MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ameen ..
19
A daki mama tayi ta lallashi amma inaaa!! Farida kuma take ,bata ji bata gani,bata saurare,daga karshe ta tashi ta tafi dakin deeni,ta hau bisa gadonsa tana shakar kamshinsa,tana kuka tana fada masa irin tsananin son da take masa.
Farida taba gushe ba a gurin har sai data shide ta suma a wajen,mama da shamsu sukayi asibiti da ita a rude. Da kyar likita ya samu ta karfado,,sai dai zazzabi mai zafi ya lullubeta,haka nan bata nar kukan da take ba har sai da akayi mata allurar bacci,bacci me nauyin gaske ya dauke ta .
Mama ta zuba mata ido tana kallonta,tana matukar tausaya mata tare da mata addu’a a ranta ,tana maganar zuci.
” Yarinya karama ta hadu da kaddarar da ta kasa jurewa,ta kasa tawakkali,haka nan mahaifanta sun kasa ganewa.””
Nan ta mike don zuwa tayiwa mahaifiyar farida waya ,,nan shamsu ya zauna ya zura mata ido,sai ya daina jin tausayin kansa se farida.. halin da ta shiga ya firgita shi,ya san suna matukar son juna da Deeni amma bai zaci farida na haukan son deeni haka ba. Shin taya zai rayu da macen da take matukar haukan son wani bata ji bata gani ? Taya zai iya rike amanar da mahaifinsa ya damka masa bayaan cin amanar dan uwansa da ya yi ?
Yana cikin wannan hali mahaifiyar farida da yan uwanta suka shigo,hakan yasa ya fita .
Kowa dai bashi da ikon mata wani abu sai addu’a har kusan magriba ,mahaifansu maza sukazo. Tabbas sun tausaya mata,amma hakan bai sa dayansu yaji yana da niyyar canja ra’ayi ba.
Har faridan ta farka tana kuka tana rokon mahaifinta,amma sai ya kau da kai gareta,yace,intaga bata auri shamsu ba to dayan su ba ya numfashi ne ko ita ko shi mahaifinta,ko kuma shi shamsu din . Yana gama fadi ya fice abinsa.
Daga nana farida tasawa kanta dangana,sai dai ita tasan tabbas mutuwa zatayi in tta auri wani da ba Deeni ba ,don haka ta soma shirin bankwana da duniya tana jiran ta Allah ta kasance akanta.
* * * * * * * * * * *
Tun lokaci da aka kulla maganar auren shamsu da farida duk iyayen su suka hau shirye shiryeb biki ,duk wanda yaji magnar aurwnsu sai yayi mamaki saboda kowa dai yasan farida da Deeni take soyayya ba da yayansa ba .
Tuni Alh umar ya siyawa shamsu da farida tsalelen gida na gani na fada,ba abinda bai sa musu ba na zamanj mai tsadar gaske.
Hatta kayam daki bai bukaci Alh Ahmad da yayi ba,b dakin da bai sa kaya a ciki ba ,duk wani kayan l
Kyalw kyale an sakwa farida da shamsu.
Ganin kara da kawaici da Alh umar ya masa yasa shima ya ce to ya bar wani maganar hada kayan aure ,haka nan shi ya dauki nauyin biya masa kudin sadaki. Alh umar baiki tayi sa ba ,saboda a fadinta shamsu dansa ne.
Ansa bikinsu a juma’ar farki na watan karshe.
Ranar da Deeni ya bugowa mama waya gaba xaya rudewa tayi har ya so ya fahimci akwai matsala ,amma sai ta nuna masa ba komai,tana fama da hayaniya ne ana shirin auren yayun farida wani satin ,sannann shamsu ma zai yi aure.
Ihu yasa mata na murna da mamaki ,ya ce
Mama ya shamsu zaiyi aure ? Mama kinsan ban taba ganin ya shmsu da budurwa ba sai kace me tsoron mata,amma nayi mamaki . A ina matar da zai aura take ? Unguwar mu ?
Mama tayi masa dariar da bata kai zuci ba ,tace.
Deeni kenan ,wannan tambayoyi haka,ro koma dai yana nema ko baya nema ya samu ,yarinyar unguwarmu take ,”
Ayya mama,ina farida? Tna zuwa kuwa ? Kinsan nayi ta neman wayar ta a kashe,haka layin ummanta ma baya shiga ,ina jin dai hidimar bikin suke mama,yanzu da ina nan da har dani za a hada da auren yayun ta da yaya shamsu ayi,amma ba komai mu namu mu biyu zaayi mana special one ….
Tuni mama taji t rude ,ganin shamsu ya shigo tayi saurin mika mishi wayar.
Ga dan uwanka nan kuyi magana “”
Jiki ba kwari shamsu ya karbi wayar yayi da mama ta koma gefe tana hawaye,tsananin taisayin danta ya ratsa ta ,tana tunanin ranar da deeni zai samu labarin auren farida shamsu da halin da zai shiga ,bacin rai da tashin hankalin da zai shiga ne babban fargabarta . Tasan halin Deeni da zuciyar sa,in ta kule shi ba me kyau bane ……
Oh Allah !!! Kayi mana maganin abinda ba zamu iya yiwa kanmu ba “”
Tunda shamsu ya karbi wayar Deeni ke ta masa surutu yana zolayar sa,yana masa tsiya amma yayi tsit kamae ruwa ya ci shi. Deeni na tambayar sa yarinya da zai aura yar wanj gida ce? Kuma meye sunanta?
Tuni yaji kansa ya sara,tambayar tayi masa kunci , y rasa inda zai sa kansa.ya hau masa kame kame,yayin da deeni ya dauka zafin kan aure ne ya debe shi,don hka ya kyale shi,nan ya kawo masa zancen da yafi kowanne kunci.
Ina amanata da na baka ,farida ? Ina fata kana kulamun da ita ,ya take ,a wane hali take ? Kullum sonta da shi nake kwana ina tashi ,bani da burin da ya wuce in gama karatu in dawo in auri farida…………
Kafin ya kai ga ida maganar sa shamsu ya yi saurin katse wayar tare da kashewa ,saboda ba zai iya jurewa ba . Dum kunyar deeni ta ishe shi hauahin kansa da tsanar kansa ya kama shi , bai san yaushe ya sa kuka ba………….
Nace wai dan ma ba ido da ido suke magana da deenj ba kenn????
ASUBA TA GARI YAN UWA
SUMY LUV????????????
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤
20
Kwanci tashi ba wuya,bikin su farida ya matso,an gama shirin komai ,’yan uwa da abokan arziki sun gama cika gidagen duka biyu cike yake da jama’a.
Duk wanda ya kalli fuskar shamsu da farida yasan suna cikin dmuwa da tashin hankali,kowa kuwa yasan dalili ,don haka dai aka dinga binsu da fatan alkhairi.
Ana gobe daurin auren da safe mahaifin farida yayi kiranta falo,fuskarta a kode kuma a kumbure saboda kullum tana cikin kika. Nan ya sata a gaba yana mata nasiha.me ratsa jiki sosai tare da fada da kuma gargadi na taji tsoron Allah tayi biyayya ga mijinta,ta rungumi kaddarata hannu bibbiyu.
Tana kuka tayi masa godia ,tare da alkawarin zata yi masa biyayya,ya rungumi kaddara ,ta saduuda,Allah ya bata ikin jurewa.
Yaji dadi kalamanta sosai ,ya sa mata albarka sannan ya ce mata Deeni ya kira shi yana son magana da ita saboda duk wayar da zai saneta ya kora a rufe.
” Inaso in ya kiraki ki nutsu ki amsa,kar ki nuna masa komai . Sannan karki fada masa abin da bai sani ba ,kar kiyi yadda zai zargeki. Ki tuna taratu yake yi ,idan yaji wani abu yana iya barin karatun ya dawo,kuma ya samu an daura miki aure,yazo aita rigima dashi ,zhi ya rasa ki kuma zai rasa karatun ,kinga ya yi biyu babu kenn. Ni na tabbar in kina son deeni ba zaki so hka ya faru da shi ba “.
Nan ya mika mata wayar,” zai iya kira a kowanne lokaci””.
Gabanta na tsnkewa ta karba tana tunanin me zata ce masa ? Ya zata yi ta fara magana da deni ?
Tana cikin wannnan tunanin kuwa ya bugo ,nan ta zurawa wayar ido da lambobin nasa tana kallo,idonta ya ciko da hawaye ,da kyar ta iya hadiye kukanta ta dauki wyar .
Murya kasa kasa tayi sallama,nan Abba ya mike ya bar falon,don ya basu wuri suyi magana.
Farida na!!!. Deeni ya fada cikin muryar shauki .
Farida I missed u so much,nayi rashinki sosai wayarki da ta umma sam ba a samu,na san dai hidimar biki ne ko ?
Lumshe ido tayi tna jin muryarsa hade da soyayyarsa mai karfi suna ratsa ta .
“Darida kinyi shuru ,kina jina kuwa ?
Ina jinka deeni,ina sauraron daddadar muryar da nayi matukar kewa ne. Deeni kunnuwa na sun jima suna son jin wannan muryar,kasan mun jima bamu yi waya ba ,wayarka ba a kira ,sai dai kai ka kira,in kuwa an kira ma za a ji baya shiga.”