HAUSA NOVEL

MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacin da isha’q yashiga secondary zahra anyayeta,komai nata isha’q ne yakemata shine ya canja mata sunanta daga zahra adam yamayar mata *zahra adam isha’q*,tunda nake a rayuwa banta’ba ganin soyayya da sha’kuwa irinta zahra da isha’q ba.

Kai intakaice maku labari,lokacin da isha’q zaitafi Germany karatu gaba d’aya dashi da zahra saida suka kwanta asibiti.

Alokacin munzata sha’kuwace,sai dai abin mamaki sam zahra bata kula samari duk da takammala karatunta na secondry ko saurayi zuwa yayi wajenta saitace yaje yatambayi isha’q idan yayimashi to itama yamata.

Isha’q kam kullum cikin kushe samarin zahra yake,kullum cewarshi hadadd’en gaye zahranshi zata aura.”

Doctor ru’kayya ta numfasa tacigaba,

“zahra yarinyace mai tarbiyya da tsoron Allah,tanada matukar natsuwa da kamala,mahaddaciyar Alqur’ani ce.zahra wankan tarwad’ace tanada yanayin girman jiki,don duka sa’anninta zaka zata tagirme masu saboda jikinta mai saurin tofone,

Sam magana bata dami zahra ba,gwanar kwalliya da tsafta,gwanar iya kalailaye mutane da tattausan lafazi ce.

Lokacin dana lura cewar zahra da isha’q sunkamu dason junansu sainafi kowa murna,don inaganin isha’q yayi matarvda har duniya tanad’e bazaiyi kaico da itaba.

Sa’banin yayanshi dabai dace damacen kirkiba.

Isha’q baitafi karatuba saida baikonshi da zahra,

Koda yaushe suna manne a waya suna firar soyayya,

Alokacin itama takoma makaranta tana karantar likita cewarta zata gajenine.

Isha’q yagama karatunshi da sakamako mai kyau yadawo gida,alokacin aka tsaida maganar aurenshi da zahra dangi kowa yayi murna.”

Tashare hawaye taci gaba,

“sai dai kash ana saura kwana uku bikinshi zahra tatashi da matsanancin ciwon mara cikin dare wanda yayi sanadiyyar d’aukewar numfashinta duk da kokarin ceton ranta damukayi Allah ya amshi abarshi.

Alokacin isha’q haukane kawai baiyiba saboda zautuwa saida yakwashe sati guda baisan inda kanshi yakeba,daga baya zama tamkar wanda yarasa memory nashi.dataimakon Allah da addu’u a isha’q yazama normal sai dai duk barkwancin isha’q yatafi yazama tsakaninshi damu gaisuwa kawai,yaci alwashin bazai taba aureba.har yakoma ga mahaliccin shi muddin baisamu kwatankwacin zahra ba,

Tad’ora dafad’in “babu tallar yammatan daba ayiwa isha’q ba amma yace ina.shifa angon xahra ne,tausayinshi yasaka naxura mashi idanuwa,har tsawon watanni shidda.

Dayake Allah gafurune kuma rahimu saiya maido mana abinda muka rasa tsawon lokaci muke kwana muke tashi da kukan rashinta.”

Tadakata tana nazarin fuskokin dattijan biyu,

Sai dai cikinsu babu wanda yasan inda zancenta yadosa,hasalima anasu ganin wannan matsalace data dace tasanarma wad’anda suka santa bawai basuba.

Indai ba’itama tarasa nata hankalinba,su menene nasu illah iyaka suce Allah yajikan rai.

(anasu ganin ba.)

Abba yad’an numfasa yace”to dafarko muna maki ta’aziyya dakuma bakin cikin rasa y’a tamkar zahra.saimuce Allah yajikan rai,abu nabiyu daya tsayamun araina shine mudai bamusan menene ainahin dalilinki na za’barmu a matsayin wadanda zaki sanarma damuwarki ba.

Idan har kina son sanarda wani damuwarkine babu mafi cancanta kamar yan’uwanki da danginki bawai muba,da bamuda maganin dazamu iya baki domin warkewar damuwarku.

Ummata jinjina kai”wannan gaskiyane.”

Murmushi doctor ru’kayya tayi tace”malam aikune maganin matsalata,nazone da ‘kokon barata dakuma nan arziki akan ku taimakeni,kamar yanda Allah ya taimakeku idan baku za’bama d’iyarku zahra mijiba kubama d’ana isha’q aurenta.”

Daga umma har abba had’a idanu sukayi,lokaci guda suka sakarma juna murmushi,abba yace”toga dai dukkan alamu acikin abu biyi dole asamu d’aya,imma dai makuwa kikayi kokuma kema bakida hankalin.idan bayaga haka yaushe zakice inbama d’anki auren zahra.? Tukunnama haka kawai siyaa bagatatan sai ind’auki y’a inbaki saikace banida hankali.”

Dr. Rukayya taji zafin maganar abba,amma dayake ance mai nema baya fushi,saita sake numfasawa tace”kayi ha’kuri abban zahra nafahimci baka gane zancena ba sabo……”

Sauran maganar ta ma’kale a fatar bakinta lokacin da zahra ta kunno kai gidan, tana fad’in”Allah ya isa banyafe ba,muguwa azzaluma kinbugi wuta balbal har kabarinki na balbala da wuta,kuma wlh yaro ya’kara cemun zahra’u mala’ikar yara sainaci kutmar babbar saibitin babakeren buuuuu………”

Bata ‘karasaba umma takaima bakin naushi,tace “to jarababbiya ko’ina saikin nuna halin naki.”

Zahra cikin hawaye tace”to umma sai takamani tayita dukana wai don nabugi d’anta aishi yafara jana.”

Umma ta zuba mata harara”gara dayajaki aike karyace ko.dakowa zaidinga tsokana,kinzama sakarya a layi kowanne datti badole a sauke a kankiba.”

Zahra tace “wlh anjima sainayima gidansu ruwan duwatsu.”

Umma tayi tsoki”aikin da kika iya kenan fitinanniya.”

Dr.ru’kayya datayi mutuwar zaune,tasaki baki aranta tana tasbihi ga Allah wanda ya’kagi kamanni yakuma banbanta halayya.”

Nima sai naga comments xan cigaba don naga kamar buk din beyi muku dadi ba

Kuna tare da maman meenat, Aisha t. Fulani Insha Allah

[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����‍♀

By maman meenat

EDITED BY AISHA ABDULLAHI(UMMUN FAROUQ)

CHAPTER 7.

Umma taja tsoki takoma tazauna abinta,

Yayinda zahra ta cillar da jakar islamiyyar dakuma hijabi tafad’a band’aki.

Dr.ru’kayya tasauke numfashi tana kallon su umma kafin tace”wannan kuma ‘kanuwar Zahran ce kokuwa.?

Umma ta kalleta da mamaki tace”a’a itace zahran ai.”

Wani shegen gumine ya karyoma dr.ru’kayya lokaci guda tafara tsane zufa da handkerchief dake hannunta aranta tana addu’ar tafarka daga rud’adden mafarkin dayayi hajijiya da tunaninta dama kwakwalwarta.

Tad’an saita kanta kad’an kafin tad’ora dafad’in”to agaskiya dolene ku kalleni a matsayin wacce kanta ya zautu,kokuma ‘batan kai inba hakaba babu mahaluki mai hankalin dazai dubi karancin shekaru irinna zahra a gari ba ‘kauyeba yace ayimata zancen aure.”

Tad’an tsagaita tana sauke numfashi kafin tad’ora dafad’in.”adukkan zatona dakuma tunanina nayi zaton zahran babbar budurwa ce,amma don kamanni da tawa zahran tabbas suna kamanni nagasken gaske,sai dai kash wannan zahran tayi kankantar dabe kamata ace anyimata aure yanzuba.”

Sai lokacin su abba suka fahimci inda tasa gaba,

Abba yami’ke yana cewa”inace dai yaron dakeson zahran shine awaje tsaye ko.?”

Doctor ru’kayya ta’amsa dacewar”shine malam”,

Abba yafita kofar gidan,isha’q har lokacin yakafe kofar gidannasu zahra da manyan idanunshi yanason ganin ta’inda kyakyawar fuskar zahra mai kama data black Americans zata ‘bullo,sai dai sa’banin zahra saiyaga abba yafito yana sa’ba babbar riga.

Isha’q yayi saurin du’kawa yana gaida abba,

Abba ya’amsa kanshi tsaye yace”kaine isiyaku.”?

Isha’q yawaro idanuwansa masu kwarjini da haiba,yace”abba isha’q nake.”

Abba yace “afto ai duka dai d’ayane,to inason magana dakai ga mahaifiyarka can cikin gida don haka kashigo ayita a gabanka ta ‘kare.”

Gaban isha’q yabuga da ‘karfi,idanunshi tuni sun canja launi daga farare zuwa green tsigar jikinshi tabada yarrrr,aranshi yana addu’ar kada Allah yasaka yasake rasa zahra akaro na biyu bayan tadawo gareshi.

Kai yama rantse komai rintsi bazaifa rabu da sanyin idaniyarshi ba,aidukkan mai imanin dayasan tarayyarshi da zahra abaya bazaiga laifinshi don lokaci guda ya mayincema little zahra ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button