MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda suka dau hanya yake basu amanar farida,tare da kara jaddada musu irin son da yake mata,da kuma irin dagewar da zaiyi ya yi karatu. Nan mahaifinsa ya kara masa tuni da ko hutu bazai zo ba ,shi da nigeria sai ya gama karatu.
Ya kalli mahaifin nasa yace,” nasanj baba,ba zan dawo ba sai na cimma manufata da burinka da yardar Allah.,”
Mama da shamsudden tarw da kaninsa. Lukman da mahaifin farida suka masa rakiya wanda mahaifin sa kuma tare zasu tafi sai ya kaishi sannan ya dawo .
Bayan sun isa zasu shiga jirgi kafin ya kalli mama yace,
” in farida taji na tafi zatayi kuka,ki lallasheta sosai kinji mama ?
” To deeni ,zan lallasheta,sai dai kai kuma wa zai lallashe ka?
Idanunsa suka kada sukayi ja ,ya yi saurin kai da kai ya ce,ba komai zan lallashi kaina”
Shamsuddeen yayi saurin rungumarsa yana lallashi har da lukman a masu bashi hakuri,dakyar ya iya danne zuciyarsa ya juya ya tafi. Har ya bar ganinsu yana kara maimaita musu ,mama,shamsu,lukman ku kula min da farida ,na baku amanar farida.Mama tayi karfin hali kamar zatayi kuka tace .
Mun rike amana deeni,Allah ya kai ka lafia,ya kare ka”
Ameen” ya amsa,sannan ya shige suka tafi.
Su mama basu bar filin jirgin ba har sai da suka ga tashin jirginsu sannan suka kama hanyar gida,dukkan su jikinsu a mace,zuciyar su cike da kewar deeni.
Suna isowa kofar gida kuwa sukaci karo da farida ra hada kai da gwiwa tana ta zabga kuka,,tun daga wannan lokacin mama tasoma aikinta na lallashi. Ta ja hannunta suka shiga ciki,ta dinga lallashinta tarw da kalamai masu dadi da kwabtar da rai,ta nuna mata deeni ya yi haka ne saboda kada ya ganta ya karaya ya kasa tafiya.
“” farida kiyi masa addua tare da kara masa karfin gwiwa har ya samu nasarar yin abinda ya kai shi ya dawo lafiya kuyi aurenku kinji ko ?
Ta girgiza mata kai ,. Naji mama ,na gode,zan jure in Allah ya yarda.
Yawwa farida ,shiyasa nake sonki,akwai biyayya da jin maganar na gaba da ke. Allah ga miki albarka.
Ameen mama” . Ta fada murya a sanyaye. Ta mike tayiwa mama sallama ta nufi gida zuciyarta cike da tsananinson deeni,da kuma kewar sa. Ita dai bataki ta dawo gidan da zama ba tayi ta zama a dakin deeni tana kallon inda yake rayuwar sa tana jin dadi ,sai dai ba halin yin hakan sai dai ta dinga zuwa,ya zama dole tayi hakuri da rashin Deeni……
Sabo shi akewa kuka,inba so kuma baza’a yo ba ,,ma’anar so a zuciya ku rike amana ku kau da zan ba….. …????????????????????
Byee
Sumy luv????❤????❤????
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Writting bySA’ADATU WAZIRI GOMBE
=================== GIDAN NOVELS ====================================
17
Washegari bayan sun gama breakfast ,Alh. Umar tare da shamsu da likman duk sunyi shirin fita office yayin da lukman makaranta zai tafi.
Alhaji ya kalli shamsu dake shirin mikewa yace ,
” ka zauna ina da maganar da nakeso muyi da kai da mahaifiyarka ,kai kuma lukman kaje driver ya ajiyeka a makaranta””
Nan ya mmike ya fita ,yayi da shamsu ya bar dining table din ya nufi tsakiyar falon kamar yadda yaga mahaifinsa yayi yana tunanin to wacce magana Alhaji zai yi da shi haka?
Mama ta iso cikin falon ta zauna a kujerar da ke kallon tashi , tace .
” *Alhaji muna sauraronka ,wace magana ce haka?
Ya gyara zama yace,inaso ku saurare ni da kyau da kunne basira,kwanakin baya kafin deeni ya tafi karatu munyi wani shirri ni da mahaifin farida. Maganar gaskia bamu shirya maganar auren deeni da farida ba ,sai shamsuddeen da farida ,haka kuwa bazai yiwu ba har sai deeni ya tafi karatu ya bar kasar nan,fatiyarsa kuwa abu ne mai wuya in ba har yaji za a aura masa farida ba.
Maganar gaskia mahaifin farida bai yarda da barin ‘yarsa tayi jiran shekaru biyar ba,ni kuma ban yarda da aurawa deeni mace ba tare da ya gama karatu ya mallaki hankalin kansa,yasan ciwon kansa ba daga farida har deeni soyayyar yarinta ce ke damun su,dukkan su basu san ciwon kansu ba ,ba yadda za’ayi mu hadasu aure da deeni .
Sai dai maganar ta mana amfani , na sami deeni ya nutsu yana karatu,kafin shekara biyar din nan zai shiga ruwan hankalinsa,ya nutsu ,zai mance farida idan yaji dan uwansa ya aureta ya fara sabuwar rayuwa. Itama kafin nan zata gane shamsu shi ne wabda ya dace da ita.
Babban dalilin kulla wannan aure shi ne ,na farko dacewar farida da shamsu,tana dai dai lokacin aurw shima haka. Sannan Nuraddeen ya bata mata lokaci ,tun tana karama bata bawa wani saurayi dama ba sai deeni,ba zan so yanzu da ta tashi aure ya zama tamkar deeni ya yaudar ta ba. Yanzu bata da wanj,haka bazan so kuma nahaifinta ya aurar da ita ga wani wanda bai dace da ita ba ,wanda bazai bata kulawar da jindadin da ya dace da ita ba .
Farida tamkar diyar cikina na dauke ta ,shiyasa zan damka amabarta ga dana wanda na yadda dashi ,na amince masa. Inada tabbacin shamsuddeen zai bata suk wata kulawa da kauna matsayin mijinta. Sannan burina da naki zai cika na ganin farida ta zama surukar mu,zamu hada jini da zuri’a dasu ,zata haifa mana yan jikoki. Da Shamsuddeen da Nuraddeen duk abu daya ne a wurin mu,don haka mun yanke hukunci a watan sha biyu za muyi auren su december ,sai ku soma shiri.”
Yana gama fadi ya mike zai fita,,hajia tayi saurin mikewa cikin girgiza da firgitar jin maganganunsa hade da mamaki,yayin da shamsuddeen kansa na sunkuye,maganar mahaifinshi ta mugun kadashi da bashi tsoro. A kullum yana yiwa mahaifinshi abinda yake so,amma wannan karan zasuyi tsiya irin wadda basu taba yiba ,don kuwa ba zai taba aurwn macen da kaninsa,jininsa,dan uwansa ke ciwon so ba.
Hajiya ta sha gabansa,ta tsare shi da ido ,ta ce
” wacce irin magana kake ne me kama da ta yara? Ba na tsammanin deeni da farida yara ne ,sai dai kai da mahaifin farida ne tunaninku irin na yara. Kuna nufin kuce min kun yaudari yaran ku kenn? Kun yiqa yaranku karya kuna iyayensu ? Kana son fada mun zaku wargaza rayuwar yaranku da hannun ku ?
Na yarda na amince ina son farida matsayin sirika ,haka kuma babu bambanci tsakain shamsu da nuraddeen a wurinmu. Sai dai fa inaso kasani akwai bambanci tsakanin deeni da shamsudden a wajen farida . Zuciyarta da ruhinta gaba daya deeni suke so,deeni suke muradi.
Wannan maganar da ka kawo bata wasa bace,kanason haddasa gaba tsakanin yaranka ,ka dauki abinda daya take matukar so kabawa daya? Shamsu yace kamaka yanason farida ne ko ita faridan ta fada maka zata amincd ta auri shamsu ? Kasan ko yawan soyayyar da ke tsakanin farida da deeni?
Wannan ba damuwa ta bace ” ya fada cikin daga murya d bacin rai,ya ce
” karki zara maganganunki zasu canja min niyyata da ra’ayi na,ba shawararki nake nema ba ,ina fada muku ne dake da danki ku soma shirye shiryen biki,banason sake jin wani raayi naki ko na wani musu akan maganar nan “” ya kalle shamsu da kansa yake sunkuye , ya kira sunansa.
” Kai shamsudden ,dago kai ka kalleni nan ” yayi saurin dago kai cikun tashin hankali da kuma tsorata da yanayin mahaifin nasa, yace .
Na maka zabin mat matsayina na mahaifinka ,ina fata ba zaka bani kunya ba idan har na isa da kai,kuma na taba maka wani alfarma a duniya a matsayina na uban da ya kawo ka duniya,to ina so kayi biyayya ga maganata ka auri farida, ka rike ta hannu bibbiyu da amana . Ni nan mahaifinka nina baka amanar farida kanaji na ? In kuma kana ja to inji ”