskarta da hannayenta”am readay my mum”
Yafad’a da shagwa’barshi,memasa kyau.
Tace “i see”
Tami’ke tana gyara zama mayafinta dasaka glass d’inta,
Isha’q ya tsuramata idanu”am proud of you be my mother mumma.”
Tashafi fuskarshi itama da murmushi,aranta tana jin zallah farin ciki saboda dawowar walwalar d’anta daya rasa tsawon lokaci.
Tare suka jera gwanin sha’awa suka shige cikin d’aya daga cikin motocin gidan,
Tazauna a mazaunin kusa da driver yayinda isha’q yake driving suka lula gidansu zahra.
Umma tagama gyara d’an matsakaicin gidansu,tana saka turaren wuta tajiyo sallamar doctor ru’kayya,
Taleko da fara’arta tana fad’in “lale marhaba da ba’kin yamma.”
Doctor ru’kayya ta murmusa aranta tana yaba wayewar umma.
Ruwan randa mai sanyi umma ta’ajiye gaban doctor ru’kayya,bayan ta shimfid’a mata tabarma.
Dr.rukayya tazauna tana cire gilashin idanunta,likaci guda tana kai ruwan da umma ta’ajiye mata a baki.
Takur’ba kana tace da umma”nasan baki sanniba ko?.”
Umma ta gyad’a kai”kwarai kuwa.”
Dr. Ru’kayya tasake murmusawa tace a ta’kaice”sunana ru’kayya anas kado malumfashi,ni haifaffiyar malumfashi ce,iyaye da dangi mahaifina y’an canne,sai dai dangin mamana sune mutanen funtu’a, nayi karatun likitana anan Nigeria sai dai nasamu sakamakon zama babbar medical doctor ne a India,inda acanne na’karasa karatun nawa.
Nayi aure anan kaduna da mijina babban d’an kasuwane anan abubakar gumi,awancen lokacin ayanzu yanada manyan kamfanoni a ciki da wajen ‘kasar nan.
Inada y’ay’a uku maza biyu sai autata hanan,
Babban sunanshi aliyu yayinda mai binsa shine isha’q,
Daganan haihuwa ta d’aukemun sai daga baya Allah yabani hanan,Aliyu yanzu haka yana ‘kasar turkey yana kula da kamfanin mahaifinshi dake jigilar rid’i.”
Muje zuwa
September 23, 2017at 10:27pm ·
*by anty y’ar charas*����♀
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����♀
NEW WORLD NOVELS
BY MAMAN MEENAT
EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR)
Wannan shafin naku ne yn (Madarasatul Tahafeezul Qur’ an Funtua, Allah ka qaramana fahimta a
iliminmu)
Chapter 6.
Doctor ru’kayya tad’an tsagaita jin ana kwad’a sallama,duka itada umma sukakai dubansu ga hanyar shigowar,abbane yashigo da ledar yalo a hannunshi,umma tami’ke da sauri tana mashi sannu dazuwa ta’amshi ledar dake hannunshi tawuce d’aki da’ita.
Abba yadubi hajiya ru’kayya kallon rashin sani,
Itakuwa ‘kasa tayi dakai tace”malam ina wuni ya hidindimu.”
Abba ya’amsa da “Alhmdlh”yawuce ciki bakinshi fal da tambayoyi.
Daki yasamu umma tsaye da alama zaman jiranshi takeyi,yamata kallon tsaf kafin yace”wace hajiyace nagani anan tsakar gida,kuma hada wani d’an saurayi nagani a ‘kofar gida dawata kwatsetsiyar mota,wasuke nema kuma?.”
Umma tad’anyi jim kafin tace”to malam nikam bazan iyacewa komai ba,nadaiga tazo batace ga abinda yakawota ba,amma naji tad’auko tarihin yaruwarta tana bani,bansan da wacce tazo ba.”
Abba yace “shige muje,aiyanzu zamani ya canja bana barki ked’ayaba.ina zahra ne,ko bata dawo daga islamiyyar ba.?
Umma tace”kaima kasan nanda isha’i yayima zahra kad’an kaganta anan gidan,watakil sai takwas na dare idan tagama yawon tsokanar jama’a.
Abba yayi ‘kwafa yace”gab nake da kawo ‘karshen iskancin yarinyar nan ai.
Umma tafito har tsakar gidan tana mitar”ai indai zahra ce,bazance bazaka iyaba amma abune mai wahalar gaske.”
Dr.ru’kayya ta kafe umma da idanu tanason nazarin maganar datake jiyowa tana tashi daga bakin umman.
Gefe baba yazauna bisa kujerar roba,yayinda umma tazauna akan y’ar tsugunno.
Abba yasake gyaran murya yace da dr.rukayya”baiwar Allah lafiya dai,bamusanki ba,maid’akina tace kinzo kinata bata tarihinki kodai kinyi ‘batan kaine.?”
Dr.ru’kayya murmushi tasaki dacewa “ko d’aya malam.kamar yanda nabawa matar ka labarina hakane,inada yaro isha’q wata’kila kaganshi anan waje,hakane?”
Tayi tambayar gami da tsatsare abba da fararen idanunta masu cike da zallah wayewa.
Haka kawai abba yaji tayi mashi kwarjini idanu,tanada tarin baiwar cika ido.
Ya’amsa dacewa”kwarai kuwa.”
Tace “gud”
“Yarona isha’q yarone nagari,yanada kyakyawan hali abin ayaba,bawai don yana d’anaba a’a,halin isha’q yasha banban dana sauran maza donshi mutum ne dayasan hakkin wanda yake tare dashi,bayada girman kai bayada miskilanci,yataso tun yana yaro tare da zahra,d’iyar kanwatace wadda Allah yayima rasuwa tun ranar data haifeta batako kalli fuskarta ba.zahra tatashi cikin maraicin uwa hakan yasaka nad’auke duk da mahaifinta baiso hakanba, nareni zahra cikin ‘kauna da aminci.
Zahra tasha’ku da isha’q saboda idan bani ko isha’q ba zahra bata yarda dakowa acikin gidanmu.