MIJIN-KWAILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Daga nan aka rufe cafta,akace atafi satar kifi,wajen y’an kifi.
Haka kuwa akayi xahrace gaba sungama tsara plane na yanda zasu saci kifi,
Suna zuwa saitin wani mai kifi yakasa a faranti yana tsaye gaban kifinshi,
Zahra nazuwa wajen saitin kifin ta yanke jiki tafad’a akan farantin kifi,
Sauran yaran duk sukayi fuskar tausayi”wayyo zahra sannu,”
Mai kifi ma fad’i yake subhanallahi sannu yarinya.
Zahra ta bala riga akan kifi ta dumbuji uku,
Sannan tari’ke ciki”wayyo cikina ummilolo zoki tadani.
Ummilolo itace mai hijabi,dan haka tana zuwa zahra ta ‘kunsa mata kifin a hannu,
Tasaka ariga,
Suka mi’ke suna kakka’be jiki zahra na d’angyashi.
Kamar ance maikifi ya kalli kashin kifinshi yaga anyimashi rani,
Yabisu aguje yana ‘kwala masu kira,
Sukuwa ‘kafa menaci ban bakiba,
Tuni sun sata.
Maikifi saida yayi Allah ya’isa saboda balagaggun kifayen suka d’auke,gashi ranar ba ciniki.
Awani lungu suka ma’kale zahra ta’amshe kifin ta finfincinar masu,tana la’kume sauran.
Uwande ta kalli d’an nata,taga na ummilolo yaninka nata biyu,tace”gaskiya anyi son kai,na ummilolo dayawa namu kad’an”.
Zahra takaima bakin duka tana harararta”sannu mara gode Allah,da kud’in babanku aka saya kifinne,”?
Uwande tayi gum tana mamular kifin da aka bata kai da bindi.
Nan sukayi gaba,
Dai-dai kwalbatin y’an ganda suka hango wata budurwa da saurayi ana tafe ana rangaji suna gogar kafad’un juna,
Ummilolo ce tafara gani ta lakaci zahra,duk suka ware idanuwa suna mamaki.
Zahra tace”aje ajanye gyalen tsinanniya,”
Nanfa kowa tacire takalmi suka ma’kala a jijiyar hannayensu,suka d’age zani sama.
Saida budurwanan tazo saitin majalisar masu ganda,zahra tayi wuf ta fizge gyalen dake kafad’ar budurwar,
Suka auna aguje,budurwar tarasa yazatayi,ta waiga dacewa”honey dallah kabisu ka’amso man gyalena,kaga kayan jikin rabin ‘kirjina duk awaje yake.”
Saurayin yace”tabd’i,sarai nagane yarannan masu gudu kamar barewa,nida rannan gaban idanuwana suka janyema wata budurwa zani,yaseen da rarrafe tashige gida,camon ki kare wajen kawai mutafi asfa gayu d’innan kingane ai “
Ran budurwar ya ‘baci kawai saita tsugunna ta fashe da kuka,
Me mutane zasuyi banda dariya da ihu…
*Nima nadara,nabi bayan zahra balbali zahra bala’i ta’ba d’aya kaga goma*
KUNA TARE DA MAMAN MEENAT, INSHA ALLAH
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����♀
BY MAMAN MEENAT
EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN FAROUQ, HYDR)
Muna miqa saqon ta’ axiyan Hamma umar Allah ya jiqan shi yayi mishi rahma yasa mutuwa ta xama hutu a garesh, muma in tamu taxo Allah kasa muyi mutuwar shahada)
Chapter9.
Daga wajen tonon fad’a su zahra basic zame ko’inaba sai gida,saboda lokacin tuni angama sallar magirb,
Da sand’a tale’ka cikin gidan tace “inshigo’”
Umma dake ninke kayan da abba yacire dazu ta harareta dacewar “dawwama anan,har mahadi ya bayya,”
zahra taahigo kanta tsaye,tad’auki buta tafara alwalar magrib umma bata tankataba.
****************
Hadadd’en saurayin dake sanye cikin ‘kananun kayan riga shirt dakuma wandon jeans kirar kamfanin Gucci,akwai kwatsetsen takalmin kafarshi mai shegiyar tsada gordon rush,
Face dinshi manne da space na Prada,watch na hannunshi dolce jikinshi manne da mayen turaren American crew.
Sumar kannan nashi ka rantse na macene saboda gyara da kula kai infarct isha’q ‘karshene akan tafin hannayenshi kawai yakan kashen kud’i masu yawa,ha’koranshi kuwa akoda yaushe suna walwali da daukar idanu saboda time daya ware musamman domin su yakan je wajen wankin hakora lokaci zuwa lokaci.
Hatta da tafin kafar isha’q baya barinta face ya tsaftaceta da mayukan dake tsaftace ‘kafa dasakata taushi.
Yanda yake wana steering kadai abin kallone,duk inda ya gifta mutane kan bishi da idanu musamman motar dayake tu’kawa new modern ce kirar mazda mx-miat abin saiya bada wani styles na daban.
Adai-dai kofar gidan sadiq ya matsa horn mai. gadin yale’ko dakai lokaci guda ya wangale get din yanama isha’q barka da zuwa,
Yafaka mota inda aka tanada don hakan,lokaci guda yazaro wallet d’in dake manne abayan aljihun jeans dinshi,yafiddo 2thousand yamikawa mai gadin,baijira sauraren godiyar damai gadin keyiba yayi gaba abinshi yana wana keys na motarshi.
Dai dai shiga harabar gidan yahad’u da hindu matar sadi’q da tsohon cikinta tana ganinshi tasaki murmushi”yau makuwa kayine isha’q yau agidan,”
Yasaki simple smile nashi kafin yace”yakike ya jiki kuma.”
Tayi gaba tashige falo tana fad’in”banacin mi’ke,”
Bayanta yabi ya nitse cikin manyan kujerun dasuka zagaye falon yadauki remote yana canja channel daga Bollywood zuwa dstv yana searching ‘kwallo,
Hindu tuni tacika gabanshi da kayan sanyi tasani yafi shan hollandia ko malt sune best drinks nashi.
Ya fincine hancin malt na gongoni yana zubawa a glass cup yana tambayar”ina mutumina ne.”?
“yana jinka yanzu zaka ganshi yafito wankane yana shiryawa.”
Isha’q yad’an dara,dacewa kice nazo asa’a dama tad’i zai rakani.”
Idanu hindu ta fiddo waje”to gaskiya bari yafita ba,haka kawai wata budurwar ta kwaceman shi.”
Tafad’a tana turo baki da alamar fushi.
Isha’q dariya sosai yakeyi yanacewa”aigara kishirya don mutumina hudu zaiyi,”
Maganar sadiq ta katseshi”a’a banganeba,wato kai ka’ki aure shine zakazo ka ‘killen dannawa auren ko,”
Yafad’a yana dariya lokaci guda yana zaunawa kan hannun kujerar da isha’q yake kai.
Yami’kama isha’q hannu suka tafa duk suna dariya
Isha’q yace albishir fa nazo inyi maka,
Duk suka bishi da idanu sunason jin abinda zai fada masu,
Yasake kora maltina yana kallon sadiq wanda ya tsareshi da idanu,
“anbani zahra abokina,daga yau nakoma angon zahra “
Wata zabura hindu tayi”nice to hear isha’q seriously pls dagaske kasamu zahra?”
Isha’q ya saki dariya lokacin da sadiq yakai mashi duka yana fad’in abokina bakada mutunci wlh,wato saida ka rikita masu yarinya da salon wankanka ko?”
Amma duka sati biyu da had’uwa ace har anbaka saikace kaza,koda yake nasanka gwanin iya sarrafa soyayya but natayaka murna sosai abokina aikawai daga wannan wankan muwuce inga amaryar nan.”
Hinduma fad’i take “nayi murna isha’q kaga nasamu ‘kawa,”
Isha’q ya sauke numfashi.
Headache wlh typin din bayamun dad’i kuyi hakuri pls,
Tun d’azu nakeson typing amma kaina yana matsamun dafatan zaku gafarceni.
Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����♀
BY MAMAN MEENAT
EDITED:AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ)
Wannan shafin naku ne masoyan mijin kwaila, sai daku xamuji dadin cigaba da rubutawa in baku bamu hadin kai rubutun baxamu ji dadin yiba. Maman meenat nayi muku fatan alkhairi, t. Fulani ma baa barta abaya ba��
Chapter 10.
Isha’q yad’an murmusa yana shafar sumar kanshi,
Sadiq yace “Allah am serious abokina,yakamata inga wannan zahran tauraruwar mata.
Isha’q dake mi’kewa tsaye yana tafiya abinshi yana bashi amsar”zaka ganta very soon but not today,”
Hindatu tasakeyin dariya”isha’q bani phone number nata my be mu saba kafin tazo gida,idan dai tanada son jama’a.”
Gaba yayi abinshi yana bata amsar”kidaice zaki koyamata gulma da kitififi kawa,”
Duk sukayi waje da sadi’q suna mata dariya.
Ajikin motar isha’q suka tsaya,sadi’q yana tambayar”abokina kamata yayi ashirya komai harkar girma kasan y’ammatannan yanzu suncika saka bidi’a a al’amarin aurensu.”