HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya kara kallon sa da kyau yace,,”yanzu ma maganar yaran nan ce ta kawo ni,kan maganar da mukayi kwanaki ,kaga tsahon wata tara kenab da tafiar deeni,komai ya mike masa ya soma fuskantar karatunsa da gaske,haka nutsuwa tana kara shigar sa,din haka inaga lokaci yayi da zamu fito mu bayyanawa yaran nan da iyayensu mata manufar mu da kuma dalilinmu ,kaga watan sha biyu nakeson auren yaran nan ,kuma har da farida ciki,kaga yanzun wata biyu ya saura ,gara mu sanar dasu su shiryawa maganar auren tun wuri;””

Alh. Umar ya sauke ajiyar zuciya ,yace.

” kayi gaskia tamkar ka shiga cikin zuciyata ne,inada shirin maka maganar sai ka rigani ,inaga yanzu abinda za’ayi ,ka kira farida da mahaifiyarta kayi musu bayani,haka nima nan zan kira nawa iyalin nayi musu magana. Abinda nakeso da kai shi ne,mu tabbatar musu da maganar da muke fada UMARNI ne muke basu ,maganar mu doka ce a gare su ,dole su bita ba wai ra’ayin su muke nema ba. In munyi haka zai zo mana da sauki,amma in muku nuna ra’ayinsu muke nema zai sa mu sami matsala ,zai zamana tamkar mun vasu damar kin bin abinda muke so ne ”

Alh Ahmad yayi dariya,yace,,kayi gaskia ,maganarka abin dubawa ce. Inaga gobe in Allah y kaimu zan kirasu muyi maganar,zaka ji yadda mukayi da su”

Alh. Umar ya amsa da,nima in Allah ya yarda goben zanyi magana dasu,sai mu duba ranar da ta dace mu tsayar da ranar biki”

” To shikenn ,Allah ya kaimu goben ”

Da wannan. Maganar suka yi sallama ,tare da yiwa juna sai da safe akan zasu hadu washe gari bayan tashi daga harkokin su da yamma za su hadu……….

SHIN IYAYEN SU SUN YARDA ZAA AURAWA DEENI FARIDA NE KAFIN YA DAWO ????

WANI IRIN FARIN CIKI DEENI ZAI YI IDAN YA SAMU LABARIN AN DAURA AURENSHI DA FARIDA?

MUJE ZUWA ????????????

.

sumy luv????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Cpoied by SUMAYYA SA’AD❤❤

18

Kamr yadda ta kasance da su shamsu haka ta faru tsakanin farida da mahaifinra da mahaifiyarta. Tunda ya fara musu bayanin manufar sa bai kai ga karasawa ba ma farida ta mike ta tare shi da fadin .

“Abba ba zan taba airen wani namiji a duniya ba inba deeni ba ,nayiwa deeni alkawarin kaona da zuciyata,zuciyata deeni take matukar so,don haka Abba kabar wannan maganar ta yaudara. So kike inci amanar deeni ? Kuma Abba bazan iya rayuwa da wani ba in ba deenni ba ,Abba ka taimakeni ,gara min mutiwa ta daa rasa deeni”

Mikewa yayi ya sharara mata mari sai data ga taurari.

” yarinyar banza mara kunya” ya fada yana huci.

“. Ke har kin isa kiyi jayayya dani ? Yaushe kika koyi rashin kunya ? Kin san me kike fada kuwa ? Har kina fadan mutuwa da iliminki da hankalinki ,kin san meye mutuwa da har kike ikirarin gara miki mutuwa ? Me aka miki me zafi a duniyar nan haka ? Kuma ko me ya miki zafi babban sabo ne kice kin gwammaci mutuwa . Miji dai nike da hakkin zaba miki shi ko ? Ba ke ba ,don haka na zaba miki shamsu ,inkin isa  in na daira miki aure da shi ki ki zama a gidansa ,sai in san ke cikakkiyar mara kunya ce ”

Ta durkusa har kasa tana kuka ,baba kayi hakuri don Allah kar ka rabani da masoyi na deeni,Abba deeni shi ne rayuwata ,ban taba tunanin wani a matsayin mijina in ba deeni ba,Abba ba zan iya biyayyar aure ga kowanne namiji ba sai Deeni ”

Ki daina bata yawun bakin fa, shamsu dai kin aurwshi kin gama ”

Ta miki , Abba bazan auri shamsu ba sai dai ka kashe ni ”

Ya kalleta cikin bacin rai ,ya ce

Baki isa ba ,idan kinason zama a gidan nan matsayin diyata ,idan kinaso mahaifiyarki ya cigana da zaman aure a gidan nan kar ki sake musu dani akan maganar auren ki da shamsu””

Maganarshi ta karshe ya mugun girgizata ,tabbas bazataso auren uwarta ya kare akanta ba . Ya kalleta,kina da zabi ,ko naki auren ko na uwarki,ina saurarwnki”

Cikin tsananin kuka da bakin ciki tace ,Abba na amince ba don inaso ba ,sai don umma,”

Ro banason sake jin komai ko wani musu akan maganar nan,munyi mun gama . Haka ko da wasa ban yarda idan kunyi waya da deeni ki sanar masa ba ,balle ya dawo ya daga mana hankali. Sai ki soma shirye shiryen biki”

Ya kalli mahaifiyarta da ta bude baki tana sauraron su cikin tsananin mamaki ,ta rasa abin fadi. Tabbas namiji halinshi sai shi .

Yace ,ki rubuto mun duk abinda ku ke bukata na bikin farida za’a siyo shi,cikin december za’ayi auren ”

Yana gama fadi ya juya ya fita ba tarw da ya saurarwsu ba,haka farida ta zauna a wajen ta sa hannu akai tana ta rusar ihu tamkar wacce aka cirewa ido ko ta easa uwarta ko ubanta.

Mahaifiyarta dai bata da yadda zatayi sai lallashi da nasiha ,sai dai tabbas dole ta taya ‘yar ta kukan rashin babban masoyinta . Sannan karin tashin hankalin ma wai ta auri dan uwansa?

Nan ta rungumo ta a jiki tana lallashi ,tana mata addu’a.

‘Farida Allah zabi mafi alkairi”” tana fadi tana hawaye ,basu ankara ba sukaga jama’ar gidan duk sun cika falon kowa na tambayar meya faru ? Duk wanda yaji abinda ya faru sai ya tausayawa farida gami da juyayin wannan alamari,saboda kowa yasan karfin soyayyar dake tsakanin Deeni da Farida.

Haka farida ta wuni kuka ,ba ci ba sha,bakin ciki da takaici ya cika mata zuciya,tsananin kewar deeni da kaunarsa taji yana ratsa ta. Hankalinta ya mummunan tashi ,taji kwakwalqarta na juyawa tabdinga jin kamar zata yi hauka saboda kwakwalwarta ta kasa amince mata da hukuncin da mahaifinta ua yanke akanta,ta dawo tamkar wata mai jinni.

Ta mike da gudu ko dan kwali babu akanta ta nufi gidansu deeni,kai tsaye ta wuce dakin shamsu tana kwala masa kira.

“. Ya shamsu”” ya shamsu ka taimake ni ”

Ta sameshi ya kasa tsaye ya kasa zaune yanata zagaya dakin ,shima abin duniya ya masa zafi. Bai ankara ba ya ganta a dakinsa ba zata tamkar an jehota ,ta sunkuya ta kama kafafunsa.

 

Ya shamsu ka taimake ni kace baka sona,kace ba zaka aure ni ba . Yaya shamsu kaima ka sani ko ? Kasan deeni nake so,kasan ba zan iya rayuwa da wani namiji ba in ba deeni ba . Ya shamsu ina son Deeni ,ka taimake ni ya shamsu ,bazan iya aurenka ba “”

Kaka take tana ta surutai kamar mahaukaciya ,sai da shamsu ya rikota suka fuskanci juna.    Kiyi hakuri farida ,an fada miki ba dole akayi min ba ne kamar yadda aka miki ? Bani da yadda zanyi sai dai bin umarnin mahaifina,bani da yadda na iya,ya zame min dole zan ci amanar dan uwana .

Deeni ya bani amanr kula da ke kafin ya dawo,zai dawo ya samu naci amanarsa ,na auri macen da yake matukar so. Farida ba abu ne me sauki ba a gareni,duk kuka da rokona da zakiyi bani da ikon canja ra’ayin mahaifina ,yadda bazaki iya kin bin umarnin mahaifinki ba haka ba zan iya kin bin umarnin mahaifi na ba ;””

Ta fashe da kuka, to ya kakeso nayi?

Kasan dai deeni nakeso ,Deeni ne rayuwata,please ka taimake ni ya shamsu ka taimake ni.

Mama ce taji hayaniyarta ,ta fito ta zo ta janyeta, yayin da shamsu ya lumshe ido hawayen bacin rai na zuba masa,yana jin kukanta na ratsa kunnuwansa,yana kuntata masa zuciya

…..

 

Kuyi hakuri bacci yazo yasin ????????

Sumy luv????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Writting bySA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤

Salam !!yan uwa ayi mun afuwa na rashin posting two days????????????????

????uma sannan naga sakonninku,kuma naji dadi sosai Allah ya bar zumunci

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button