MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Abba ya kafeta da idanuwa kafin yasaki dariya dace”Allahu akbar azzawa jallah gwanin hikima,dama ku iyalan alh saifullahine,mutuminane kai mutum na gari.bazan ta’ba manta alkairinshi gareni ba.”
Yanuna umma data le’ko daga d’aki tana murmushi yace”gata kinganta nan haihuwarta ta farko kamar bazatayi ba,banida sisi a aljihuna banida kadarar sayarwa aka tsawwala mana kudin yimata tiyata dubu tamanin nad’aga gidan danake ciki zan sayar bawan Allah yaganni a asibiti ina kuka yake tambayar meya faru,na sanar mashi wlh hajiya atake ya shiga ofis din likita yarubuta mashi kudin a takaddar banki,yace ayi gaugawar ceto rayuwar saudatu.kuma yace nabishi ofis dinshi,bayan yabani takarda ta address naje shine yabani dubu d’ari nafara sarin bulawus ina kaiwa kasuwa da wannan sana’ar Allah ya d’aukakeni gashi ina cikin rufin asiri har yanzu.”
Dr. Ru’kayya tasaki
lallausan murmushi tasan mijinta yafi dahaka kaf halinshi isha’q ya d’auko.
Abba yadinga mamaki itama umma saida tasake yima Dr Rukayya godiya,
Abba ya ‘kwalama zahra kira yace maza kice ‘bakonnan na waje yazo yanzu yashigo ciki.
Tafita kai bako d’an kwali tahangoshi yajingina bayanshi a mota yayi lamo Allah kadai yasan abinda yake tunawa.
Ta dage iyakar ‘karfinta tace”kai mai motar nan,kai mayen kallon mutane kazo ana kira.”
Isha’q yaji gabanshi yasake bugawa yace “ina zuwa,tajuya zata shige gida,
Yace”jirani mana.”
Tawaigo tana ‘kare mashi kallo saikuma tabuga zani da murgud’a d’uwawu”sumbuqa sagwaigwai takashin mage da barima hada sarqa a gabanta”,
Isha’q yadafe kai “oh Allah zahra kam anya tanada cikakkiyar lafiya kuwa?”
Ita komai nata sai tasaka wauta da shirme.
Ya ta’be baki dacewa “aini nace naji nagani.”
Yashigo da sallama yasamu waje ya zauna,
Abba yasaki murmushi dacewa”taso kadawo kusa dani d’ana isha’q. “
Isha’q yakoma jikin abba yana du’kar dakai.
Abba yace”isha’q kadaiga wacece zahra,amma ahakan kace kaji kuma ka gani ko.?”
Isha’q yace “hakane abba agaba duka wannan zata dena aikowa da tashi ‘kuruciyar.”
Abba ya gyad’a kai yace”kuzama sheda ni malam adamu jafar nabama isha’q saifullahi auren d’iyata zahra ko bayan babu raina.”
Wata zabura isha’q yayi dacewar “Allah abba gaskene kabani zahra,bakuma mafarkin dana saba yi bane.?”
Abba yace”ba mafarki kakeyiba isha’q idan mahaifinka yadawo daga tafiyar dayayi za’a tsaida lokacin biki,kafinnan zakaji sharad’ina daga bakin mahaifiyarka.”
Dr. Ru’kayya baki har kunne take zuba godiya gasu abba da umma.
Takamo zahra wacce takoma gefe tana y’ar ‘kwado tace”zo d’iyata zahra kina sona,zaki zauna wajena?”.
Zahra tayi jimm kafin tace”indai kinsan gidanku akwai bene tozan zauna indinga shan dad’in bene.”
Dr. Ru’kayya tasaki dariya dacewa “kema d’akinko akan bene yake ma.”
Zahra dad’i yac tace”indai da gaske kike tokice kwarakwatsi”,
Umma tace “au zaki fara shirmen naki kenan,”
Dr. Ru’kayya dari take sosai dacewar “zahra koban rantseba bazan maki ‘karya ai.”
Tazuge jakarta tafiddo rafar y’an hamsin-hamsin tami’kama zahra”karbi kisaya sweet kinji d’iyata zahra,aibanzata ‘karama bace dana siyo maki ice-cream.”
Zahra ta kalli kud’in gami da zaro idanu tace”nidai banaso,ki’aje kud’inki bene kawai nakeso kihau dani,indingayin sululu.”
Mamaki yacika dr.ru’kayya aranta tana riyawa ashe duk wautar zahra tanada tarbiyya?
Lallai zasuji dad’in zama da’ita lokacin da ‘kuruciya ta barta.
Babu yanda batayi da zahraba,amma ‘kememe ta’ki karbar kud’in dole ta mayar a jaka.
Tanamasu umma godiya dacewar zata aikoma zahra da sweet tunda ta’ki karbar kudin.
Har zaure umma tarakata itakuwa tari’ke hannun zahra tace taje taraka mota.
Sunfito bakin lungun isha’q yana bud’e mota,idanun zahra yasauka akan jabiru wanda jiya ya ‘kalamata sheri wai taje kwad’ai gidansu ummilolo,
Bata tsaya tabi takan dr.ru’kayya ba,tafincike taruga da gudu tayi wajen jabiru wanda ya d’auko ni’kan gari akai.
Tana zuwa ta hankad’ashi garin ya zube a kwata,sannan ta cukumi rigar jabiru tafara ‘kuli-‘kulin kubura dashi Dr.ru’kayya tana daga nesa ta hango yara harsun fara zagayesu suna wa’kar”bamu rabawa sai dai mu’kara zigawa bugi cikin.”
Subhanallah cewar dr.rukayya wadda tuni tanufi inda zahra take dambacewa,
Dasauri tarike hannu zahra wadda take yayyafa ruwan bala’i,
Jin anri’ke hannunta yasaka batare data waigo ba tace “wlh kowaye yasakeni inba hakaba najuyo saina yima mutum wanka da ruwan kwatar nan,
Dr. Ru’kayya tace”oh oh zahra haka kike ashe.
Zahra tawaigo suka had’a idanu da Dr Rukayya,
Tace”shinefa jiya wai yace naje gidansu ummilolo naci garin kwaki,alhalin karya yakeyi ni aigidanmu anmafi cin dad’i abbanmu kullum da dare yanama siyomana kifi itakuma umma saitayi wanka taje can d’akin abban mu har…..”
Dr. Ru’kayya tace “ya’isa zahra nasan kunacin dad’i ai,amma kiyi hakuri bakiga kin sakashi kukaba.”?
Tace”aima wlh danban shillirashi nayi mashi fad’an y’an chanis ba,dasaikinga nafasa mashi baki.
Rannan ma damukayi fad’a da hinde saida nakusa ‘kwa’kulo mata kunne,itakuma irin fad’an sharuhkan nayi mata.”
Dr. Ru’kayya ta jinjina kai tana kallon isha’q wanda yayi tsuru,baiso mummy tagane halin zahra yanzu ba.
Yasanta dasakama ranta damuwa dayawa,
Tajuya ga zahra dake cema yaron”yaro zan kamaka,zamuje lungun bata kashi saina gurje maka baki da kashin kaji ha’koranka sun zube,banza latas karas kabeji masu kwana abakin titi d’an kabewa mai…”enough pls.”
Dr. Ru’kayya tafad’a ranta a’bace”kewai waccce irin yarinyace,ahaka kikeson inje dake gidan bene kina dakarmun d’iyan ma’kota.tonikam ba’a haka dani,idan bazaki sake haliba lallai zan ‘bata dake sam banason masifa kin ganni nan.”
Zahra tayi tsit,sannan tace”nadena ai.”
Dr. Ru’kayya tayi murmushi dacewa “gud girl”
Tashafi gashin kanta,
Tayima yara y’an kallo tsawa kowa ya kama gabanshi.
Itama mota tashige tana d’agama zahra hannu,lokacin gaf da magrib.
Motarsu na ‘bacewa zahra ta hango su ummilolo da sauran ‘kawayenta,taje suka kashe “tace yara albishirinku?”
Duka suka kasa kunne dacewa”goro fari ‘kal”
Tarage murya sosai”amanatun amana wa’azabatun azaba,idan kuka tona taciku,kun yarda?”
Duk sukayi tsuru,
Tace “inbaku yardaba shikenan.”
Sukace “munyarda zahra,”
Zahra ta tafa hannaye dacewa”yara kuka gayama wani saina dirji baki ehe.”
“amanatun lauratun ‘kwan kiyashi,yara ankusa yimun aure.
Duk suka zaro idanu waje suna kallonta sun sandai ‘karya ba halin zahra bace,don sam tsage gaskiya take komai d’acinta.
Ummilolo tayi karfin halin cewa”mai ‘karya”
Zahra ta’amsa da “d’an wuta abishi da duka har wuta lantarkin babalo da an kyasta sai wuta.”
Duk suka ce”yeeeee dagaskene.
Nanfa aka zauna ana labarin aure,ummilolo tace “tab ashe zahra ke zaki dinga dafa abinci kiyita ci dayawa cikinko yayi ‘kullumeme saimuga zahra ta haihu.”
Sauran yara suka kwashe da dariya,
Zahra ido ya raina fata tace”ai sai in’ki cin abincin,inyita shan ruwa kawai.”
Uwande tad’an fisu wayewa tace”kai wlh ance bacin abinci kesa mutum ya haihu ba.”
Duk suka zaro idanu sukace “to menene”?
Tace inkun yarda amana,
Sukace sun yarda.
Tace”wlh yara idan kuka yarda namiji ya ri’ke maku hannu ya luliya tafin hannunku saikuga ciki yafito ‘katoto,”
Zahra data gama tsorata tace”lalalala aikuwa Allah yasoni ban wasa da maza.”