HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya sunkuyar da kai muryarsa na kyarma yace ,,naji baba ,na amince,na maka biyayya,bani da ja ,”

Mahaifin nasa yayi murmushi , ya ce naji dadi ,Allah ya maka albarka ,Allah yasa ka gama da duniya lafia,Allah yasa ‘ya’yanka su maka biyayya kamar yadda ka mun “”

Ya kalli mama cikin bacin rai ,ya ce.

Saura wani yayi garajwn sanar da deeni abinda ke faruwa,ko ma waye ne zai fuskanci mummunan fushi daga gare ni””

Yana gama fada ya juya ya fita,ya bar mama da shamsu cikin balain tashin hankali.

Haka kai yayi da gwiwa tamkar wani karamin yaro yana kuka ,hankalinsa ya mummunan tashi . Dum yadda ya kai ga kin aurwn masoyiyyar dan uwansa bai isa ya ki bin umarnin mahaifinsa ba,bashi da karfin gwiwar kin yiwa mahaifinsa biyayya ,ya zama dole ya bi umarnin mahaifin sa kamar yadda ya ke masa tun yana dan kankaninsa.

Mama ta tsinci kanta cikin rashin hankali da kaduwar da itama tana bukatar mai lallashinta balle ta lallashi shamsu.

Sai dai shamsu ya kas jurewa har sai da ya matsa gabanta yana kuka yana fadin .

Mama ki taimake ni kiyiwa baba magana ,ya za ayi in auri farida yarinyar dana shaida soyayyarsu da kanina da nake matukar so ? Tun suna yara ni na san irin soyayyar sa sukewa juna ,mama ya za ayi in jefa kannena biyu cikin tashin hankali da bakin cikin rabuwa da juna? Ya za ayi in raba su ta hanyar auren farida ? Mama da wane ido zan kalli Deeni?

Kasa magana tayi saboda bata da abinda zata iya fada masa illa ta taya shi kuka ,hawaye taji yana gudu a fuskarta,tausayin yaran nata duka biyub ya kamata.shin mahaifin su bashi da zuciya ne da bai tausayinsu ? Ko baya hangk cewa zai hada gaba da fitina a tsakanin yaransa?

Da kyar ta iya budar baki tana lallashin sa tare da bashi hakuri cewa basu da yadda suka iya ,saboda mahaifinsu yafi karfin su duka .

” ka dage da addu’a in haka shi ne mafi alkhairi Allah ya tabbatar ,in kima ba alkairi Allah ya warwre shi.

Mama ina alkairi a auren cin amana ? Mama kin tuma har deeni ya shiga jirgi yana bani amanar farida ? Mama yaya deeni zai dauke ni in yaji na ci amana na auri macen da take rayuwar sa,farin ckin sa,koman sa ?

Tayi murmishin karfin hali tace, kar ka damu ,Allah na nan ,kayi kokarin mai da al’amarin ka gare shi,haka nan deeni ya san halin mahaifinku,zai fahimci ba kayi auren ne da niyyar cin amana ba .

Shamsu ,yana da kyau ka  kwantar da hankalinka ,kasawa kanka aurwn farida ko baka so,ka tursasawa kanka da zuciyarka,saboda tun da mahaifinka ya lashi takobi sai ka auri farida to ba makawa si ka aureta ,sai wani ikon Allah,,””

Nan ta shige ciki ta barshi a wurin a durkushe ,abin duniya ya masa zafi. Daga karshe ya mike ya koma dakinsa,office din da bai fita ba kenn. Ranar mahaifinsa ya masa wannan uzurin ,don yasan halin da ya tsinci kansa . Ya bashi dama yaji da kansa da zuciyar sa.

Haka mama ta koma daki hankalinta tashe ,idonta rufe tana addu’a da fatan kar wanan abu ya zama sanadin wargaza kan ‘ya’yanta ,yayin da tausayin farida da deeni ya cika mata zuciya . Tabbass zasu fuskanci tashin hankali,sai dai zata taya su da addu’a Allah ya basu juriya……

 

Shin farida zata amince da wannan sabon al’amarin ??

 

Yaya deeni zaiji idan ya riski wannan bakin labarin ??

 

Ga masu binmu sai ku biyomu a wannan lambar 08029350366  dan jin ra’ayoyinku ,,kofarmu a bude take …

 

Cigaban labari kuma yanaga yawan ra’ayoyinku ,domin shine zai tabbatar da kuna binmu da gaske kamar yadda kuka fada..mun gode

Sumy luv????????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤

16

Sati guda da tafiyar Deeni komai ya mike masa,ya gane yadda wurin yake. Gida guda mahaifinsa ya sama masa kusa da makaranta,bai samu wata matsala ba ya fuskanci abinda ya kawo shi,ya hau karatu gadan-gadan . Ganin ya mike yasa mahaifinsa ya yi sallama da shi ya dawo gida nigeria don fuskantar nasa ayyukan.

 

Ya dawo hankalinsa kwance,bashi da wata matsala ganin deeni ya mike kuma da gaske yake,wannan ya matukar bashi kwanciyar hankali.

Duk da Deeni yana matukar kewar farida,amma ya daure bai mata waya ba saboda gudun mai da hannun agogo baya,a duk lokacin da zai ji muryarta dukkan wani kokarinsa zai iya komawa baya,hankalinsa zai tashi yaji yanason komawa ya ganta. Don haka ya daure,ya hora zuciyarsa da rashinta na tsawon lokaci ,sannan ya kirata.

Da farko ta nuna masa fushinta na kyaleta da ya yi ba waya da kuma tafia ba yayi ba tare da ya bari ta masa rakiya ba . Sai da ya jira ta gama mitar sannan ya ja dogon numfashi ya ce.

“” farida na,farida matar Deeni . Kinsan deeni da irin son da yake miki ,trust me inada da dalilina na yin haka””

” Na sanj Deeni ”

Ta fada murya kasa kasa,ta kara da cewa.

” ina kewar ka ne kawai Deeni,kasan na saba da kai da soyyyarka ,Deeni ba dadi da baka nan ”

Yi hakuri farida,zai zama tarihi”

Ya canja zancen ta hanyar zolayarta da cewa,

Nasan duk randa kikazo America kika ga dogon gini rudewa za kiyi ,saboda farida ta yar kauye ce ”

“” Ta turo baki tamkar yana ganinta ,ta ce.

“” kai da bamu ga ka rude ba ,saboda kaima dan kauyen ne ai”

Yace oho dai ,ni dai yanzu na zama dan birni na barki”

Dariya sukayi duka,sun jima suna hira suna bawa juna labarin yanayin da suka shiga da kuma halin da suke ciki. Ya bata labarin yadda yake matukar jin dadin karatun sa a yanzu,,yake kuma ganewa,saboda yadsa aka saukaka musu shi,sabanin yadda yake a nigeria.

Itama ta bashi labarin makarantar high islam da mahaifinta yasa ta koma,saboda yaki barinta tashiga university sai dai tana karuwa sosai ta fuskar addini a wannan makarantar ,tana kuma ganewa ,tana jin dadin karatun addini.

Sunyi sallama da juna ,suna yiwa juna addu’a da fatan alkairi,zuciyoyin su cike da jin dadi da farin cikin magana da juna

Wasa gaske deeni ya mike da karatu har ya saba da rashin farida ,yana kiranta wani lokaci sau daya a wata ,saboda dagewa da yayi ya fuskanci karatun dake gabansa,soyayyar farida na kara masa karfin gwiwa. Haka itama farida kullum suka yi waya sai ta karfafa masa gwiwa da kara jaddada masa soyayyar da take masa .

Itama haka tayi sabo da ba sa waya da deeni sosai sai lokaci lokaci,kuma ta fahimci dalilin sa don haka tayi masa uzuri ta fuskanci nata karatun tare da musu addu’a.

*      *       *      *      *

Zaune yake a falo shi daya yana kallon labarun karfe tara ,Alh umar kenan ya mai da hankalinsa gaba daya kan jin abinda ke faruwa a kasar tamu, lokacin Alh Ahmad ya masa sallama ya shigo falon.

Ya mike da sauri yana dariya ya tare shi saboda muhimmancin da yake dashi  a wurinsa,yana matukar girmama shi,da kuma dangantakar su ta makwabtaka.

Nan ya nuna masa wurin zama tare da sawa a kawo masa abin sha. Suka sake sabuwar gaisawa,suka dan taba hirarsu data shafi kasuwanci da kuma kasar gaba daya. Tare suma kalli labaran suna sharhi akai.

Bayan sun gama Alh Ahmad ya kalle shi ya ce .

“” ya labarin deeni kuwa ? Duk da dai muna waya da shi amma mun kwana biyu bamuyi waya ba ,yana lafia ko ?

Alhaji yayi murmushi yace ,lafia kalau,ya maida hankali yana karatu yadda ya kamata. Ina kara maka godia bisa taimako da hadin kai da ka bani “”

Alh.Ahmad ya yi daria ya ce ,”Ai deeni ya dana ne,kamar yadda ku ka riki farida kamar ‘yarku haka nima na riki deeni””

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button